BA LABARI 1-2

664 37 4
                                    

BA LABARI
      By
Fadeela Lamido

EXQUISITE WRITER'S FORUM.

                 PAGE 1 -2

Bismillahir Rahamanir Rahim.

Manyan motocine guda guma zafafa ke shigowa cikin unguwar, banda kyalli babu abun da motocin keyi yayin da suke tafe cikin nutsuwa.

      Sannu ahankali take tafiya cikin babban hijjabinta tare nikaf dinta baki yayin da hijabinta ya kasancen kalar sararin samaniya, karan motocin da takeji ne yai masifar gigitata, yayin da yai sanadin gushewar hankalinta, diriricewa ne da dimuwa ya same ta lokaci guda wadda ya haifar mata da rawan jiki tare da gushewan hankali harya kaita da curewa guri guda.

       Hayaniya ne ke tashi bisa kanta, cikin yanayin firgici take jin muryan maza saman kanta suna fadin, " sannu ba dai kiji ciwoba ko?"

       Wata muryan taji cikin fada ana fadin, aigara taji ciwon ko Yayane, tunda musamman ta shigo da tsuguna saboda tanason tajawa mutane bala'i toh Allah ya fiki, idan mutuwa kike nema dan ubanki kije ki tari tanka, dallah tashi ki bamu waje, cikin tsawa yake mgnr, kokarin tashi take ta hangi wasu  karafuna wadda ke zama wa mara lafiya kafa suna tahowa gare ta.

     Sandunan karfin tabi da kallo batare da tabi tsawon sadar ba, lumshe ido tayi alokacin data hangi wata kyakyawar kafa  fara sol cikin cikin wani tsandanden takalmi, kallonta ta maida Kan daya kafar wadda sai wannan lokacin ta kula da ita, daure take tam da dauri irin na wadda ya samu karaya ko wata mummunan matsala, dan an nade kafar tunda Kan tafinsa har ya wuce kaurin sa.

    Yajima tsaye agabanta saidai ta kasa dagowa ta dobe shi, yayin da ta kasa cire idon ta akan daya kafar sa me lafiya, kuma ta kasa mikewa gaba daya.

      Ahankali taji yayi gyaran murya kadan, wata irin murya taji me cike da kasaita yana fadi ahankali, " tashi ingani babu wata matsala da ta sameki ko?"

        Ko motsi batai ba yayin da idon ta ke iya hangen kafafuwan su, zasu iya kaiwa kimanin mutum ashirin, kuma dukan maza ne cikin kayan alfarma da takalma masu tsada, wani abun Mamaki ada dukkan nin su mgn suke cikin hayaniya, amman wannan me rike da karfin na fitowa gurin yayi tsit.

       Kamar daga sama ta sake tsintar irin wannan muryan tana sake fadin, " Ina magana dake ne fah"

            Wannan lokacin ma bata tankashi ba yayin da takeji ajikinta kallonta yake saidai ita bazata iya kallon nasa ba.

        Ke bakiji ne ana miki magana dan rainin hankali kinyi banza da mutane, tashi ki bamu waje, nasame ki agurin nan takaki zan yi, wani dake can gefe kifadin haka cikin tsawa da hargagi, tsintan muryan mutumin dake tsaye agaban ta tayi Yana cewa, " Magaji bita ahankali"

       Bata sakejin muryan wani ba duk suna tsaye yayin da kadan daga cikin su suka koma mota suka zauna.

        Kyawawan kafar ta ya zubawa ido sannan ya koma kallon idon ta dake cikin ni'kaf, kasa cire idon nasa yayi har aka dauki tsayon lokaci, sosai idon nata ya burgeshi har baya iya misalta wa, tare da kasa cire idonsa akan nata, acikin ransa yake fadin ban taba ganin idon dayai kyau da ni'kabi  kamar wannan idon ba.

          Tsayon lokaci suka diba babu me cewa komai, zuwa can taji anbude motar sannan taji ance, Modibo kazo mu tafi dan Allah, muna da abunyi fa, sannan akwai tafiya me tsayo agaban mu.

       Ta kanta zamubi ne?, baka ganin ta zauna ahanya?

         Tahowa yayi Yana fadi cike da fada ke!! Dallah tashi......

    Shiii  ka koma ka zauna harsai lokacin data tashi.

        Afusace ya juya yayin da gurin ya sakeyin shiru tsayon lakaci.

BA LABARIHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin