WANI SO
NA ZEE YABOUR
@HWA*SABON SALO SABUWAR TAFIYA*
*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B*
FREE PAGE 18
Had'add'e kuma babban hall ne mai d'auke da dogon tebur zagaye da kujeru wanda aka tana dan meeting, a tattauna kan matsalolin da cigaban NNPC Company, JUNAID tun shigowar sa bai ce komai ba, zaune kawai yake, yayi nisa wurin tunanin duk maganganun da ake baya tofa baki, Da yawaa sun lura da yanayin sa, D'aya daga ciki ne ya tab'a sa da cewa "MAINA are you with us?", Dan' zabura yayi yace "Afuwan, headache", Yaa fahimci me yake nufi sannan bai cika magana mai tsawo ba, K'ok'arin maida hankalin sa yayi kan meeting d'in sai dai abun yaci tura, ya kasa fahimtar komai, ga kan sa dake k'ara tsananta masa da ciwo, Da k'yar yaga an gama meeting d'in, Bai koma office d'in sa ba, parking space ya fita, Direban sa na zaune wurin zaman direrobin company, Yayi saurin tasowa cikin ladabi ya bud'e masa murfin mota mazaunin baya,
Asibiti ya umarci direban sa ya kai shi, Cikin ladabi ya amsa da toh, yana jan kan motar, Tafiyar mintuna kad'an ta kawo sa asibitin Dr Muhriz dake nan garin Abuja, Kai tsaye office d'in sa ya nufa, akwai kyakkyawar alak'a tsakanin su, idan yazo baya jira a masu iso, bai cika zuwa asibitin ba ma sai ya tabbatar Dr Muhriz ya shigo gari, Cikin natsuwa ya murd'a handle na office d'in ya shiga,
Idon sa ne ya sauka kan Dr muhriz tare da amaryar sa Nana, tana zaune kusa dashi, hannun su mak'ale da juna, JUNAID kawar da kansa yayi gefe, a zuciyar sa ya raya "Kullum tamkar su had'iye juna, ba k'aramin so suke wa junan su ba, wanda basa iya b'oyewa a gaban kowa", Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi ya juya da zumar fita, Muryar Dr Muhriz ya tsinkayo, "Maina dawo mana", Nana tuni ta janye hannun ta, ta shige band'aki,
Junaid ya dawo ya zauna kujerar da ake attending patient, Bayan sun gaisa, Junaid yace "Am having a severe headache", "Subhanallah, wata damuwar ta sake tasowa da ciwon kan ya dawo, naga tun da na baka magunguna lokacin yayi sauk'i", Junaid ya jinjina kai alamar eh, Dr Muhriz ya sauke ajiyar zuciya, yana jawo abun auna bp gefen sa, Ya soma auna shi, "Ya salam Bp d'in ka ya hau, am sure shi ya saukar maka ciwon kai mai tsanani", Junaid yayi shiru sanin ko shakka babu hakan ne, "Amma idan babu matsala ko zaka iya sharing damuwar ka dani, am a doctor ko zan san shawarar da zan baka, da prescription da ya dace", Junaid guntun murmushi yayi yace "Am sorry, it's personal", Dr Muhriz yace "Ok no problem amma please MAINA ka rage sawa kan ka damuwa, ban san damuwar ta ka ko zaka iya k'ok'arin yak'i da zuciyar ka wurin yakice ta ba, dan tayi yawa da har tana tab'a lafiyar ka, idan ka cigaba da sa damuwa haka it may leads to something else Allah ya tsare", Junaid ya amsa da "Amin" sanin damuwar sa abu ce da ba zai tab'a iya dainawa ba har abada, yasan asibiti ba zasu masa ganin ta ba, yana neman taimakon maganin asibiti ba ne, gudun damuwar ta kwantar dashi, Drugs Dr Muhriz ya rubuta shi yace ya karb'a a pharmacy asibitin, dan suna da wahalar samu saboda tsadar su, Suka yi sallama ya tafi.
***********************
Ihun su Hayyimat take jiyo wa daga falo, suna murnar zuwan su Ummi, akwai shak'uwa da sakewa sosai tsakanin su da kakar su, duk hutu suna zuwan mata wanda wani lokaci tare da Jauhar suke zuwa, Jin suna fad'in sunan Ummi, yasa ta zura hijabin ta dan k'aramar riga ce jikinta, Ta fito falo,
"Amarya, Amarya" Cewar Fadila, Murmushi tayi tace "Sannun ku da zuwa", "Yawwa" Suka amsa har Aneesa, Kan Ummi ta juya ta dan' duk'a da cewa "Ummi ina wuni, sannu da zuwa", "Lafiya lau Amarya, ya hidima?", Kunya tasa ta kasa amsawa sai kanta da ta sunkuyar k'asa, Ummi tayi murmushi tace "Toh Allah yasa a k'ulla alkhairi", Cikin zuciyarta ta amsa da "Amin",
Gidan cike yake da mutane yan' zaria ma duka sun zo, kasancewar yau za'a fara biki, "Aneesa ki sauka d'akin Jauhar ko, kune sa'anni zaki fi sakewa" Cewar Ummi, Aneesa ta amsa da "Toh", Fadila tace "Nima ai d'akin nata zani" dama can suna shiri dan watanni ne tsakanin Jauhar da Fadila, Jauhar sosai taji dad'i dama d'akin nata ita kad'ai ce, k'awayen ta duk yan' garin ne babu masu kwana,