WATA DUNIYA P 9&10.

1 0 0
                                    

.⚔️🌍WATA DUNIYA🌍⚔️

⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️

LABARI/RUBUTAWA
KHADIJA S.SAMINU
(ƳAR GATAN MAMA)

Marubuciyar......

A WANI GIDA
RAYUWAR MU!
MAGANIN KAR AYI!
nd now...... 

⚔️WATA DUNIYA⚔️

⚔️⚔️🌍🌍🌍🌍⚔️⚔️




*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

NA SADAUKAR DA WANNAN LABARIN GABA ƊAYANSHI GAREKI MAHAIFIYATA ABAR ALFAHARINA HJY.ƘURAINABU IDRIS YARO YAHYA,ALLAH YAJA DA RAI AMEEN😍😘💞💞

⚔️🌍⚔️🌍⚔️
SHAFI NA 9&10

⚔️🌍⚔️🌍⚔️

Haka kuwa akayi sukaɗauki hanyar DEENUL-ISLAM wanda shine ainihin garinsu.

Koda suka isa masaurauta yamma takawo jiki sosai domin daf ake da sallar magriba.Mutanen garin kowa sai barka da zuwa yake musu tare da miƙo gaisuwa ga SARAUNIYA SINIYYA da MUSLIM dakuma baƙuwar dasuka gansu tare wato GIMBIYA ZULMAT duk da awajan wasu daga mutanen garin ba baƙuwar fuska bace awajansu kasancewar ba inda ZULMAT bata shiga yaƙi domin kare addininsu na iyaye da kakanni.

Mayaƙan garin kallonsu kawai sukeyi cike da mamakin meyakawo ZULMAT masarautar su.
Basu tsinke da lamarinba saida sukaga sun sakko daga dawakansu sunnufi cikin masarauta.
Nan Sarauniya tayi umarni da akawowa GIMBIYA ZULMAT kayan ƙwalam da maƙulashe,haka kuwa akayi cikin ƙanƙanin lokaci aka cika gaban GIMBIYA ZULMAT da kayanci da sha iri-iri,batare da ɓata lokaci ba tahaucin wanda zata iya sannan tabar wanda zata bari.
Jim kaɗan aka kirayi sallar magriba inda kowa yatafi domin ya gabatar da ita banda GIMBIYA ZULMAT.Bayan SARAUNIYA SINIYYA ta gabatar da sallah ne tasa ashigo mata da GIMBIYA ZULMAT domin tanason suyi magana ta fahimta da ita.

"Ina maiyiki sannu tare da fatan kinji daɗin kalar tarbar da mutane na sukayi miki"

Sarauniya ke faɗin wannan magana sanda Zulmat tazauna agefenta bayan isowarta.

"Yake wannan Sarauniya mai ɗumbin tarihi,haƙik'a nayi farin ciki mara misaltuwa da kalar tarbar dana samu awannan masarauta,kuma najinjina karramawa irintaki da mutanen da suke tare dake yake.
Yake wannan sarauniya! Inamai sanar dake cewa naga alamun mamaki sun bayyana ƙarara afuskar mutanenki sanda idanuwansu sukayi tozali dani,ina tsoron kada su sakaki kikoreni daga wannan gari,domin nasan keɗin kinabin maganar mabiyanki aduk sanda suka kawo miki shawara kinabinta.....ina tsoron kada subaki shawarar dazata saka kice bazaku zauna tare danib......."

Katseta Sarauniya tayi ta hanyar faɗin....

"Ki kwantar da hankalinki yake baƙuwata,inamai tabbatar miki babu wani wanda ya isa ya umarceni da korarki awannan garin gaba ɗaya,namiki alƙawarin zama tare damu duk rintsi duk wuya matuƙar zakibi dokokin da zamu gindaya miki kuma zaki rayu kamar yadda muke rayuwa,sannan kuma zakiyi abu guda ɗaya,inamai tabbatarmiki da zarar kinbi dokokinmu bamai rabamu harsai idan kece kika buƙaci hakan"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 06, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WATA DUNIYAWhere stories live. Discover now