BABI NA BAKWAI

173 14 0
                                    

RAHMA'S POV

Tunda na shiga kofan gida ina tsaye na kasa gaba na kasa baya. Addu'a nayi na nufi kofan shiga gidan. A falo momy da daddy ne suna zaune suna kallon TV.

"Sannun da gida Mommy, sannu da gida daddy" muryana yana rawa na gaishesu. Daddy ne ya iya amsa min da "yawwa." Ko kallo na baiyi ba.

Tablet ɗin jakana na ciro na miƙawa daddy ina mishi bayanin yadda mukayi da principal. A daƙile ya karɓa ya cire glass ɗin idonshi.

"Ko na second ɗaya bazan ɗauki ganin lalacewan tarbiyan gidana ba. Sau ɗaya idan naga abinda ya saɓawa tsarina to inshaAllah zan karɓe kuma kin gama zuwa makarantan." Idonshi a kaina.

"InshaAllah haka bazai faru ba daddy" jikina yana rawa na karɓi tablet.

"Momy ga tablet a school ɗinmu an bani." kaman bada mutum nake magana ba ko kallo na batayi ba taci gaba da cin chewing gum tana ta ƙara dashi. Naci gama da tsugunnawa gudun kar in tashi ya dawo min damuwa. Kuma dama nasan itace babban matsala na.

Wani kallo daddy ya watsa min alamun in tashi daga nan. Cikin hanzari natashi na hau sama.

Nasan wannan yaƙin ba'a ƙareta sai daddy ya tafi za'ayi abinda nake tsoro. Ina shiga na cire uniform ɗina na saka tablet ɗin a charge nayi wanka nayi sallah domin yau nagaji.

Ina zama na jawo jakana zanyi assignment naga paper bag da mus'ab ya bani. Cirowa ina murmushi. Ci nayi na naɗe bag din na mayar jakana domin idan aka gani to kashina ya bushe.

Yadda muka rabu dashi nasan ban kyauta ba, dan haka na ɗauko paper na rubuta mishi apology letter dan bazan iya mishi magana baki da baki ba. Kuma in mishi godiyan snacks dayake bani domin last one ma ba ƙaramin rufamin asiri yayi ba. Hakama da yau zai matuƙar rufamin asiri.

Momy haka kawai idan tanajin haushi na to bazan ci abincin gidanba. Kuma a yau yadda na kawo wannan tablet nasan banda abinci a gidan.

Maybe ma Mus'ab ya gama min magana kenan saboda ba kowa ne yake iya rayuwa dani ba saboda rauni na.

Tablet ɗin na duba naga ya cika. Sai a lokacin na tuna ban iya setting ɗinshi ba tunda ban taba yin waya ba ko wani abu makamancinsu.

Tunani na tsaya yi ko in bari gobe in kai wa principal ya duba min. Ko kuma in bawa Mus'ab yayi.

Nafarko principal baida lokaci na biyu kuma Mus'ab zaiyi wuya ya sake min magana irin yadda naga yayi zuciya ya chanza seat a school bus ɗin nan.

Kunnawa nayi nayita amfani dashi haka nayita shige shige, wasu abun na iya nayi setting wasu kam ina tsoron in ɓata. Zan bari kawai in kaiwa principal ɗin.

Dare ya tsala na kwanta inata tunane tunane har asuba yai. Sallah nayi na tafi kitchen domin haɗa breakfast. Sai wajen 7:15 na kammala. Wanka nayi na shirya domin nayi latti sosai. Ina fitowa naga daddy ya fito da trolley zaiyi tafiya. Gaishe shi nayi ya amsa chan ciki ciki na mishi addu'a Allah ya tsare hanya. Ko amasawa baiyi ba yaci gaba da tafiya momy tana binshi a baya sai harara nakesha.

Saida na bari naji fitanshi kafin na fito kofan gida dama tun ina ciki nakejin horn ɗin school bus a layin bayanmu.

Ina fita kuwa sai ga school bus ɗin ya iso. Kofa aka buɗemin nashiga ina kalle kalle ko akwai space kusa da window.

Mus'ab ne yake ɗago min hannu daga nesa yana murmushi. Nuni yamin da inzo ya ajiye min kusa da window. Mamaki nakeyi har na isa wajenda yake. Kaman bashi bane muka rabu jiya cikin wani irin yanayi.

"Top of the morning to you pretty wonder woman."

"The rest of the day to yourself" na amsa tare da zama a inda ya ajiye min.

"Wait, did you just answer this greeting, how did you know about it?"

"A wani littafi dana karanta THE ABANDON PRINCE."

Wata ƴar dariya yayi ya juyo yana kallo na. "Kardai kice min kin karanta littafin nan daga season 1 har karshe?"

"Nope, ban karanta last two season ɗinba. Inata nema ban samu ba."

"What if i can borrow you mine in return of us being friends? Because I have the last two seasons and even other ones you'd love to read."

Kallonshi nakeyi ina murmushi da mamakin yadda yayi saurin hakura da abinda ya faru jiya.

"Do you mind a question?"

"Yeah."

"Dan Allah sarki yana sawa a kashe budurwan prince ɗin. Almost every single day sai na tsaya tunanin yaya za'a ƙare."

"Idan na faɗa miki bazakiji ɗadinshi ba. Yana faɗa yana dariya."

Har muka isa school muna hiran novels ne da wanda na sani da wanda ban sani ba.

Nidai nasan ban taɓa sakewa da wani mutum ba bayan umma asiya sai Mus'ab. Kaman yamin magic sai hira muke muna dariya

Muna isa aka fara assembly. Ina ɗaga idona zanga Mr. AA yana kallo na.

Muna shiga class Mus'ab ya miƙo min envelop. A hankali na karɓa na tambayeshi menene wannan ɗin.

"Read. It's for you." Yana faɗa yana murmushi.

Na buɗe kenan Miss zainab ta shigo zata fara first period. Jaka na saka gudun kar a gani ys dawo min matsala, zan jira har ta gama class ɗin.

Tana fita saiga Mr. AA ya shigo zai fara second period. Tsayawa yayi yana ƙarewa yan ajin kallo wanda tun ana yan ƙananun magana har akayi tsit kaman ba kowa a ajin. Ido ya ƙura min wanda yasa naji hanjin cikina ya kaɗa.

Tunda ya fara class ɗin yana juyowa idonshi a kaina yake sauqa. Yana cikin koyarwa ya shigo da quiz tsakanin maza da mata. Haka akayita muhawara ana dariya.

Irin yadda ake musu da dariya yasa nima nayi joining ina dariya. Kallona yakeyi yana murmushi. Kawar da kaina nayi ban sake kallonshiba. Haka dai har aka gama class ɗin kowa yanata farin ciki da raha saboda yau anji daɗin karatun.

Break aka fita naga Mus'ab a zaune yaƙi fita.

"Ain't you going for break today?"

'Yes i am not going. I will only go if you will go too."

"You don't have to worry yourself over me going to the cafeteria. I hate crowd and noise and i am not hungry."

"Then let's go get something and find quite place and eat. There i will get to know you more."

"Uhmmm excuse me, mustapha can i send to the VP office to submit this files?" Mr. AA ne yayi magana.

Dukkanmu juyawa mukayi muna kallonshi dan munma manta dashi a class ɗin.

"It's okay sir. By the way it's Mus'ab." Tashi yayi ya dau files ɗin.

"Sorry i have been contemplating the name Mus'ab."

"Hey Mus'ab you should go and eat. Don't starve yourself to dead." Na faɗa ina ƙokarin buɗe jakana.

Yana fita na mayar da hanakali na kan envelope ɗin daya bani. Paper ne yayi rubutu masu kyau yana bani haqurin abinda yamin jiya. Kuma yamin alƙawarin bazai sake ba.

Ina murmushi nayi folding ɗinshi back na mayar jakana. Nawa letter na ɗauko nayi  saurin ƙara wasu abubuwan na saka mishi a jakanshi domin dama nayi niyan saiya fita zan saka a jakanshi.

Ina ɗaga ido naga wannan mayen mutumin sai kallona yakeyi. Allah shine shaida wallahi na tsani mutumin nan tun farkon haɗuwanmu gashi kuma yana ƙara sawa ina ƙara tsananshi saboda kallo.

        ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Masu karanta littattafin AMJAD ina godiya da kuma kara baku hakurin rashin posting akai akai.

AMJADWhere stories live. Discover now