Chapter 22

60 7 9
                                    

Aadilah Ajlal

Short Story










This is a fictional story based on my imagination.



Dedicated To Maimuna Abdallah💖



22



~ * ~

AuthOR'S POV:

Lokacin da Ajlal takoma gida Ammieh bata dawo ba don haka ta zauna a wajen gidan tana ta tunanin maganganun su da wannan yarinyar Shumaira kuma taji tanason jin ainahin labarinta saboda dole akwai babban dalilin dazai sasu zama cikin dajin nan tunda sunada damar zama a ko ina cikin fadin duniya nan.

Mikewa tayi ta dauka duwatsu bayanta zauna a gefen wani ruwa nan tafara jefa duwatsun ciki.

~ * ~

Jalil Khalil shine ainahin sunan shi amma mutane sunfi kiransa da Doctor Jay kuma sun hadu da Amah a bikin wani friend dinsa tunda yaganta yaji yakamu da sonta kuma sai akayi sa'a itama tana ganinsa taji ya birgeta daga nan fa suka fara soyayyah wanda basu dauki lokaci mai tsawo ba sukayi aure.

Bayan ankai amarya gidanta dake Foutain Estates hadadden Estate ne mai kyau da tsari kowa yana yaba gidan masu farin ciki nayi hakama masu bakin ciki nayi nan fa akabar Amarya daga ita sai halinta.

Bayan kowa ya watse har wajen karfe 1am amma babu ango babu dalilin sa.

Ganin hakan yasa Ramlah (Amah),mikewa tacire kayanta tasa masu saukin nauyi saboda anata ganin bai kamata tasa sleeping dress ba a daren ta na farko ba, wannan shine zai nunawa miji tabbas ya auri yar masu tarbiya dakuma sanin yakamata.

Bayan tagama duk abinda zatayi sannan takashe duk bulb's din gidan,sannan tadawo bedroom dinta ta kwanta cikin karamin lokaci bacci ya dauketa dama a gajiye take ansha hidima sosai.

Baccinta take hankali kwance tamkar batada damuwa jitayi kamar ana tabata kin bude idanunta tayi saima kara jan blanket datayi ta rufe jikinta, again taji ankara yaye blanket din tsaki tayi bayan ta bude idanunta amma bataga kowa ba.

Harta koma ta kwanta sai kuma taji kamar motsi a parlour mikewa tayi bayan ta dauki phone inta ta kunne light, gani tayi duk bulbs din a kunne itadai tasan cewa ta kashe komai kafin ta kwanta amma yanzun har TV a kunne take a fili tace "inaga Doctor yadawo ne" daidai lokacin Idanun ta ya sauka akan daya daga cikin kujerun parlour mutum indai bai saniba zaice mutum ne a wajen smile tayi tafara tafiya harta isa wajen tana cewa "doctor yaushe kadawo? aida kasani ka tashe......" Saidai magananta ya makale sakamakon tozali da abinda tayi mutumin dake zaune a kujera ne ya juyo gaba daya fuskanshi tamkar ta mage ga idanunsa bakin kirin bakin sa wasu irin hakorane masu abin tsoro,,,, ihu Amah tasaka nan da nan komai yakashe kanshi baka ganin komi sai duhu.

Amah kam kokarin kunna phone dinta takeyi amma taki kawowa nan tafara tafiya cikin duhun yanzun burinta shine taganta a dakinta kuma kan gadonta.... Saidai cak ta tsaya dayin tafiyan jin alamun mutum a bayanta a hankali take juyowa saidai bataga komai ba cibaga tayi da tafiya nan ma taji tayi tuntube da wani abu cikin tsoro takai hannunta kan abin wata irin kara tasaki jin wani hannu mai wasu irin farce kuma daidai lokacin bulb din suka kara kawowa Idonta yasauka akan wata mata sanye da fararen kaya gashin kanta sunyi sama suna wani irin motsi idanunta bkin kirin bakinta wasu irin abubuwa masu tsayi suna fitowa daga ciki, direct wajen Amah ta nufa ganin hakan yasata faduwa a kasa tana ja da baya baya,, jitayi tayi karo da wata kafa a tsorace ta juyo nan idonta yasauka akan doctor shikam da mamaki yake kallonta metakeyi a irin wannan lokacin? tambayan daya yimata kenan da sauri ta tashi ta rungume shi sosai take kuka shima hugging dinta yayi sosai ya rufe idonsa saikuma ya bude su gaba daya eye color din takoma blue saikuma tadawo normal hannunta yakama suka koma bedroom nan yafara tambayanta abinda yafaru nan ta fada masa anan yahau gargadinta da kada tafadama kowa wannan maganan shida kanshi zai nemo mafita.

Aadilah Ajlal Where stories live. Discover now