33-34

6 0 0
                                    

♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️
*MATAR MAHAIFINA*
♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️♦️

~Labari da Rubutawa~
      Na
MAMAN AMATULLAH

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS          🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

              *💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

Wannan littafin na kuɗi ne za ki biya nera ɗari biyu(200)ta asusun banki 0003187186 Khadija salisu Ja'iz bank ko ki turo katin MTN na ɗari biyu(200)ta wannan lambar,08168159409,ga mai neman ƙarin bayani ya tuntuɓe ni ta lambar da ke sama.

      FREE PAGE

Shafi na 33-34

  
     Tana fita Magajiya ta bita da harara tare da ce wa "Wato da ke kin ɗauka banza zakici,ke baza'a more ki ba to baki sa ki zauna min anan ba ina ci da ke babu riba ba,matsiya ciya wacce bata gaji arzik'i ba in dai KD ce gaki a cikinta"

Guri ta samu ta zauna a k'ofar gidan ta zabga uban,ta gumi in da hawaye wani ke bin wani,ta jima a zaune tana tinanin in da za ta dosa,kafin ta mik'e ta ɗauki kayanta ta yi gaba,tana tafiya tana kuka,ta yi tafiya me ɗan nisa kafin ta hangi titi,ƙarawa ta yi bakin wani gida ta zauna tare da zabga ta gumi tana kallon motocin da jama'ar da ke ta faman shige da fice,,tanan zaune agurin nan har aka kira sallar azahar nan fa ta fara tinanin in da zata samu ruwan da zatayi sallah,shawara ta yan ke akan ta karasa fita titin ko zata samu shago,tashi ta yi ta ɗauki jakar kayanta ta ƙarasa bakin titin cikin ikon Allah kuwa sai ga shaguna ma ta samu,k'ara sa wa ta yi ta siyi ruwa,guda biyu,sannan ta dawo in da ta fara zama,Alwala ta yi ta shimfiɗa ɗan kwalinta tayi sallah,bayan ta idar ta jima tana kai kukan ta gurin mahaliccinta akan ya kawo mata mafita,tana idar wa ta sake gyara zama a gurin dan ko niyar tafiya ma bata da shi dan ko ta tafima bata san in da zata dosaba,,da yake uguwar shiru ce babu yawai tar muta ne hakan ya sa,babu wan da suka sawa zamanta ido,,

KANO

Mtsss mtsss kai wai wannan wacce irin masifa ce ace mutum tin safe yake aiki sai kace jaki gaskiya na gaji,Wallahi da nasan in da zanga ya rinyar nan da Wallahi ni kaɗai nasan abin da zanyi mata dan iskanci ko me akayi mata a gidan da har zata ɗebi kaya ta gudu, duk wannan bam bamin faɗan Sa'ade ke ta faman yin sa  ta aikin gida, wata zuciyar ta ce mata to ai ke daɗi mafa ya kamata kiji,kin ci nasarar korar uwa da ƴarta gidafa yanzu ya zama naki daga ke sai yaranki kinga sai ki ci karanki babu babbaka, ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi,tare da ce wa "Kuma fa haka ne,tamafi ruwa gudu kai Allah yasa ma ta faɗa mugun hannu ko wa ma ya huta" Ji ta yi wani farin ciki ya mamayeta,haka ta cigaba da aiki tana jawowa Juhaina mugayen alkaba'i

KADUNA
Tanan zaune har magarba ta kawo kai,wasu matasa ne taga sun nufo in da ta ke zau ne ji ta yi wani tsoro ya shigeta sosai,duk da bata da tabbacin gurin ta zasuzo amman ya na yin su be yi mata ba sam,tana cikin tinani ta ji ance "Ah ƴan mata kin ɓata ne ko wani kike nema? amatuƙar tsora ce ta ɗago ido ta dubi wan da ya yi mata maga na,kallo ɗaya ta yi masa ta sauke idon ta tare da kautar da kai gefe ba tare da ta ce komai ba, da yan ya sake ce wa "Ya beb da kefa muke idan kin ɓata ne ko ba kisan in da zaki ba to mu muna da masaukin irinki,ko ya kace abokina?Ya k'arasa maganar yana ɗaga wa abokinsa gira,yanzumma ko cikanku bata ce musu ba sai ma ƙoƙarin mik'e wa da ta ke, gaban ta suka sha, su na ce wa "Ya wai muna yi miki magana ki na  wani sharemu,to Wallahi bari kiji mungani kuma mun buƙata kuma dole ki bamu haɗin kai,idan ba haka ba mu kwata ta k'arfi,dannu ba ma ganin abu kuma ya yi mana bamu ɗan-ɗana ba,ko ya mutumina? "Kwarai kuwa aboki na beb ɗin ta yi kai da ganin kalarta kasan,za'a huta," Ya k'arasa maganar suna dariya,,wani irin bugawa kirjin ta yake ban da hawaye babu abin da suke zuba daga idanunta,cikin rawar murya ta ce "Dan Allah ku dubi girman Allah ka da ku ɓata min rayuwa ta,dan Allah kuyi hak'uri ku bani hanya na tafi" Dariya suka sake yi a tare tare da ce wa "Ai tin da muka yaba dole sai mun lashi zumarki,balle ma gaki a ariar mu,to kinga sai yan da mukayi dake," Waige-waige ta farayi babu ko alamar muta ne gashi ana ta kiran sallah duhu ya fara shiga fargaba da tsaro ne suka ƙara ratsata,babu abin da take sai addu'ar ne man tsari a zuciyarta, da sauri ta tsugunna a kasa,tana ce wa ɗan Allah kiyi hakuri,karkuci mutunci na,,suku wa ban da dariya  babu abin da sukeyi, wata da bara ce ta faɗo mata,hannun ta ta ciko da kasa dukka biyun,in da ta mik'e tana k'ara basu hak'uri, "ke kinga kina ɓata  mana lokaci muje kawai,dukkansu sukayo kanta da nufin riketa cikin zafin nama ta watsa musu k'asa a ido da sauri sukarufe ido suna murza wa ganin haka yasa ta ɗauki jakar ta ta ruga bakin titi da gudu,gudu ta ke da iya k'arfinta ko da ta k'araso bakin titi ko duba wa ba ta yi ba ta tsallaka saura k'iris,wani me mota ya bigeta amman ko bi ta kansa ba ta yi ba ta wu ce,dan gaba ɗaya a firgi ce ta ke,jikin wani gida ta samu ta ɓuya ,a wani ɗan lungu,tana mayar da numfashi,gawani kuka da ya ƙwa ce mata,lallai tabas ta yi kuskure da har ta gudu ta bar gidansu dan ta gwammaci wahalar Sa'ade da wannan halin da ta tsinci kanta a ciki,sai yanzu ta ga ne rayuwa cike ta ke da ƙalubale iri-iri,kuka ta sake fashe wa dashi tana jin dama ta buɗe ido ta ganta a gida idan yaso Sa'ade ta yi gunduwa-gunduwa da namanta,

Bayan idanunsu sun buɗe suma ta kowa sukayi da gudu,sukayo bakin titi suna ne manta sai dai babu ita babu dalilinta,haka suka hak'ura suka koma suna cizon ya tsa,,

Tanan rakuɓe alungu har aka idar da sallar isha,gari yayi duhu ta ko ina tsoro ya ƙara mamaye zuciyarta,,ko sallah ta kasayi tin da ba ta da ruwa sai ta nemo,haka ta cigaba da zama cikin tsoro da fargaba ga dare yana ta larayi,gashi ba tasan in da zata dosa ba,jin shiru unguwar kowa yana cikin gidansa,ya sa ta dakar da zuciyar ta ta fito,dan ta samo ruwa ta yi sallah,ci ke da tsoro ta tako zuwa bakin titi ta siyi ruwa na nera goma kuma ita kadai ta rage mata,,tana siya ta koma in da ta fito tana tafiya tana waige kar wani ya biyota,duk da duhun lungunnan haka ta koma,ciki ta daura alwala ta yi sallolinta ta jima tana yin addu'a akan Allah ya kawo mata mafita,nan zaune har misalin sha ɗaya na dare,,tsoro da fargabar abin da ze sameta,fal zuciyar ta,

    Tanan zaune,misalin sha biyu na dare 12:00am  ta fara jiwo hayaniya na tin karota tini cikinta ya k'ara ɗurar ruwa,k'ara ɓuya tayi duk da cikin duhu ta ke tin tana jin muryoyin daga nesa har sukayo kusa,da ita,jitayi kamar ma lungun zasu shigo,jakar kayanta ta k'ara rungume wa tana ambaton Allah,ba tayi aune ba taji wani yayi karo da ita,,taga-taga yayi ze faɗi ya yi sauri dafe bango yana,dan karo ashar tare da ce wa "Kai ku haska min" ana haska fitila sukayi ido biyu da Juhaina wacce take dun kule guri ɗaya,ɗaya daga cikin su ya ce jar uba yau she mata suka fara kawo kansu har fadar mu,ke mutum ko Aljan? Cikin rawar murya tace mutun ce dan Allah kuyi hak'uri Wallahi ban san nan ɗin gurin ku bane" Ha ha ha ha dariya suka saka su duka,kafin ɗaya daga cikin su ya ce ,to ai gashi kin sani,kuma kin kawo kanki,ko ya kace oga ka samu mata,?Wan da aka kira da oga ya ce kamar ka sani dama yau a matse na dawo,beb ɗita ta k'wafsamin,sai ga tsuntsu daga sama ga sashshe,kuma wannan daga jin muryar ta zatayi zaƙi kamar yan da muryar ta ta ke da zaƙi,ko ya kuka ce yara? Duk suka amsa da haka ne oga,ɗa ya daga cikin su ya k'ara da ce wa "Ni kai na har na jiƙa wando daga jin muryar ta ina fatan zaka sammin in ɗana idan ka gama" Ai kar ku samu damu wa duk zaku ɗana na ma har gida ai sai yan da mukayi dashi,,cikin matsanan cin tashin hankali da kuka ta ce dan girman Allah kuyi haƙuri Wallahi ni ba ƴar iska ba ce,kar ku ɓata min rayuwa,na roƙeku,, "Ke kinga ai mu dama irin ku muke so garama ki dena bamu hak'uri dan yau dole mu lashi zumarki,kai ku ɗauko min ita,, Juhaina najin haka ta mik"e tage da sauri,tare da matawa baya,k'ara matsota sukayi,cikin zafin nama ta saka hannu ta bigesu ta yo waje a guje,,ta nufi bakin titi,tin k'arfin ta take gudu,idan suma suka biyota,,kuka ta ke tana neman temako amman da yake dare ya fara shiru ka ke ji,tana k'ara sowa bakin titi ya yi dai-dai da zuwan,wata mota,da sauri ta sha gaban motar tana neman temako,wani wawan birki akaja ji kake ƙeeeeeeeeeeeeee,da sauri ta zagayo tana dan Allah ki temaka min wasu ne suka biyoni,da sauri matar ta buɗe mata mota tana cewa sauri ki shiho,cikin sauri ta faɗa motar tare da rufewa da ƙarfi taja motar suka bar gurin.....

comment and share plz😍

MMN AMATULLAH CE🥰

MATAR MAHAIFINAOnde histórias criam vida. Descubra agora