Chapter Nine

983 171 91
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ALHAJI ALIYU BUGAJE RESIDENCE
NASSARAWA GRA

A yau Sunday wanda ya kasance 30th September na shekarar..

Hanifa tana zaune a kan gadonta cikin Duvet wuraren qarfe goma da rabi na safe. Bata dade da ta farka daga bacci ba. Da alama dai sauka gadon ne ya gagareta.

Tun ranar juma'a da al'amarin nan ya faru take tunanin what next for her regarding Sadiq, she had so many options wanda tayi reducing to just 3- ta cigaba da wulaqanta shi har ya tafi, tayi resigning ko kuma ta cigaba da aikin amma a canza mata department.. bata tsayar da shawara ba amma tabbas cikin wadannan options din zata dauki daya!

Wayarta ce tayi qara alamun text message ya shigo.

Janyo wayar tayi sannan ta duba... Alert ne na salary.

Gani nayi tayi zaraf ta tashi zaune yayinda take qara kallon figures na salary dinta..

Ranta a matuqar bace na ga ta yaye Duvet din da ta rufa da shi tana fadin "ni za'a yi ma rashin mutunci??? saboda kudin shi ne ke circulating a kamfanin sai ya zabge mun salary?? toh wallahi bai isa ba.."

Gani nayi ta sauka daga kan gadon ta wuce ta fita tana ta masifa.. ko tsayawa ta dauki robe na rigar baccin nata bata yi ba.. daga ita sai gajerar sleeveless inner one din, gashinta all messy as usual idan ta tashi daga bacci.

Kai tsaye sashen Paapa ta nufa.

Ta tarar da shi kwance a kan 3-seater kujera riqe da remote yana kallon News a tashar Al-jazeera.

Yanayin yadda ya ga Hanifa kuwa ya tabbatar akwai matsala..

Gani nayi ya tashi zaune yayinda ta qaraso tace "Good morning Paapa"

"Good morning Baby.. zo ki zauna nan.." ya nuna mata space a gefen shi sannan ya cigaba da fadin "...ya na gan ki haka??? me ya faru kuma???"

Hanifa wadda ta zauna a gefen shi ce ta miqa mishi wayarta tare da fashewa da kuka tana fadin "Paapa ka ga anyi salary amma ji abinda aka tura mun.. ai ba haka aka rubuta za'a biya ni ba a offer letter.. this is like 50% off fa Paapa.. Sadiq ne yake nema ya wulaqanta ni saboda kudin shi ne... ni wallahi..."

"Baby sssshhhh, stop crying and listen to me. Kin tuna cewar an baki suspension har na sati biyu?? are you aware that idan an ba mutum suspension hakan yana nufin baza'a biya shi kudin adadin kwanakin da ya je suspension din ba?? its logical tunda you cant be paid for aikin da baki yi ba" Paapa ya fada yayinda yake riqe da hannunta.

"toh Paapa ni yanzu me wannan kudin zasu yi mun??? bazasuyi covering expenses dina ba na wannan watan.. Ko complete salary dina ma maneji zan yi balle 50% of it..."

"Zan tura miki kudi a account dinki... shikenan"

Tana share hawayenta ne ta matsa tare da rungume shi tace "nagode sossai Paapa, you are the only person I have in this world that care about me.. I am grateful for having you as my Paapa.. I love you so much my bestie"

Paapa wanda yake murmushi yace "I love you too my Baby"

Hanifa wadda tayi breaking hug din ce tace "toh Paapa wai for how long will this continue???"

"what??"

"this whole Sadiq thing.. Ka mayar mishi da kudin shi ya tafi ya bamu wuri for good, I swear even after this six months da zai yi ina mai tabbatar maka he will always come back to claim his money saboda na ga alama bayada kirki"

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now