*🍀SILAR FYEƊE🍀*
NA💋
UMMU MAHER(MISS GREEN💚)Wattpad user name
Rabiatu333Arewabooks
rabiattu044413🟪14
"Aliyu da ma jiya munyi magana da alajaa Hajara kan maganar aurenka da Ƴar wajenta Rasheeda shiyyasa na ce bari in faƊa maka idan yaso Sai Kaje ka ganta ku haƊa kanku."
Tunda ta fara magana Aliyu yaji ransa lokaci Ɗaya ya tashi,a halin da ya ke ciki yanzu na busy shi bai ga abinda zaiyi da wata mace ba,kai idan ma ya ce zai auren ai cutar matar zaiyi,kuma bayan haka ko da auren ma zaiyi zai auri mace mai kunya ne ba Rasheeda mara kunya ba,yana cikin tunanin ya jiyo Hajiya na cewa"ka tashi ka tafi Allah ya yi maka albarka na ji da Ɗin wannan biyayyar da ka yi min kai ma Allah ya baka masu yi maka".
shi dai admiral A.rasa me zai ce ya yi ya tashi ya tafi kansa na mai tsananin sara masa,ya shiga ban Ɗaki ya sakarwa jikinsa ruwa.
ya rasa me yasa ba ya son ko zancen aure?ya rasa abinda yasa kuma baya jin feeling a duk macen da ya kusanta,bai taɓa kuma son wata ɗiya mace ba tunda ya ke a rayuwarsa har kawo i yanzu da shekarunsa sun dushi 37.
***Wani irin hamdala gimbiya Salimat ta yi sannan ta ce"ranka ya daɗe ina mai miƙa godiya ta a gareka abisa son dukkanin farin ciki na matuƙar alkhairi ne sai ka tabbatar da ka sama min farin ciki na."
Ƴar fara'a nahaifin Salimat ya yi sannan ya ce"babu komai gimbiyar mata,ai abinda ki ka zo dashi ba abune wanda ya zama sabo ba,sunnah ce ki ke son yi don haka ina miki fatan alkhairi aduk inda ki ke gimbiya.
Cikin jin kunyar mahaifin na ta,ta tashi ta shige sashinta tana ji a zuciyarta kamar ta samu Admiral A. Ta samu.
Shu kuwa gogan Admiral A.ba ƙaramin kaɗuwa ya yi ba da ganin Mai martaba har cikin office ɗinsa,kuma ya nemi yardarsa wajen auren ƴarsa,kunya da kawaici sosai Admiral A. Yaji don haka cikin nutsuwa ya amsa masa zai auri Salimat ba bisa tursasawa ba,a zuciyarsa kuma yana mamakin irin mugun son da Mai martaba ya ke yiwa ƴarsa Salimat,mai makon namiji yaje neman aure amman sai aka ɓige da nemawa ƴa.
Kan Aliyu gaba ki ɗaya ya kulle ya rasa me zaiyi taka mai mai ga Hajiya ta saka shi a gaba akan Rasheeda,ga Mai martaba shima da ya sako shi a gaba akan Salimat kuma Mai martaban ya ce baya son bikin ya wuce wata ɗaya,haka zalika itama Hajiya ta ce ba ta son ya wuce wata 1.
to wa zai aura a cikinsu yabar wata?ana nufin sai dai ya haɗa su rana ɗaya ne ko kuwa?shi kansa gaba ki ɗaya ya kulle gashi yanzu wani irin tulo masa aiki a keyi a office.Ga ba ki ɗaya kansa ya yi mugun kullewa.
***
A hankali na ke rainon ƴan biyu na,kyawawa dasu kamar ka sacesu ka gudu saboda tsabar ƙyau da ƙwarjininsu,Abba na kuwa kullum cikin hantara ta ya ke yi dani da ƴan biyu na,ko laifin me su kuma sukayi oho.
Daman bai taɓa ɗaukarsu tun suna tsummansu har yanzu da suke wajen wata na uku.
Mmn junior ita ke kula da komai nawa hatta wankan jarirai ita ce ta yi min har nima kaina ita ta yi min,kaya kuwa kullum cikin aiko min dasu ta ke masu kyau.
Dangin Abba na dana Mama na babu wanda yazo don ya dubani ko yaga halin da na ke ciki.
Busy🤯
*Miss green ce*
YOU ARE READING
SILAR FYAƊE
Romancesilar fyaƊe labari ne akan wata yarinya wacce wani ya yi mata fyaƊe wanda ita kanta bata san wanda ya yi mata ciki ba,shima kuma bai san wacce ya yiwa cikin ba,kubiyoni don jin yadda labarin zai ka ya.