"Aunty you're like an angel to me, I just want to see you"
Murmushi kawaii tayi,yayin da Hashim yake mamakin irin shakuwar dake tsakanin Asiyah da Diyya, Ammar fita yayi awa d'aya na cika ya shigo da nurses guda biyu a biye dashi.Ba Asiyah kad'ai ba hatta Diyya da Hashim Saida sukaji kirjin su ya soma bugawa.
💦💦💦💦💦💦💦💦
.......... "Are you ready?"
Ammar ke wa Asiya wannan tambayar Murmushi tayi ta d'aga Masa Kai alamun eh, Shima Murmushin yayi ya kalli Hashim yace "She likes laughing"
Murmushi kawaii ya Masa.A hankali ya Fara cire bandage d'in Diyya da Hashim duk hankalin su na kanta , sai da ya rage bandage d'aya Ammar ya ummurci Diyya da ta tsaya a gaban Asiyah hakan kuwa akayi, bayan ya cire idanun ta a rufe yace "Open your eyes slowly and carefully"
A hankali take Bud'e idanun ta tana ganin wuri bashi bashi ba idanunta na wassakewa ta sauke su akan wata kyakkyawar halitta fara, ba doguwar bace sannan ba gajera bace Murmushi tayi Mata ita ma Maida Mata "Aunty Diyya kece?"
"Eh nice" idanun ta ya cika faal da hawaye mikewa Asiya tayi ta rungume ta kyam a jikin ta cikin kuka take Mata godiya.Gyaran murya Hashim yayi "Wato ni ba a damu dani ba ko? kin ma manta Dani?" Yadda yadda maganar ne ya sanya ta dariya Yana magana Kamar d'an shekara biyar harda langwab'ar da Kai, Kare Masa kallo tayi ganin yanda ya canza ya Kara haske ya Kara kyau.
Karasowa yayai gaf da ita Diyya ganin zai iya ture ta, ta matsa ta basu wuri, kallon kallo sukeyiwa juna, wani irin wutar son junnan su ne ke tafarfasa a cikin zukatan su, hannu ta ya riko yace "Nayi matukar murna da idanun ki suka dawo Baki ji yanda nake ji ba ba yau"
"Hmm nago..... " Saurin rufe Mata Baki yayi da lausassan hannun sa ya gyad'a Mata Kai had'e da fad'in "Ban bukatar kalmar godiya daga gare ki, Nayi wannan ne a matsayin ki na wacce na fiso, wannan kad'an ne, sannan kofa a Bud'e take idan kina bukatar wani abu just tell me"
"Ko wacce irin bukatar da Zama maka dashi zaka min?"
"Eh insha Allah just name it"Diyya har ta Isa kofa zata fita Asiyah Tace "Aunty Dan Allah kizo"
Ba musu ta karasa inda suke, kallon sa tayi Tace "Inaso ka had'a ni da Aunty Diyya ma'ana ka aure mu"
Zaro Ido yayi yace "Amma wasa kike ko?"
"Dagaske nake"
Iska ya hura Mai zafi yace "Na amince" ya Maida kallon sa ga Diyya "Da fatan zaki amince da hakan My Diyya?"Saurin 'dago kanta tayi tana kallon sa cike da mamaki sakin hannun Asiyah ya nufi inda ta tsaya Murmushi yayi yace "Kina mamaki ne?"
Kai kawaii ta d'aga Masa Murmushi yayi yace "Maganar aure ne ya baki mamaki ko Kuma Kiran ki da nayi da My Diyya?"
Kai a kasa murya chan ciki Tace "Duka biyu"
"To ki daina mamaki kinji"
Kai ta d'aga Masa idanun ta hawayene ,d'aga habarta yayi yace "Kuka? Please ki daina" ai kuwa kamar ce mata yayi ta kara, ganin kukan yayi yawa ya rungume ta, a tare suka sauke wani ajiyar zuciya.Asiyah sai Murmushi take (Ni ko nace Asiya Murmushi Kuma ko Yar kishin Nan babu) Diyya da Hashim sun Lula wata duniyar,dama gogan naku Yana so Yana kaiwa kasuwane a kunne ya rad'a Mata "I miss you Bae"
"I miss you too" Kara kankame ta yayi a jikin sa kamar zai Maida ta cikin cikin sa.Gyaran muryar da ammar yayi ne suka tuna Basu kad'ai bane yayi saurin sakinta kamar wani Mara gaskiya.
Dariya Ammar yayi yace "Congratulations Asiyah"
"Thank you Dr"
Hashim yace "Is there anything left?"
"No I have already discharge her"
"Good in that case we are going back to Nija tommorow"
" What so soon?"
"Yeah what will we wait for?"
"you're right, but Amma gonna miss you guys"
"Same here bro, you'll attend our wedding right? Cos you'll be our guest of honor"
"Insha Allah, ill be there."A motar sa ya Maida su har masukin su, sannan yace zai dawo da yamma su fita cin dinner, Hakan kuwa akayi karfe takwas ya dawo ya d'auke su suka fita,tare da matar sa suka zo, Sunci sun Sha har sai karfe goma saura ya dawo da su, sannan ya musu alkwarin Kai su airport.

YOU ARE READING
MATAR UBA 2021(A TRUE LIFE STORY OF ASIYAH)
Short StoryLabarin Wata Mata da take azabtar da 'ya 'yan mijin ta ba Tausayi ba tsoron Allah, Kar ku Bari a Baku Labarin.