Final Chapter 25

106 8 33
                                    

                  Aadilah Ajlal

                        Short Story

This is a fictional story based on my imagination.

Dedicated To Maimuna Abdallah🥀

Warning:Read it on your own risk it contains mature content and a very strong language.

Final Chapter
25

~ * ~

Kuka takeyi sosai su kansu nurses din ba karamin tausayi tabasu ba kamata sukayi suka daurata kan bed bayan sun bata maganin bacci cikin minutes baccin ya dauketa.....

Tundaga ranan kullum sai Ajlal taje wajen Aadilah amma bata kulata su Amah ma kullum sai sunje dubata amma bata magana banda kuka babu abinda takeyi saboda tagaji da ce musu lafiyanta lo babu abinda ke damunta amma babu wanda ya yadda da ita.

Kamar kullum sunje cin abincin rana sosai nurses ke kula dasu saboda ko abincin wasu basa iyaci masu hankali kadan ne zakaga sunaci shima duk rabi sun zubar dashi a kasa hakan yasa mai hospital din karo nurses saboda ake kula dasu da kyau.

Wata nurse ce takawoma Aadilah abinci amma ko kallonshi batayi ba tayi zurfi a tunani wai itane ake mata kallon marar hankali saboda kawai.... Nurse din ce ta katse mata tunanin datakeyi nan ta shiga rarrashinta dakyar tasamu taci abincin...

Aadilah zaune gaban Doctor yana yimata tambayoyi dakuma yanayin datakeji a jikinta yanzun shiru tayi batace komai ba duk tambayan duniya yayi mata amma taki magana nurse yakira yace akoma da ita harsun kai bakin kofa saikuma ta fisge tadawo gaban Doctor din hannunta tasa ta buga desk din dayake kai sannan tace "indai harsai nayi magana sannan zaka sallameni to bazan taba yin magana ba, babu shakka saina dauka fansa akanka kasani nasani lafiyalau nike amma saboda son zuciya zaku maidani mahaukaciya inaji ina gani bazan taba kyalekaba I hate you and I will hurt you kamar yadda kayi hurting dina."

daidai lokacin security suka shigo suka kamata suka maidata dakin bayan anyi mata needle.....

Ajlal kam tunda tabar asibitin take kuka, hankalin Ammieh yatashi ganin irin kukan datakeyi dakyar tayi shiru sannan ta bata labarin komai itama Ammieh ta jinjina lamarin sosai taji tausayin Aadilah shawara sukayi kan yadda zasu fito da Aadilah daga can mental asylum din.

Amah zaune gaban Aadilah tana bata abinci saboda yau tunda ta tashi taki cin komai har yamma bataci komai ba gashi kuma dole saitaci Abinci sannan za a bata magani sannan ayi mata needle bayan tagamaci ta kalli Amah tace "Amah meyasa aka kawoni nan? Amah shin wani cuta ke damuna?" Hannunta takama tace "Aadilah karki damu Doctor yace jikinki yana kyau kuma abinda ke damunki shine Hallucinations ma'ana..."
"Nasani nasan ma'anar shi kuma nasan yanayin cutar amma fa ni lafiyalau nike banga wata alamar cewa hallucination ke damu naba, Ajlal she's real.." Kanta ta girgiza tace "kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki zaki samu lafiya kuma ita kanta yarinyan dakike magana akanta sam babu ita Ajlal is not real kawai imagine dinta kike tunanin kine yake nuna miki cewa akwai wata wadda kike rayuwa da ita Aadilah." Komawa tayi ta kwanta batace komai ba ganin hakan yasa Amah mikewa cikeda tausayin yar tata tafice daga asibitin gaba daya.

9:00pm

"Aadilah kitashi kisha magani" tanaji tayi shiru ko motsi batayi ba zama tayi a kusa da ita tace "Aadilah yakamata kicire komai aranki, kisaki jikinki indai kika kwantar da hankalinki komai zaizo da sauki zaki samu lafiya tunda abin naki baiyi yawa sosai ba kuma...!" Ranta a matukar bace ta mike hannunta duka ta rufe ears dinta cikin bacin rai tafara cewa "ENOUGH! Enough of this bullshit!! I'm done with this..this lies, take all your fucking shit and get the hell out of here just leave me alone." Da mamaki,tsoro take kallonta tunda take wannan shine karon farko data fara ganin Aadilah a irin wannan yanayin matsawa tafarayi zatayi magana Aadilah ta daga mata hannu tareda da nuna mata kofa cikin sanyi jiki tafice daga dakin.

Aadilah Ajlal Where stories live. Discover now