23-24

524 34 16
                                    

Baffa ne yabi bayan Grandson ɗin nasa da kallo yana mmki hali irin na Ibrahimul Khalel.
Not too long Ya Heemu ya dawo cikin ɗakin ɗauke da gorar ruwa yana kafawa a bakinsa tare kwankwaɗar ruwan da sauri da sauri kamar zai janye gorar ruwan zuwa cikinsa.
Yana gama sha yaja ya zauna dab da Baffa kansa a ƙasa amma jikinsa har yanzu was vibrate amma ko a fuska baza ka taɓa gane ai nayin abinda yake cikinsa a zcy ba.
Huci kawai yake yana fesar da iska hatta gashin kansa wanda suke a murmurɗe kamar anyi masa (Dada)
Sai da suka miƙe tsaye.
Baffa ya gyara zama yana ɗan daidaita nutsuwarsa cike da kamala da kuma haiba irinta kamilallun maza Baffa ya kalli Al'mustapha yace.
"Al'mustapha ina neman amincewar ka akan ka bawa jikana auran ƴar kuma jikata idan babu damuwa"
Wanda aka kira da Al'mustapha yaja gajeran numfashi tunanin halayyar Moha yake.
Yarinyar tana da wahalar sha'ani mai gane mata sai ya shirya.
Bata da tsoro sam ga tsaurin ido haɗi da zallar ƙuruciya, bata sanin dai-dai da abinda yake ba dai-dai ba, sai dai ita ɗin abin tausayi ce sosai.
Musamman idan ciwonta ya tashi ko da yake duk zafin ciwonta bai kama ƙafar na (Hawwa'u Jidderh, kulu kuma Julde ƴar makauniyar Abu Maleek ba).
Tana da rauni sosai amma shi kansa bai san mene rauninta ba, har gobe kuma abu guda yake sawa ta saduda shi kansa baya gane wannan lamari nata domin abun yana masa kama da JUYAYI.
rawar kai yay mata yawa over nutsuwarta ɗaya Ya Heemu gashi wani dalili na sawa ya cire dukkan wani hope nasa akan ɗan ƴar uwar tasa.
Idan Khalel baya kusa mgnar wa Mamansa za taji? Wazai mata tsawa ɗaya ta samu nutsuwa?
Baffa ne yay gyaran murya yace
"Alhj Al'mustapha kai muke saurare"
Numfasawa Alhj Al'mustapha yay kafin ya ɗaga kai ya kalli Aysuhtul humaira yaga taiwa Ya Heemu ƙuri da idanu kana ya mayar da kallonsa ga Ya Heemu yaga hankalinsa kwance kamar ba shi ya shiga tension ɗin daya shiga yanzu ba.
Kansa a ƙasa yana latsa Wayarsa mai ƙirar Iphone 12 max pro.
Cikin sanyin nutsuwa haɗi da kamala da kuma kamewa irinta mazan jiya masu sanin darajar na gaba dasu yace.
"Baffa Nima kamar ɗa nake gareka to bana da haufi akan dukkan wani shawara daka yanke akan wannan sabon al'amarin, yadda Jikar ka Aysuhtul humaira zata amince da sharaɗin ka haka nima zan amince da sharaɗin ka Baffa, ka amince ɗari bisa ɗari Allah yasa Albarka ya kaɗe fitina"
Ya ƙare maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa yana mai tausayin yarinyar tasa, wacce har yanzu bata san abinda yake mata ciwo ba, girman jiki ne kawai da Ubangiji ya bata.
Jinjina kai Baffa yay cike da gamsuwa da kuma girmama girman karamcin da Al'mustapha yay masa.
Kullum yana buƙatar kasancewar da yarinyar sa, amma baya samun damar haka.
Domin dashi da Baffa ba'a san wanda yafi son Moha ba, ƙarfin soyayyar da Baffa ya kewa Moha yasa gaba ɗaya ya dawo da zamanta wajansa, ganin haka yasa sauran jikokinsa dawowa wajansa baki ɗaya, Shoona, Hannah Sai kuma Sunaina ita wannan tana karatu waje sbd tana ɗan gaba dasu, Murgayiya Safa kam ƙulafucin uwa gareta kamar dai SARAUTA haka take, sometimes shike ɗaukan ƙafa yaje wajanta yana cewa yaje biko.
Tuna wannan karamcin na Al'mustapha yasa Baffa faɗin.
"duk da cewa ina da iko akan abinda zan aiwatar amma dole dai na nemi amincewar ka domin kai ka haifi Aysuhtul humaira, Ina gdy ƙwarai da wannan karamcin ka nuna min nima mahaifi nake gareka kamar yadda nake mahaifi a wajan Matarka (Aunty Meera)".
Casbahar hannunsa ya ajjiye tsohun yasan me yake duk da cewa ya tsufa ainun amma sosai yake da himma da kuma saurin fahimtar abubuwa masu muhimmanci.
Yaransa ya kalla sannan ya kalli  jikokin nasa a nutse yace.
"Haruna fito min da dukkan abinda yake aljihun ka"
Baba Haroon ya sanya hannunsa ya ɗauko harfar kuɗi ta 500 wanda ya kasance 50k ne, kuɗin ya ajjiye gaban Baffa da sauri kuma yasa hannu ya ɗauki zoben daya faɗa daga cikin kuɗin.
Zoben Ya Heemu yabi da kallo sai kuma ya janye idanunsa yana maida kallonsa ga Wayarsa.
Baffan yace
"A bisa abinda yake faruwa ga yaran nan ni kuma na yanke nawa hukuncin da nake ganin shine dai-dai da abinda nai nazari, dan haka na bawa Omaru auran Aysuhtul humaira, bisa sadaki dubu hamsin Allah ya sawa Auran albarka"
Gaba ɗaya suka amsa da Ameen.
Nan Baba Haroon ya zama waliyin Ango Ya Omer sai Kawo Shuriem ya zama waliyin amarya.
Ya Omer wani hawayen farin ciki ne ya sakko daga cikin idanunsa ya rungome Baffa yana masa gdy.
Moha kam shiru tai sai zare fararan Idanunta masu sheƙi wanda kamarsu ya ƙara fita sak dana Ya Heemu.
Ji tayi abu mai girma da kuma nauyin gske ya danne mata kai.
Yayinda bugun zcyarta ya tsananta, ƙarfi da harbawar ko wacce ƙofa da take jikin zcyrta ya ƙaro fiye da ko wanne lokaci.
Cikin rashin makamar abinyi da kuma rashin gane ainahin abinda yake faruwa idanunta ya fara fidda wasu zafaffun hawaye mai fidda zafi da kuma kala, yadda hawayen suke gudu a saman farar ƙyakkyawar fuskarta zai sanya ka tabbatar hawayen bana jin daɗi bane sam-sam ko kaɗan.
Duk wannan abinda ake idanunta yana kan Ya Heemu ita kanta ba tace ga kallon da take masa ba.
Wasu abubuwa na shekarun baya suka fara dawowa gareta da tunanin, Shadow'n photon abin ya fara yawo cikin ƙwayar idanunta masu fidda ƙyallin zaiba.
Ya Heemu ya ajjiye wayarsa ba tare daya kalli kowa na wajan ba ya mayar da ganinsa kan Baffa yace
"Baffa ina da buƙata"
Shafa kansa Baffa yay yana mai jin so da kuma ƙaunar Ya Heemu na ƙara huda ƙofar jijiyoyin zcyarsa.
Cike da kulawa yace
"Haba zakina, faɗi ko mene indai maifi ƙarfina ba Tabbas zan maka"
Lumshe idanunsa Ya Heemu yay yana tsotsar laɓɓansa wanda suka gama yin jaaa sbd azabar da yake gana masu wajan cijesu.
Numfashinsa na fita ɗai ɗai yana samun daidaito a tsakiyar ƙahon zcyarsa wacce take wassafa masa dukkan abinda yake yana fesar da kuntun numfashi mai zafin gaske tare matsawa sosai wajan Baffa nasa cikin ƙasaitacciyar muryarsa wacce ya gama dai-dai ta yace.
"Aure na keso ka nema min, Nima yau na keson Auran ya kasance"
Jinjina kai Baffa Yay domin daman abinda yake jira kenan bashi da Burin daya huce ya ɗauki baƙaƙen yaran Ya Heemu wanda yake fatan su ɗauki baƙar fatarsa sbd jar fatar ta ishi idanunsa da gani.
Yana Murmushi yace
"Kada ka damu gaya min Wacece wacce kake so, kuma ƴar ina ce waye mahaifinta"
Idanunsa ya lumshe yana kokawa da Numfashinsa wanda ya ke son fallasa a sirin zcyarsa yace.
"Baffa Mumyn Arman na keso"
Ba Baffa ba hatta Moha da take ƙarama sai data ɗaga kai ta kalli Ya Heemu haka Ya Omer da sauran mutanan cikin ɗakin.
Sam Baffa bai mmki ba sbd Uncle ɗin Mannal ya jima da faɗa masa, kuma ya amince da haka sbd babu haramci ciki, fiyayyan halitta ma ya auri wacce ta girmesa so dukkan abinda za'ai koyi dashi bai huce nasa ba, kuma daman shekaru ai lamba ce kawai.
Kawo Shuriem yace "Khalel mariƙiyyar taka? Mahaifiyar Arman best friend ɗin Hjy Ruma fa?"
Ko kallan inda yake Ya Heemu bai kalla ba Baba Haroon yace
"ikon Allah kenan"
Uncle Aliyu kam Shiru kawai yay dan ba komai kake jin yay mgna ba, sai abu mai muhimmanci yanzu ma har yay Shiru sai kuma yace.
"Son a shekarunka? Baka son mure ƙuruciyar ka ne? Mannal fa, this is difficult dear age mate ɗin Mahaifiyar ka"
Alhj Al'mustapha yace
"Ai age is just a number ba dai shi yaji ya amince ba to Allahamdulillah ai, kawai ku saka albarka is better than talk"
Baffa yace "Aliyu kiramin Mahaifin Mannal"
Ba musu ya kira ya bawa Baffa suka gaisa Suna jin sanda mahaifin Mannal yace "ikon Allah"
Ya Heemu kam jikinsa yaja zuwa na Baffa yana yanayinsa na sauyawa ya shiga tasbihi a ransa yana ƙara kwantar da kansa jikin Baffa.

AUREN FANSAWhere stories live. Discover now