12

69 3 0
                                    

WANI SO

NA ZEE YABOUR
@HWA

*SABON SALO SABUWAR TAFIYA*

*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B*

FREE PAGE 12

Jauhar kwana tayi zantukan Jameel na mata yawo a zuci, komai yace kada dangin shi su raina ta, shin wane irin kud'i ne dasu har zasu raina gadon miliyan biyu, a iya sanin ta baban shi ne mai kud'in dangin duka sauran bayan sa suke, Haka a tunanin ta ba kayan d'aki zasu yi zaman aure ba, ita fatan ta ta samu natsuwa, soyayya da kulawa, "Kada hakan ya dame ki, shi ma zai fahimta da zarar kunyi aure kin fara bashi kulawa ta musamman", Cewar wani b'angare na zuciyar ta, Da tunanin haka bacci ya d'auke ta.

**********************

"Zuciya ta ba zata iya jure ganin Jameel na son wata ba, ya zama dole na gaggauta fitar da ita rayuwar sa, mallaki na shi ni kad'ai", Meenal ta fad'a tana matse wayar ta, Tayi ta kiran sa number busy wanda take da tabbacin da Jauhar yake waya a irin lokacin, hakan yasa zuciyar ta zafi na kishi, Shigowar kiran Jameel yasa ta saki nauyayyen ajiyar zuciya, Ta d'auka,

"Hello besty" Ya fad'a, "Nayi fushi" Ta fad'a a shagwab'e, "Am sorry da Nurul qalb nake waya", Sunan da ya kira Jauhar yasa k'irjin ta dokawa, A zahiri tace "Uhmm ana ji da ita", "Sosai kam, she mean alots to me", "Allah sarki, Allah yasa mu danahin ta", "Don't tell me baki da saurayi, ko kin fad'a ma ba zan yarda ba", "Why ba zaka yarda ba", "Duk kyaun ki da gayu, am sure samari layi suke miki", Dariya tayi na farin cikin yaba ta da yayi tace "Akwai su kam sai dai sam basu mun ba", "Kice ruwan ido ne dake", "Ko d'aya, akwai kalar mijin da nake so", "Ohh! Allah ya kawo shi to", Ta amsa "Amin", a zuci tace "Allah ya kawo shi dan ga ka, ba zan bari ka sub'uce mun ba, na dad'e ina burin samu miji irin ka mai kyau da gayu", Ya katse ta da cewa "Bara na tambaye ki", "Ina ji" Ta fad'a tana k'asa da murya, "Idan zaki yi aure, kamar gadon nawa kike ganin za'a siyan miki", "7mil dan har an fara tara mun kayan d'aki", "oh wow, yar' gata", Dariya tayi, A zuciyar sa ya raya "Kaga babban yarinya, amma Jauhar tana kiran masa gadon miliyan 1 miliyan 2, ko Meenal d'in taje gidan sa, sai ta raine shi, "Are you there?" Meenal ta tambaya jin yayi shiru, "Na fara bacci ne" Ya fad'a, yana so ya k'ara kiran Jauhar yayi winning heart d'in ta, wurin ganin ba'a kawo ta da gadon k'asa da miliyan 5, ba zai iya jure kayan kunya ba( a cewar sa), Suka yi sallama da Meenal ya kashe wayar ba dan ranta ya so ba, bata k'i su kwana suna waya ba,

Missed calls ya ma Jauhar bata d'auka ba, hakan ya basa tabbacin tayi bacci, sanin ko sunyi fad'a bata k'in d'aukar wayar sa, Ya ajiyewa wayar ya kwanta bacci shi ma.

************************

Asubahin farko ya bud'e idanun sa tare da ambaton Allah, Ya kunna switch na d'akin da ke kusa da gadon sa, haske ya gauraye d'akin, wanda ya k'ara masa kyau, band'aki ya shiga ya d'auro alwala, Ya fito ya tsaya bakin madubi ya fesa turare mara hawa kai sosai, JUNAID Allah yayi sa mutum mai tsananin son k'amshi da tsafta komai nasa a killace yadda kasan mace, Ya fita zuwa masallacin dake had'e da gidan su, Yayi kusan minti talatin a masallacin, kafin aka yi sallah, a nan ya zauna yana karatun qur'ani da addu'o'i har gari ya waye( d'abi'ar sa ce haka, duk bayan sallar asuba, yana zama masallaci har rana ta fito, saboda falala na lokacin, idan bai tsaya ba, toh akwai k'wakkwaran dalilin da ya hana sa).

K'arfe bakwai da mintuna ya koma gida, sashen Abee ya shiga sanin baya baccin safe, A falon sa ya same sa yana rik'e da tasbaha yana lazimi, Cikin ladabi yace "Abee ina kwana?", "Lafiya lau Junaid", Shiru ya ratsa falon na minti biyu, Abee ya numfasa yace "Aure ita ce cikar kamalar mutum Junaid, ka duba ka ga yayyen ka baya burge ka, Yayi auren sa tare da iyalan sa, A rayuwar aure mutum ya kan samu natsuwa ga tarin lada da falala, shin ba ka sha'awar ganin jinin ka, ka bar mai maka addu'a a bayan k'asa", Junaid ajiyar numfashi mai nauyi ya sauke yace "Abee aure lokaci ne idan yazo zan yi", "Nasan da haka, amma in your case ko alamun aure babu, balle mu sa ran kana so, lokaci ne bai yi ba, mata kala kala mahaifiyar ka ta sha kawo su gidan nan, sai magana tayi nisa ka ruguza, yanzu ta kawo Aneesa ita ma ka nuna baka ra'ayi, shin menene matsalar ka?", "Babu komai Abee", Ya fad'a yana jin zafi k'asan zuciyar sa, damuwar da ke cin sa baya jin zai tab'a fad'awa kowa, "Shikenan, Allah ya kyauta yaushe kake free Malam umar zai zo ganin ka", "Da la'asar In Shaa Allah", "Ok sai yazo lokacin", Junaid ya jinjina kai a zuciyar sa yana mamakin ganin me Malam Umar ke so ya masa, ko sun kira sa ne ya masa wa'azi kan aure, idan wannan ne babu abunda bai sani ba, kasancewar sa mutum mai son addini da neman ilimi, amma babu damuwa k'arin ilimi ne, da tunanin haka yayi ma Abee sallama ya fita.

WANI SOWhere stories live. Discover now