BA LABARI PAGE 17- 18

239 18 0
                                    

BA LABARI
      By
Fadila Lamido

EXQUISITE WRITER'S FORUM.                
      

                      Page 17- 18

   Bude idonta tayi adaidai lokacin da da Modibo yasa kafarsa acikin dakin, cikin tsananin mamaki take binsa da kallo, domin kuwa tasan karfi cire kofar nasa ne bane me muryan da da taji d'in ba, tambayan kanta tayi toh muryan kuma da taji d'azon d'in fa?

     Kafin ta gamawa kanta wannan tambayan taganshi yana takowa abayan Modibo, hakan yasa tai saurin tashi zaune batare data sani ba, kallon sa tayi sosai sannan ta maida kallon ta gurin Modibon dake tsaye fuskarsa daure tamau babu alamar wasa"

          Ganin inda ya tsare ta da kallon tuhuma ya sa tai saurin sunkuyar da kanta kasa, cikin kwalkwal da Ido, zuwa can tajin Modibo na fadin, " ita ce ko?

      Itace Mana Modibo, ai tunda muka shigo wannan Unguwar na shaida ita ce,  domin babu wata  yariya dake da d'abin daka lissafa.

           Lumshe Ido Modibo yayi na tsayon lokaci zuwa can yace, "wani irin labari kaji akan ta?

         Kawai dai ance iyayen ta sun rasu tana zaune ita daya kawai, kuma ni kaina ganau ne, domin bata mu'amala da kowa, sannan wani abun da zai baka Mamaki Modibo na dade Ina zuwa gidan nan wlh tak bata taba cemin ba, kuma duk wadda namai tambaya sai yace min tana mgn ba kurma bace, mgnr duniya nayi harna gaji, kai ta taba maka mgn ?

      Matsawa Modibo yayi bakin gadon ya yaye mayafin data rufa dashi yana fadin, "abun da kazo dashi mata dashi ni bada shi nazo ba, wurgi yayi da bargon tare da cigaba da fadin, bance miki karki kara kin bude min kofa ba?, Ke! Kin sanni kuwa?

      Ganin yadda ta sunkuyar dakai Suraj yayi yar dariya wadda bakai ciki ba, sosai ya kula mazoran Modibo yayi tasiri a gare ta, dan haka yai saurin fadin, "kai mata hakuri Modibo, anan gurin ita ta ganka, batasan wanene kai ba, daman hakane, wani tsutsu na gudun ruwa ne agwagwa kuma a ciki take  kwana.

         Afusace Modibo ya kalli Suraj Yana fadin, " ai samun yarda ga dodo kesa ashiga ruwa lafiya, na sake zuwa na buga kofar baki bude wlh saina nuna miki wasan kokawa bana gurguwa bane.

      Har yanzun bata dago kanta ba yayin da Suraj yabita da Ido yana mamakin yanayin ta ayau.

     Shikuwa Modibo wayarsa ya daga Yana kiran Magaji domin tun Jan bargon da yayi ya gane da zazzabi ajikin ta, bayan Magaji ya daga ya shiga fadin, " ka nemi wani asibiti mafi kusa ka taho min da likita, yariyar nan Bata da lafiya.

      Sauke wayar yayi ya fice, yayin da Suraj ya bishi da kallo, bayan ya tabbatar da fitan sa ya hadiye yawon bakin sa Yana fadin, Kin gane ni?

      Batare da tace komai ba ta juya kawai ta kwanta, domin zuwa wannan lokacin ta fara jiran tsammani kawai, Bata da wani abun yi dan haka tafi bukatan ta mutu kawai ta huta.

           Fitowa Suraj yayi ya samu Modibo ya saki tsuntsayen yana watsa masu gero, yayin da fuskarshi take tattare da bacin rai.

        Wad'an Nan tsuntsayen fah?

    Saida Modibo ya had'iye yawon takaici sannan yace, " nakawo mata ne dan ta dan dingajin motsi a gidan, amman na kula tun bayan dana kawosu Bata Basu abinci ba, Ina nufin Sam bata kula dasu ba, Suraj ina son dana gama amsan magani intafi da yariyar nan, Ina tunanin inyiwa Malam baba mgn akanta, domin musamu wani daga cikin dangin ta dazaiba ni ita intafi da ita, Ina son rayuwarta ta canza, bedace ace muna barin irin haka na faruwa ba, dan iyayen ta basa raye bashi dalilin zaman rashin galihu ba, kuma ba yana nufin rayuwarta ta kare haka bane, ba yadda za'ayi ace bata da dangi dan babu wadda yake fad'owa daga sama, duk wadda kagani acikin duniya mace da namiji ne sukai sanadin zuwan sa duniya ko da aure ko babu, dan haka nasan dole tana da dangi saidai ace ba asan in da suke ba.

BA LABARIWhere stories live. Discover now