15-16

2 0 0
                                    

♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
*MATAR MAHAIFINA*
♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️

~Labari da Rubutawa~
       Na
MAMAN AMATULLAH

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS          🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

              *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

Wannan littafin na kuɗi ne zaki biya nera ɗari biyu (200) ta asusun banki 0003187186 Khadija salisu ja'iz bank ko ki turo katin MTN na ɗari biyu (200) ta wannan lambar 08168159409,game neman ƙarin bayani ze iya tin tiɓata ta wannan lambar dake sama.

        FREE PAGE

Shafina 15-16

        Yau tayi sa'a bata wani tarar da layi ba,ba suwuce mutum biyu ta samu a gaban taba,wannan dalilin yasa ba jima da zuwa ba layi yazo kanta,ta shiga "Gafara dai boka me gani har hanji" Cikin wata iriyar murya da babu ko daɗin sauraro yace "uhmmmm samu guri ki zauna ki kula karki taka ɗan sarkin aljanu yanzu ya shanye miki ƙafafi" JIki na rawa Sa'ade ta ɗan ja da baya dan ta tsorata da jin kalaman sa, guri ta samu ta zauna a matukar tsorace dan gani take kamar zata zaune kan ɗan sarkin aljanu, cukin tsawa wacce ta ƙara firgitata yace "Kinutsu kiyi min bayanin abin da yake tafe dake" Jiki na rawa baki na kar kar wa tace "Am...am dama nazone akan maganar miji na inaso a mallake minshi ya zamana nice mijin shi kuma ya zama matar,dan inaso ya zama sai yan da nayi dashi" "Indai wannan ce buƙatarki an gama ya sunan mujin naki? Cike da zumuɗi ta faɗa masa nan ya dinga surkulle irin nasu na mishirikan bayi,yana gamawa ya dauko wani garin magani ya bata tare da cewa "Ki kar ɓa da hagu da hagu zaki karɓa,kitabbatar kin saka masa abinci ko abin sha,abin buƙata anan kawai ki tabbar ya shiga cikin sa,zakiga aiki" Jiki na rawa ta saka hannu ta karɓa tana godiya kuɗi ta kwance a gefen zanin ta ta miƙa masa, cikin wata irin murya yace "Ajiye anan ɗan ta tsi-tsi zezo ya ɗauka idan kin ajiye ki fita da baya",Hannu na rawa ta ajiye, ta miƙe ta fice,..

   Cikin ikon Allah har ta dawo gida malam be dawo ba haka ma yaran gudan,Auwalu kaɗai ta tarar yana wanke kayan sa,ko da ta shigo ko ci kanki be ce mata ba,dan ya raina ta, baki ta washe tana "Aa Auwalu yau kuma wanki akeyi lallai ga dukkan alamu babu na sawa," Bakibya turo gaba yana "Wai ke umma komai kika gani sai kinyi magana ni Wallahi bana son sa ido" me makon taji haushi sai ma dariya  da tayi ta ƙara da cewa "To shikenan nayi shiru, nace na kawo karon nawa ka haɗa dasu danni ma na tara wankin? "Taf Aa Wallahi karki kawo nima naji da nawa ke babu damar kiga mutum yana wanki sai kin nemi a haɗa da naki to gaskiya bazan iya ba ato" "To shikenan babu komai zanyi da kaina" "Da dai yafi" Yafaɗa yana ƙun ƙuni,,ana cikin haka Sani da Juhaina suka dawo hannun su riƙe da na juna,da sallamar su suka shigo,Sa'a de dake tsaye a ƙofar kicin ta ƙaraso da sauri ta jawosu,ta raba hannunsu cikin masifa tace "Wai ni kam ke wacce irin natacciyar yarinya ce ban hanaki yawo da Sani ba ke baki san hanya ba dole sai kun taho tare,, to daga yau sai yau kar na ƙara ganin ki tare dashi kitafiyar ki ke kaɗai duk abin da ze sameki ya daɗe be sameki ba,,ita dai Juhaina batace ko mai ba sai hawaye da take,mari Sa'ade ta kwaɗa mata tare da cewa to ina magana kin mai dani sakarai ko sai kallo na kike da wa innan mayun idanun naki" kuka ta saka tana dafe kumatu tare da cewa "Umma kiyi hakuri na dena," "Naji maza kije ki cire kayan makaran tar kije kiyi wancan wanke-wanken da ubanki ya hanakiyi tin safe kuma muddin kika bari ya dawo ya sameki kinayi baki gama ba sai jikinki ya faɗa miki,dan sai na zane miki jikin ki,zaki wuce ko sai na ƙara marinki" tana kuka ta wuce ɗakin,nan ta bar Sa'ade na tafaman bam bamin faɗa,,

Auwalu dake wanki yace "ai dama umma kece kike ragawa yarin yar nan shi yasa take abin da taga dama,da ga ita har uwar ta nifa na tsanesu Wallahi dan bakiji daɗin da najiba da taɓata ni fatana ma kar ta dawo" "Ai kuwa yanzu ba sauki kabar ni da ita" "uhm umma kike abarki da ita kin san dai halin baba kuma kin san yan da yake san wannan aljanar ƴar tasa baze zuba ido ba yaga kina wahalar da ita ba," dariya Sa'ade tayi tare da cewa "Yaro yaro ne ka zuba ido kaga yan da zan mayar dasu daga ita har uban nata Sa'ade ce fa" "Allah umma kice nima zan ƙara samun ƴanci agidannan dama baba yana ta kuramin musamman a gurin zuwa makaranta" "Ai kar ka samu damuwa daga yau na baka dama kayi duk abin da kakeso ni kuma ka barni da baban ku," "Wuh shi yasa nake sonki kinyi umma" dariya tayi tana cewa "Oh sai yanzu kasan nayi ɗazu me kace," kai ya sosa yana manta kawai umma" "To ai shikenan,, Sani dake tsaye tin ɗazu yana jin haushin abin da umma tayiwa Juhaina, yace ,"Haba umma dan Allah wai me tayi muku ne har haka kuma umma kinsan wannan aikin yayi mata yawa tin da ba sabawa tayi ba" cikin ɗaga murya Sa'ade tace "Kai dallah rufemin baki sakarai sam bakasan lefin yarin yar nan kamar uwar ku ɗaya ubanku ɗaya to Wallahi ka fita a ido na sakarai kuma aiki yanzu ta soma ko da shine ze zama ajalinta,sai tayi" "Baba umma... kai rufemin baki ko na saɓa maka zaka wuce ko sai na mammareka,,hk ya wuce ɗaki badan ya soba,,,

    Tana canza kaya ta fito ta fara wanke-wanke duk da bawai ta iya bane dan lokacin umminta nan ɗauraya kawai take taya ta,cikin sa'a kuwa har ta gama baban nasu be dawo ba,,

Yau ko da malam Sabo ya dawo ya ga canji sosai ko yan da Sa'ade ta tarbesa kaiɗai ya isa abin mamaki sai dai ya shanye mamakin sa,abinci ta kawo masa har da ruwa zama tayi ta zuba masa abinci ta ɗauki mafici aka fara yi masa fiffita ana "Bismillah malam kaci kar ya huce,sabi da mamaki zama yayi kamar wani soko dan raban da yaga haka daga gurinta tin yana zuwa zance, dan haka yace to har ya daki loma ze saka abaki,ya sauke yace "niwai ina ƴar baba ne taci abinci kuwa? jin wannan tambayar ba ƙaramin kular da ita yayi ba, wata zuciyar tace ki nutsu karki ɓata komai,daga yau fa komai yazo ƙarshe, da wannan tinanin ta ƙakaro murmushi tace "Ai tana ɗaki yanzu nake son na zuba musu idan na sallame ka" yana jin haka ya ajiye cikalin ya fara ƙo ƙarin kiranta "Ƴar baba! Ƴar baba!! da sauri ta fito tana amasa wa, tana "Baba gani" "Yauwa ƴar baba zonan muci tare ai nasan kina jin yinwa ko? kai ta ɗaga alamar eh,,,

   Sosai ran Sa'ade ya ɓaci tana gani zaa ɓata mata shirin ta, "cikin sauri tace haba malam kabari Dan Allah na bata nata amman ya na kawo maka abincinka kace tazo kuci tare to sukuma sauran yaran fa? du ban ta yayi tare da cewa to shikenan,kawo mata nata,to tace jiki na rawa ta ta tashi taje ta kawo mata ,kar ɓa yayi sai da ya bata ya tabbatar ta koshi kafin ya fara ƙo ƙarin faracin nasa in da gaba ɗaya Sa'ade ta gama kosawa taga yaci,ji take kamar tayi masa ɗura,,

   Juya abincin ya dingayi amman ya kasa kai wa bakin sa,  "Haba malam waimeke damun ka ne sai kace yaro sai faman juya abincin kake kaci mana,dan Allah ko se yayi sanyi" "Abincinne sam bana jin cinsa" "haba ai daurewa zakayi dan Allah kaci" ,"To shikenan bari naci, ɗebowa ya yi yakai bakinsa sam ya manta da ya yi bismillah, ajiyar zuciya tana jin zuciyar ta tayi mata wani sanyi,...

Sharhi da tayani turawa😍

MMN AMATULLAH CE🥰

MATAR MAHAIFINAWhere stories live. Discover now