CHAPTER 8

908 97 50
                                    

Suna isowa ta sauko gaban ta na faduwa ba wanda ya rakota ba me tarbarta sai kace tsinanniyar kaza. Knocking tayi aka bude wata me aiki tace sannu da zuwa driver dake tafe da akwatinta ya mikawa me aikin.

Yace this is the new madam da sauri me aikin ta gaisheta sannan ta wangale kofa. Bismillah maryam tayi sannan ta shiga tana me ajiyan zuciya da jiran abinda kaddara zai wullo mata.

Saide tana shiga tsakiyar parlour sai ta dake toh ina zata yi gida da dakuna bata san ko ina ba. Ganin ba sarki sai Allah yasa ta juya ta kalli Wanda ta bude mata kofa tana jiran a mata bayanin inda zata nufa.

Murmushi mai aikin tayi mata sannan Tace madam bari na nuna miki dakin ki. Gyada kai maryam tayi sannan tabi bayan me aikin tana kallon abubuwan dake parlourn tana tunanin yanzu anan zan zauna ko?

Toh in an sallami kaka ta ina zan kaita? Allah ya kiyaye na kaita gidan maci jan nan dole na fara wata sana'a na tada kudin da zan samu ko gidan haya na kama mata ne.

Dai dai lokacin me aikin ta nuna mata kofan wani daki tace madam ga dakin ki nan godiya maryam ta mata kamin me aikin tace sunana zainab nice wacce zan dinga kula da harkokin ki in kina bukatan wani abu ki kira ni ta hanyar talho.

Gyada kai maryam ta sake yi tace toh ba komai nagode. Tafiya mai aikin tayi bayan ta janyowa maryam kofa ajiyan zuciya maryam tayi ta lalumo wayar ta tayi tagumi bata ma san me zata yi ba.

Shin be kamata ta ga sirikan ta ba? Kawai an kawo ta daki? Toh me zata yi yanzu kenan taci gaba da zama kamar tulun kayan wanki?

Ganin de babu sarki sai Allah yasa ta mike ta fita ai de da nawi kazo gidan mutane ka shige daki kuma gobe ko anjima ta fito da niyar taci abinci a gaban su?

Kai ita ta rikice ma. Kiran zainab tayi tace ina babban madam ? Zainab tace babban madam sunje wani reception  har zainab zata tafi maryam tace um nace ba ina.... umm.

Murmushi zainab tayi tace karamin oga ya tafi asibiti duba kafar sa ko wani wata ake masa check up. Sosa kai maryam tayi jin kunyar yanda zainab ta ranfo ta.

Gyada kai maryam tayi alamun godiya sannan ta koma daki taci gaba da aikin tagumi bayan kamar minti 5 ta janyo wayar ta kunna wa'azi me taken "hukuncin laya a musulunci"

Can da dare yayi maryam taji de shiru ko tafiya kake kana jin sautin kafar ka tsabar rashi mutane fita tayi dan duba yanayin gidan tayi karo da zainab tayi wanda ke shisshirya abinci a kan dinning table.

Zainab tace yanzu nake shirin kiran ki ai maryam tace aiya na gaji da zama waje guda shine nace bari na fito. Ganin karan tv da maryam keji a parlour yasa ta juya ta nufi parlourn da zaman shiru gara ko tv ta kalla.

Ko da tazo taga yana kan peace tv bata canja ba kawai waje ta nema ta dofana mazaunan ta da ka ganta kasan bata sake jiki ba.

.........

Hilal da ya dawo bayan anyi sallah issha ya dawo gida. Ta wayar sa ya tura sako zuwa kitchen  cewa yana jin yunwa sannan ya zauna a parlour yana jira zainab ta shirya in ta bar wajen yaje ya ci abinci.

Remote ya janyo kawai yakai sunna tv program da ake bai masa ba dan haka ya canja zuwa peace tv. Ba'afi minti 10 ba yaji ana takowa zuwa parlourn  mamaki ne ya kamasa dan yasan cewa su ana kiyaye ka'ida a gidan in ba ya zama dole ba mata da maza basa cakuduwa saide in muharraman juna ne.

Toh me zaisa zainab tazo parlour wanda kamata yayi ta sannan botton kawai zai yi kara kowa yasan lokacin cin abinci yayi.

Kallon hanya yayi yaga bakuwar fuska ce gyara bakaken tabarau dinsa yayi yaga ta zauna da alamu bata lura dawhi ba tunda dama a kujeran sa yake zaune.

Ba'a dade ba yaji sautin daga dining table dan haka ya nufi can gaban maryam ne ya fadi ganin mutum a kujera ya wuce ta gaban ta da sauri.ta mike be kulata ba kamar ma be ganta ba dukds jikin sa ya basa ita ce matar da aka aura masa.

So yake yayi observing dinta tukun saide ganin yadda ta zabura kamar bera da aka takawa jela yaso ya bashi dariya. Binshi da kallo maryam tayi kamin a hankali tabi bayan sa dan bata bukatan wani ya fada mata shine mijin nata.

Ko da ta isa taga ya shiga space dinsa taja daya daga kujerun dake wajen ta zauna abincin shi ya fara ci ita kuma ta rasa me zata yi ko abin cewa can de ganin shirun yayi yawa tace umm ina yini? Shiru ba amsa hasali ma kamar be jita ba.

Ganin haka yasa taja bakin ta tayi shiru  abinci kadan ta zuba wa kanta da sauri da sauri ta cinye ta koma daki tabar shi yana cin abincin sa.

Koda ta koma daki akwatinta tayi ta bude ta cicciro kayan ta tace ta bude wardrobe da niyan saka kayan sai taga ancika mata su da kaya anjera shadodi sai atamfofi sannan laces abayu su vest haka da kuma kayan bacci jera wanda tazo dasu tayi tsarin yanda aka jera sannan ta dauko kayan bacci guda daya riga da wando na cotton da flower a jiki ajiye wa tayi akan gadon ta shiga bayi.

Ba wani hayaniya ko abin azo a gani na tashin hankali bayi ne me kyau kawai kuma damuwar ai ka biya bukatar ka ne. Wanka tayi sosai da dumi ta ma rasa tunanin me zata yi. Fitowa tayi da niyar daukan towel  taga wayam ita dama ta saba in tayi wanka dauro zani take tasa hijabi ta fice hankalin ta shaf be bata ba kayan ta kuwa kar ma ayi batun da yayi sharkaf da ruwa.

GODIYA NAKE YAN UWA A CIGABA DA TAYANI YADAWA DAN ALLAH NAGODE SOSAI

Miss untichlobanty 💕

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 12, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAR CANJIWhere stories live. Discover now