Chapter Two

10 0 0
                                    

Ƙaddarar saduwata da Amra ta samu asali ne a maraicen wata ranar asabar. Bayan na baro wajen sana'a ta ina kan hanyar komawa gida, kwatsam sai idanu na sukayi arba da kyakkyawar matashiyar budurwa mai tsananin kyawun zati wacca gaba ɗayanta bata wuce shekaru goma sha bakwai ba. A take iduna suka gamsu da kyakkyawar siffarta, hanci na yaji mun daddaɗan ƙamshin turarenta mai kamar almiski. Ba zato ba tsammani zuciya ta ta tsunduma cikin bege da ƙaunarta.
    Hakan ne yasa na gaggauta tunkarar ta domin in gabatar da kaina a gareta.
    "Amincin Allah ya tabbata a gareki yake ma'abociyar kyau da ƙyalli".

Sai ta kalle ni cikin rashin fahimta ta ɗan hautsina fuska cikin salon ƙasaita da jan aji, amma hakan bai sa na karaya ba...

    "Duk da ban taɓa arba dake ba kafin yanzu, amma ina da yaƙinin cewa ke musulma ce, dan haka na tunkare ki da sallama a matsayin furucin farko. Hmm amma abun mamaki sai naga kin kau da kai a maimakon amsar sallama"

Dajin maganata sai ta ɗan saki fuska cikin izza ta kalle ni sama da ƙasa kafin ta amsa mun sallama ta

    "Amin wa alaikumus Salam".

Nan take naji jijiyoyin jiki na sun ƙafe, jinin jikina ya harba, bugun zuciyata ya tsaya cak, ba zato ba tsammani naji goshi na ya jiƙe da zufa, ƙafafuna suka fara rawa, duk saboda jin zaƙin muryar da ban taɓa jin irinta ba a tarihin rayuwa ta. Maganarta ta gaba ce ta dawo dani hayyaci na...

    "Bawan Allah lafiya dai ko?"
Shine abinda naji ta faɗa...

"Hmm lafiyayyar lafiya Baiwar Allah. Ki gafarce ni, amma a yau naga abun da ban taɓa gani ba, a yanzu naji sautin da ban taɓa ji ba, a zuciya ta naji daɗin da ban taɓa ji ba. Idan baki gane ba, ina nufin irin abinda turawa suke cewa 'Love at first sight',. Tabbas hakan nake ji da gaske, ki taimaka ki shigar dani duniyar ki, ni kuma zan rayu a ciki ba tare da nayi ɓarna ba".

Wannan ita ce ranar data fara sauya min ƙaddarar rayuwa, a tunani na So shine maganin dukkan wani ƙunci da baƙin ciki. Ban sani ba ashe holoƙo ne na farin ciki mai ƙare wa da Hawayen zuci...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 08, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HAWAYEN ZUCIWhere stories live. Discover now