Chapter One

20 1 0
                                    

Baƙin ciki, takaici tare da burin mutuwa sune suka dabaibaye ni a halin yanzu, bani da wani burin daya wuce naga mala'ikan ɗaukan rai a gabana yazo ɗaukan rayuwata. Na daɗe ina burin yin kuka kamar yanda sauran mutane suke yi amma na rasa wannan damar ta ganin kwaranyar hawaye a kumatu na. Kuka nake da hawaye amma a zuci, ni kaɗai nasan raɗaɗin da nake ji a cikin jikina.
    Ashe haka so yake da zafi? Ashe illar so tafi amfanin sa ga ma'abota soyayya? Ashe rabuwa da masoyi ta banbanta da rabuwa da sauran abokan taraiya? Ashe mace ba abar yarda bace?
    Na zaci nafi kowa sanin so tunda na tsunduma cikin tekun sa, na zaci nafi kowa dace aso tunda na gagari abokan takara ta har na auri muradin raina, na zaci na kafa duniyar so wacca ba zata taɓa gushewa ba tunda na yalwata gida na da so da ƙauna, amma ban sani ba ashe da saura na, ashe dai akwai wani babban darasin da ban sanshi ba a baya. Yanzu farin ciki na ya gushe, dariyata ta mutu, murmushina ya ƙare, walwalata ta tsaya, babu abinda nake yi sai hawayen zuci...

HAWAYEN ZUCIWhere stories live. Discover now