CHAPTER 1

861 74 17
                                    

Mika mata ledan tayi tare da yin murmushi tace nagode sosai sai kin kawo wani dinkin budurwar da ta kawo dinki tana gyara gashinta da ya leko zuwa cikin hijabi tace insha Allah nima na gode kin cika alkawari.

Maryam tattare tsummokaran dake zuzzube a wajen keken dinki ta tayi ta daure dan zata hura wuta dashi anjima sannan ta shiga kitchen ta dauko abinci a kwano ta nufi dakin kakar ta. Da sallama ta shiga kakar tana zaune tana karanta littafin hadisi. Murmushi tayi mata maryam tace kaka ya jikin naki ya fada ko. Tace garau nake kamar ke.

Turo baki maryam tayi tace ni gaskiya ki dena boye min kaka na girma fa in baki fadamin matsalar ki ba wa zaki fadawa. Rufe littafin kakar ta tayi tace kuma kinyi gaskiya anan. Abincin su ka ci kakar tana mata nasiha kamar kullum inda ta kare da cewa shi halal fa halal ne ko ke kadai kike yi kuma haram haram ne ko duk duniya sunayi.

Rungumar ta maryam tayi tace nide nayi sa'a kuma nagode sosai da Allah ya bani ke. Fitar da kwanon tayi tana shirin tafiya islamiya ta jiyo kakar ta tana tari kamar ranta zai fita. Kamar an shake ta an danke mata zuciya haka taji kakar ta bata lafiya kuma basu da kowa Allah ya wadaran matar nan. Wace irin mace ce zata bar maman ta da yarta me wata uku ta shige duniya bayan ta san sarai mahaifiyar tata tana dauke da tsohon cuta.

Haka de maryam ta shirya ta fita gaba daya ranta ya baci tana me kara jin takaicin wanda ta haife ta tana fatan inama zai yuwu ta samu ta falla mata maruka ko zata huce saide kash.

..............

Dattijawa ne ke saukowa daga bayan wata mota su biyu da ka gansu kasan mayan mutane ne masu mutunci da sanin darajar mutane sannan basu kasance masu almubazzaranci ba dukda budin da Allah ya musu.

Daga kofan babban parlour governor ya fito da kaga fuskar sa kasan bai tsammaci zuwan mutane masu kwarjini irin haka ba dukda bai sansu ba. Abin da ya dan dame sa shine yadda aka yi suka shiga government house ba tare da an sanar masa har sanda suka wuce.

Saide fa bai bari sun gane abin da ke ransa ba inda ya miyar musu murmushi kamar yadda suka masa musabaha sukayi kamin dayan daga cikin su yace afuwa muke nema kaga munyi zuwan ba zata.

Governor yace ba komai ba komai saide ban waye ku ba cikin harshen turanci. Wanda ke hannun dama yace sunana Alhaji abba wannan aboki na ne sunan sa alhaji jibril kuma munzo neman aure ne.

Governor de hankalin sa be gama kwanciya ba saboda zamanin yanzu in kashe shi sukanzo yi fa amma ganin cewa dole an buncika su kan suka shigo yasa yamusu iso ciki saide fa a ransa ya riga ya sha aniya inde ba kusar gomnati bane ke neman auren bazai bada ba saboda yanda son abin duniya ta masa kakatu.

Da yake ya nuna musu guri kamin ya sanar wa hajiya bahijja wato matar sa ta talho cewa yayi baki. Kamin kace me an shisshigo da abubuwan ci da sha saide bakin nan biyu ba wanda ya taba komai a ciki.

Kallon su yayi yace bismillah da dan raini a yanda yake kallon su amma de bai fito karara ba. Murmushi suka sake masa kamin daya daga cikin su ya dauki mofin da aka zuba juice a ciki yayi kurba daya sannan ya ajiye.

Yace Alhaji bazamu tsaya dogon magana ba kamar yadda muka danar dakai munzo nemawa wa danmu auren yar ka zulaiha ne. Alhaji abubakar dattijo ne ya aiko mu ni kanin sa ne kuma kamar yadda na fadan wannan aboki na ne.
Gaban sa ne ya fadi raras dalili kuwa saboda Alhaji Abubakar dattijo shine minister of finance a yanzu. Saide dalilin da yasa aka bashi minister of finance kuwa saboda shine tsohon shugaban EFCC a lokacin sa ne aka kama barayin gwamnati kamar ba gobe kasa ta samu kudi rayuwar al'umma ya samu saraha.

Saide be samu gyara abubuwa duka ba aka canja shi toh zuwan sabon shugaban kasa yasa aka bashi tattalin arzikin kasa a karkashin sa. Daidai gabanin zai sauka case din gomna ne a hannun sa amma kamin a faea bincike ya sauka. Da sabon yahau kuma yayi binciken boge ya watsar da batun.

Paper Alhaji abbas ya zaro ya mika masa tare da fadin yace idan munzo mu baka wannan. Gwamna na karantawa gumi ya tsattsafo masa. Ajiyan zuciya yayi yace ku bani minti goma zan gana da mahaifiyar ta.

Yana shigewa wata hanya su Alhaji abbasa suka kalli juna sude basu taba ganin irin abu haka ba kawai minister ya taso su da paper yace suje neman aure shikenan.

Gwamna yana shiga bai kula masu aiki dake gaishe shi ba ya bude kofan dakin matar sa ya shiga yar su yar lele na kwance a cinyar ta tana lissafo abubuwan da take so a siya mata. Tana ganin shi ta mike tace daddy sannu da shigowa. Sama sama yace mata sannu abinsa be saba ba dan haka ta turo baki shafa kanta yayi yace babyn daddy dan bamu fili kinji. Ganin zata bata masa lokaci yace zan canja miki mota next week.

Da hanzari ta fita tama tsalle zuwa dakin ta kamar wata yarinya dukda ko already tayi shekara 17. Tana fita yace hajiya ta cabe mana. Annashuwan dake fuskan ta ne ya dauke tace kamar ya? Nuna mata papern yayi bayan ta karanta tace ya zamu yi. Gwamna yace dole mu bada mana. Hajiya tace gaskiya ban yarda ba nawa nawa zulaiha na take kuma ba kasan fa yaron nan Mubarak take so dan gwamnar jihar ***** kuma baka ji me ya rubuta bane ka bada auren yarka har sai ta haifa wa  karamin dansa jini karfa ka manta karamin dansa gurgu ne, an kasa warkar dashi baya magana sannan naji ance bazai iya yin abin bama toh tayaya zata haifi dan?

Kuma wai sai hakan ya faru duk kudin da muka sata da sunan yin aikin muyi aikin da kudin mu ba da sabon budget ba. Mangaran kafadanta gwamna yayi yace ara zakice ara zakice hajiya. (😂😂kai jama'a) yanzu de menene abinyi ?

Yanzu de me abin yi? Shiru tayi tace gaskiya bazan bada yata ba. Kasan de in muka bada ita mun kassarata ko? Yace in muka ki kuma kurkuku zan shiga fa. Tagumi tayi tace ai kajo matsalar zamani da ba social media kawai canja ta zamu yi da wata amma yar iskar yarinyar nan kullum tana cikin watsa hotuna.

Rike hannun ta gwamna yayi cikin jin dadi yace kin kawo shawara me zai hana mu samo wata yarinya sai muce ita ma diyar mu ce amma a wajen yaya na ta taso tun sanda aka kaita yaye bata dawo ba. Shiru yayi yace amma wani hanzari ba gudu ba.

A ina zamu samo yarinyar da zata yi yadda muka ce ta rufa mana asiri. Fuskan hajiya ne ya dan canja murmushi yayi yace hajiya ta nasan kina da sbin fada daga ganin yadda kika yi da fuska menene kina da suggestion ne?

Kallon shi tayi bayan taja dogon numfashi tace Alhaji zan fada ma wani abu amma da sharadi kayi alkawari cewa bazaka sake ni na ko me zance. Yace tufda bakin yawu my lady me zaisa in sake ki? Ai in kika ga na sakeki saide in kashe iyaye na kika yi. Tace be ma kai nan ba. Umm ka tuna sanda ka aureni yace sosai ma.

Ba a budurwa ka aure ni ba na taba yin aure har na haifi yarinya saide na boye maka ne saboda ina tsoran kar ka ki aure na. Jimm yayi kamin yace karki damu ina yarinyar? Dan tsimewa tayi tace ban de sani ba ko tana raye ko bata raye tun tana wata uku na barta amma naji de kamar ban de tabbatar ba fa. Yace fadi ki dena dari tace naji ance har yanzu tana nan tan dinki da tuyan kosai yace maza shirya hajiya shirya yanzu kije ki daukota bai bata kofar yin musu ba ma duk ya rikice ya fita.

Yana komawa bangaren sa yayi yake ya zauna kamin yace toh Alhaji abbas mun yanke shawara tunda baku bata mana lokaci ba muma bazamu bata muku naku ba. Zamu baku babbar diyata saboda karamar an riga anyi alkawari da wasu nan de aka tsayar da komai har rana suka sa za'ayi aure nan da wata 3 su Alhaji abbas de toh basu taba ganin abu irin haka.
Haka suka kama hanya domin isar da sako.

DON'T FORGET TO VOTE,COMMENT AND FOLLOW ME ON WATTPAD miss_untichlobanty

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

miss untichlobanty 💕

MATAR CANJIWhere stories live. Discover now