Chapter 5-6

38 0 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

*ZAƁIN SHI NE..!*

🪂🪂🪂🪂🪂🪂

_Zainab Habib(Mom Islam_


*Bismillahair rahmanir rahim*

*_Ina miƙa godiyata ga Allah daya bani iko dakuma aron rai ,na sake rubota wanan littafin mai suna a sama ,ina roƙon Allah ya baki ikon kammalashi cikin ƙoshin lafiya_*

_NOTE_  *_Bance dole ki karanta min littafi ba ,kuma wlhi duk wacce ta zageni a wanan littafin  bazamu wanye lafiya ba👌duk abinda kuka gani anayi ne shiyasa na rubuto ,ban saki dole ki karanta ba love and romantic ne_*

___________________________💕

Free Page 5-6

Baba yace "gaya mata dai Gadanga "Umaimah dake zaune kanta a ƙasa bata furta ko uffan ba ,har suka gama maganar , baba yace "nidai na gaya miki .

Bayan an ɗora abin karyawa sun karya ,baba ya ciri kayan da aka wanke masa yasa yace "idan na dawo nayi wankan , kallon agogo mama tayi kana tace "babansu ƙarfe sha biyu fa 12:pm har zakayi wanka "baba yace "ke ƙyaleni idan da kuɗi zan samu da nayi amma ko sisi bazan samu ba gara in tafi haka , ya ɗauki akwatin gyaran takalminsa kenan zai fita sukaji yaro yayi sallama , wlkslm sukace tare da fitowa dukkansu , baba ya kalli yaron yace "ya akayi ?"yaro yace "wai ana sallama dakai  ,gaban baba ya bada rass yace "Allah yasa ba wanan mayen mai gidannan bane "yaron yace "wani mutumi ne a galleliyar mota "da sauri baba ya ajiye akwatin tare da cewa "Allah yasa masu raba zakka ne ya fice ,mama da yaya Haidar da Umaimah suka bishi da ido.
Baba na fita ya samu mota ƙatuwa tsaye a bakin ƙofar gidansu ,jiki na rawa gaba na faɗuwa ya ƙarasa gurin motar yace "yallaɓai ance kana sallama dani "murmishi dattijon yayi kana yace "eh wlh baba inba damuwa ayimin izini da'akwai maganar da nakeso muyi "jikin baba na rawa ya leƙa gida ya ƙwalawa Haidar kira yace "maza fito da tabarma "cikin bin umarni yaya Haidar ya fito da tabarma ,baba yace "shimfiɗa a zaure "inda baba yace masa haka yayi bayan ya shimfiɗa ya durƙusa har ƙasa ya gaida mutumin harda cewa "baba ina yini "bayan ya amsa Yaya Haidar yabar gurin , dattijon ya gaishe da baba bayan baba ya amsa dattijon yace "wlhi wata yarinya na gani fara doguwa tana da ɗan jiki ta shigo gidannan "washe baki baba yayi kana yace "Umaimah kenan itace ai "mutumin yayi murmishi wanda ya baiyyana haƙoran makkansa guda biyu farare masu kyau , yace "ni sunana Alhaji Naira "kafin mitumin yakai ga ƙara magana baba yace "kana nufin kaine wanda ake nunowa a T V wanda yakeda gidaje dubu a cikin garin Jos "gyaɗa kai mutumin yayi alamun eh shine , baba yace "ikon Allah ashe zamu haɗu "mutumin yace "dan Allah baba idan ƴarka ce ina roƙon arziƙi da alfarma inasonta wlhi tun ranar dana ɗora idanuna a kanta na kasa kwanciyar hankali "washe baki baba yayi kana yace "ai ka kwantar da hankalinka naji labarin halin kirki irin naka mai zai hana in baka ɗiyata ,ai ka can canci a haɗa zuri'a dakai "godiya Alhaji Naira yayi kana ya miƙe yace "ni zan koma baba "baba dake jira a miƙo masa yace "Allah ya ƙara girma ,Alhaji Naira ya ciro rafar ƴan dubu ɗaya guda biyu ya miƙawa baba tare da cewa "zamu dawo da magabata na amma dan Allah ina son magana da ita Umaimahar "to..to...to baba yace "tare da godiya ya juyo takalmansa silifas yasa ya shige gida shi kuma Alhaji ya koma mota .
Baba na shiga ya zauna a tsakar gida yace "kowa ya fito "mama da Yah Haidar da Umaimah duk suka fito ,baba ya fito da kuɗin rafa ɗaya yace "kunga arziƙi har gida ashe ma mijin naki yana tafe nake ta yi miki magana ƴar lele ,yau shinkafa da miya da nama za'ayi dan ya jiƙani da nera "Umaimah da mama da yh Haidar da basu gane maganar tasa ba cikin haɗe murya sukace "baba me kake nufi ?"yace "kafin in fara magana Umaimah jeki waje ana sallama dake "Umaimah na turo baki tace "baba waye ?"baba daya zuciya yace "ubanki ne maza ki fita karya gaji da tsayuwa ki jaza  mana fitinar talauci "badan taso ba yaya Haida yayi mata magana da ido akan ta tashi ta fita , ɗaki taje ta ɗauko mayafinta ta yafa ta fice , tana fita taga mota irin ta jiya ,har zata wuce taji ance Umaimah yaki "da sauri ta juyo a zuciyarta tana cewa "mezan maka ?"zo mana Umaimah "Alhaji Naira yace "da sigar rarrashi , baba daya leƙo yace "tun daga gida nakeji ana kizo Umaimah kin fiya taurin kai au bazakije ba ?"Alhaji Naira dake murmishi yace "baba karka damu wlh , Umaimah yanzu kam ta gane me baba yake nufi amma ko babu komai zataje taji dame yazo "motar ya buɗe mata gidan gaba ,ta shige tare dayin bismillah  , zama tayi tare da gaishesa ya amsa yace "Umaimah tun jiya dana sanyaki a idona na kasa bacci wlh koda ƙwaƙƙwaran abinci na kasa ci "uhm "Umaimah tace "tare da taɓe baki tace "ai kai sa'an babana ne aure bazai yiwu dani dakai ba "dariya Alhaji Naira yayi kana yace "insha Allah aure ma ya yiwu ya zaki dinga cewa "haka

ZAƁINSHI CE..!Where stories live. Discover now