part 9

36 7 1
                                    

*FRIENDSHIP*
            *(ABOTA)*

*_SHOT STORY_*
_*[GAJEREN LABARI]*_

*E.W.F*

By
Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461.

          Page......10

Mama haby tace, "kai mun daidai ni baka tab'a burgeni irin yau ba Hussain, yo karatun me mace zata tsayayi har na shekara hudu a wata uwa duniya, ai kasan dole ne sai ta dauko maka magana............ya isheki Haby! Ya isa haka duk mugun alkaba'in da kike kirawa Noor insha Allahu badai akanta ba saidai a wani naki, ni nayi Imanin y'ata Noor ba zata aikata wani abu makamancin wanda kuke zarginta dashi ba, ba kuma don naji dad'in abunda akace tana yi bane kuskure ne babu wanda bayayi, ke waya san irin sab'on da kike aikata ma Ubangiji, ni nama godema Allah daya had'ata da mai hankali wanda yasan kanshi, na tabbata shi yaron da ace na banza ne tun tuni daga aiwatar da mugum nufinsa akanta, to zuciyarsa babu hakan aciki kuma inhar kai ubanta baka yarda da ita da tarbiyyar ta ba waye zai yarda da ita? In kana tantama ka kaita asibiti a duba maka idan ta rasa mutuncinta, sannan saika aikata masa duk abunda zakayi, sannan rashin cigaba da karatun ta ai ba kanta farauba, idan tana da rabo zatayi koda gidan mijinta ne."

Ammi na gama fadar haka ta wuce sa ta shige cikin mota mama haby sai masifa take wai ta zageta kuma Abby ya kasa daukar mataki, nidai kuka kawai nake kamar Allah ya aikoni sai yanzu nakejin bazan iya yin nesa da Annur ba, bazan iya rayuwa babu shi tare dani ba, duk da naji tashin hankali matsananci lokacin da yace bani ba makaranta aure xai mun, hakan bai kai rabin abunda nakeji ba akan kulle Annur da akai anata dukan sa, muryata harta disashe saboda kuka ayanayin da naga fuskar sa maganganun Ammi sun tsaya masa arai, kallona yayi ya daure fuskar tamau yace, "shiga mota muje"

Na tashi ina kallon hanyar da aka bi dasu Annur ko nace shi Annur d'in don su Hamid tun ba'aje ko ina ba aka sakesu, shi kadai aka bari andokesa duk anjimasa ciwo a fuska,ina shashshekar kuka nace "Abby don girman Allah kabarni naje na dubasa Abby shi marayane baida kowa sai maman shi, don Allah Abby karka dauki Alhakin sa bai aikata komi gareni ba sai Alkairi, zan iya dafa Alqur'ani na rantse dashi akan cewar tunda na fara karatuna shekara ta biyu kenan sau d'aya tak Annur ya rik'e hannu na, shima bada son rai ba. Abby ni zaka hukunta ba bashi ba saboda nice na bashi damar hakan"

Kuka nake sosai saboda ji nake har cikin raina dukan da akai masa, banga abunda Besty na yayi ba har da Abby zai masa wannan abun, kafin ma ya bani ansa mama Haby tace, "karya kike munafukar banza waye zai yarda da zancen karyar ki, kai daji ai kasan karyace"

Bai tanka ta ba yajuya ya figi hannuna mukai wajen mota, sham daman ita da baba azumi tun shigar Ammi motar suma suka wuce dayar suka shiga, motar da suka zo shida Driver da Ammi ya jefani sannan ya gayama driver ga inda zamu, ba wanda yace uffan har muka iso noor clinic wani asibitin kudi dake nan cikin katsina, mun samu mai asibitin dr nura Abby yai masa duk bayanin abunda yake so aimun, wani tuk'uk'in bak'in ciki ya cika mun zuciya wai ni zan bud'e jikina ma wani katon namiji na aurena yayi ba, ba haihuwa nazo ba wannan wane irin bakin ciki ne wannan Abby yaja mum.

Ammi kasa tsayawa tayi ta fice tana goge kwallah wani d'an daki muka shiga dashi yace na cire pant d'ina kwanta, jikina rawa kawai yake saboda abun bakone wajena sosai jikina yake kerma,ga hawaye share share suna zuba na bakin ciki da takaici Abby ne ya shigo motar sannan driver yaja muka tafi, waya yake yana cewa "ehy ku sake shi kawai"
Jin abunda yace yasa nai saurin tashi daga kwancen inajin wani farin ciki araina, amman bance komi ba har muka k'araso nan cikin sardauna gidan da muke, fitowa mukai mu duka gasu sham da baba azumi ga mama haby da ni da Ammi, gidan muka shiga Abbyn yace, "ku shiga ku tattaro yanaku yanaku ba wanda zai k'ara kwana agarin nan insha Allah zuwa magriba jirgin mu ya tashi"

Tunda na kwanta kan gadon d'akin ban sake koda kwakkwaran tari ba, gabaki d'aya na jina nake daban zuciyata cike take da k'unci da wata irin kewa dake taso mani, idan na tuna shikenan fa nida Annur bazamu sake ganin juna ba, sai inji zuciyata tana tsinkewa ban sanin sadda ruwan hawaye suke zirarowa kan kunci na, ko kadan rabani da karatun da akai bai girgiza ni ba irin kokarin rabani da Besty na da ake inaji kuma ina gani, shin dagaske Abby yake aurar dani zayyi? Bazan iya rayuwa da wani namijin ba muddin ba Besty ba, sai yanzu n tabbatar da maganar sham gaskiya ce cewa son Annur ya dad'e da girma acikin zuciyata, ina hango taya zan iya sabuwar rayuwa babu shi.?

Ban san sadda na sake sanya wani kukan ba wanda yake tasowa tun daga k'asan zuciyata yake fitowa sarari, ba wanda yace dani ci kanki kayan mu kawai ake kwasa ana fiddawa, sham da baba azumi sai Ammi ita maigirma mama haby ta hakimce falo ta saka apple gaba sai ci take kamar Allah ya aikota.

Duk wani abu mai muhimmanci namu an tattara an daure wanda bazai dauku ba an saka amotar baba mani kasurgumin munafuki, (😂😂 easy mana noor)
Duk wasu madaukan kayan mu gidan Abba kanen abby aka kaisu, zai aika mana dasu gida wadanda kuma basu nauyin muka tafi dasu airport, kamar kurame mu duka bamai iya cewa komi sai zabaya mama haby da keta zuna d'umi ba mai biyeta, acikin maganarta ne naji cewar yaya Yusra ta dawo gida gabana saida ya fad'i to meya maidota? Zuciyata tace mun "kila haihuwa tazo yi"
Duk da ansar bata gamsar dani ba amman ina fatan ace hakan ce takasance, bacci nai tayi ko acikin jirgin har Allah ya sauke mu lafiya.

Wanka na fito na iske yaya yusra zaune gefen gado na ta buga tagumi, tsaye nai ina kallon ta bata san ma nafito ba saboda zurfin tunanin data fad'a, saida na dafa kafad'arta tai saurin d'agowa firgigi tana kallona idonta cike da kwallah zama nayi gefenta nace, "yaya yusra kuka kike yi? Me akai maki haka?"

Sai ta sake sanya wani kukan mai ratsa zuciya cike da kunci haka kukan yake fitowa rungumeta nayi a jikina a haka tasha kukan har ta gode Allah, sannan ta fara cewa "Noor ban tab'ajin nayi nadamar biyewa zuciyata ba irin yan kwanakin nan, ina cikin nadamar abunda na niyewa usman muka aikata tun a malesia, noor hakika babu abunda yakai budurci muhimmanci a rayuwar mace, ban tabbatar da hakan ba saida usman ya nuna mun kowaye shi,

Duk irin kauna da soyayyar da mukai ma juna ni dashi bata hana usman ya wulakanta ni ba, saida na sakankance na bashi ragamar rayuwata sannan usman ya tsigeni daga jikin sa..............muryarta ta soma rawa jikinta shima yana rawar bakinta yana makerketa tacigaba da cewa, "har aka kawo lokacin da usman ke zargina da bin wanj namijin bayan shi, wanda zan iya dafa qur'ani bayan usman ban tab'a sanin wani d'a namijin ba, amman da yake shi abunda yake aikatawa kenan sai yake ganin kamar nima hakan take a wajena, noor nai nadamar sanin usman arayuwata da ace in ga wannan mummunan ganin da nayi gara na mutu, idona idon shi lokacin da yake video call da wata tsirara haihuwar uwarta, amman baiga laifin sa ba sai nawa saboda na nuna  fushina da kishi na, noor usman ya kalli cikin idona yace ya sake ni................ta sake fashewa da kukan mai ratsa zuciya, sai naji duk irin damuwar da nake ciki yaya yusra ta fini tausayinta ya ratsani jin irin abunda usman yai mata, lallai namiji d'an iska ne kuma ba d'angoyo bane lallashinta nai tayi ina bata hak'uri har tayi shiru nace,
"Yaya yusra ko wane bawa da kalar jarabawar sa inkika ji ta wani sai kiga ke ba komi bace, ki dauka ke taki jarabawar kenan kuma inhar usman ne ya cuceki ya dauki alhakin ki wallahi yaya yusra soon Allah zai saka maki, bazai barsa ba kuma zakice na gaya maki sai yazo yana kuka neman yafiyarki ki manta dashi kiji da abunda yake cikin ki, Allah baya zalinci kuma baya son azzalumi ki saki ranki kiyi rayuwarki cikinmu mu yan uwanki da iyayenki, tunda mu ai muna sonki"

Tana ajiyar zuciya tace, "haka ne Noor insha Allah zan tursasa zuciyata akan hakan, amman ke mekikai da Abby ya cireki a makaranta?"

Tashi nai naje na zauna wajen kayan shafa na bud'e mai nafara shafawa sannan nace, "yaya yusra shigen case d'inki da usman ne ya baroni daga makaranta"

Mamaki ya kamata sosai  tace "ban gane ba noor, kardai kice mun kin sallama ma wani kanki"

Girgiza kaina nayi ina cewa, "ko d'aya"

Na soma bata labarin *FRIENDSHIP* d'ina da Annur....................





Mom muhseen✍🏻

FRIENDSHIP (A BOTA)Where stories live. Discover now