Bankwana da masoyi (Beloved sister)

8 1 1
                                    

ABABEN KOYI DAGA RAYUWAR MARIGAYYA ANTY HAJJA HAUWA (MAMAN MUJAHID)

WACECE HAJJA HAUWA?

HAUWA ABUBAKAR SAJE...Baiwar Allah ce mutumiyar arziki wacce ta shahara da hakuri, sada zumunta, juriya, yadda da qaddara, rashin riƙo ko da anmata ba dai-dai ba, yafiya da kau da kai daga duk wanda ya ɓata mata, macece mai sauƙin kai da wasa da dariya, macece mai neman shawara hatta a gurin ƙannenta sannan ga ƙoƙarin neman ilimi da kwatanta aiki da shi.

WASU DAGA CIKIN HALAYE DA ƊABI'UN TA.

1. Hakurin jurewa jarabawa: Wannan baiwar Allah ta fuskanci jarabawa iri-iri a rayuwarta tun kafin tayi aure kamar yadda naji daga bakinta.
Ta jure rashin mijinta a lokacinda take tsananin buƙatarsa a kusa da ita saboda yara biyu dake hannunta ga kuma tsohon ciki dake jikinta haihuwa yau ko gobe! Duk da haka ta yi tawakkali ta rungumi ƙaddarar rayuwarta kamar yadda ta rungumi hidima ga marayun 'ya'yanta tare da hakuri da juriya.

2. Mace ce da duniya ko abun cikinta bai tsone mata ido ba, ma'ana dai ƙele-ƙelen duniya bai dameta ba ballantana ta zubda kimarta ko ta tsallake iyakar ubangijinta dan ta same shi. Sannan bata kasance mai yawan bani-bani ba ballantana ta maida marayun da suke gabanta jarin nema a gurin mutane.

3. Kyauta da kyautatawa: Duk da tana cikin buƙata amma hakan bai katangeta daga kallon na ƙasa da ita dan ta taimaka masu ba. Harta koma ga Ubangiji tana yiwa mai aikin gidanmu zanin sallah duk da itama yimata ake yi; ranar da zata bar duniya sai da ta biyawa wata baiwar Allah kuɗin napep.

4. Tsafta da iya bi a sannu na duk abunda ya shiga hannunta: Wannan halaye ko ɗabi'u guda biyu mata dayawa suna son Allah ya azurtasu da shi, kuma duk macen ta siffanta da tsafta da kuma iya kula da gida da kayan abinci, kayan sawa da sauransu to bazata riƙa samun matsala da mijinta ba musamman a wannan zamanin.

5. Tarbiyar yara: Tarbiyar wani gagarumin jan aiki ne babba da yake buƙatar jajircewar iyaye, 'yan uwa da dangi, maƙabta, shuwagabanni, dama al'umar baki ɗaya.
Duk da wannan babban aiki ne amma haka baiwar Allah'n nan ta yi tarbiyyar yaranta irin tarbiyyar da ya dace da addinin musulunci bisa miƙaƙƙiya kuma ingantacciyar aƙida na ahlus-sunnah wal jama'a.

6. Neman ilimi da kwatanta aiki da shi: neman ilimi abune mai sauki musamman a wannan zamanin da muke da abeben sauƙaƙa harkar koyo da koyarwa musamman social media, sai dai kuma ba kowa ne ya damu da amfanuwa da wannan ni'imar ba, wannan baiwar Allah'n ta shiga islamiya tsawon shekara uku bayan karatu da malama ke koya mana a gida duk sati, ga kuma 'yarta fatima da take koya daga gurinta.
Wannan ma alamace na ƙan-ƙan da kai wanda ba kowa ne Allah yake azurta shi da wannan ba musamman karɓan ilimi ko gaskiya daga gurin wanda yake ƙasa da mutum a shekaru.

7. Maman mujahid macece da ta samu shaidar kirki da sanin ya kamata daga gurin mutanen da suka zauna tare da ita, ga kula da hakkin na kusa da ita, fara'a da murmushi, ga wasa da dariya, shimfiɗar fuska harda na taburma.

8. Rashin riƙe mutum a zuciya koda wannan mutumin ya mata ba dai-dai ba: Tana yawan faɗamun cewar "ni fa bana riƙe mutum a raina har ya hana ni barci, sannan ban taɓa cutarda wani ba duk wanda ya cuce ni kuma shi ya sani, shi da da Allah" Allahu akbar! Wannan kaɗai zai iya zama silar shigarta Aljanna kamar yadda ya zamo silar shigar ɗaya daga cikin sahabban Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam. Allah ya ƙara musu yarda gaba ɗaya.

9. Yin amfani da sigar jam'i wajen girmama na gaba, musamman iyaye: Yana daga cikin abunda na lura da shi daga gareta yin amfani da kalmar jam'i a duk sanda take magana da Mama ko wani babba cikin mutane, wannan alama ce ta nuna girmama na gaba da ita.

10. Jinya da jinyar majinyaci: Kamar yadda muka sani tana da Asthma ga kuma kumburi da zuciyarta yayi dalilin shiga tsananin damuwa da tashin hankali bisa wani jarabawa da tsinci kanta a ciki, amma duk da haka wannan baiwar Allah'n ta tsaya tsayin daka dan hidima da jinyar majinyaciyar ƙanwar mahaifiyarmu da take gida wacce a yanzu haka duk tunani muke yi wacece zamu samu ta yi wannan jinyar mu biya ta.

Wannan kaɗan kenan daga cikin abunda zamu iya amfanuwa daga rayuwar marigayya Maman Mujahid, Allah ya mata rahama ya ji ƙanta ya sa Aljanna makomarta da sauran al'umar musulmai baki ɗaya.

Yana daga cikin albarka da Allah ya yiwa ahalinmu siffantuwa da kyawawan ɗabi'u.
Duk wa'annan halaye dana lissafo daga gareta ta ɗan kurɓa ne daga sauran 'yan uwa da suka gabaceta.

Misali: Ta koyi hakuri daga gurin Ya Lami.

Fara'a da sakin fuska daga gurin Anty Usaina.

Mai da ɗan wani naka da ƙokarin zumunci da san naka a duk inda yake daga gurin Mama Altine.

Iya girki da bi da miji ga kuma tsafta daga gurin ya Mariya. Mama Biba tace "tun da ya Mariya tazo bamu taɓa jin ta yi faɗa da wani ba ballantana mijinta.

Dama sauran 'yan uwa da ƙarancin shekaru da bincike na bai kai ga fahimtar al'maarinsu ba.

Allah mun gode maka daka azurtamu da 'yan uwa masu albarka, ina addu'a Allah ya jikansu da rahama yasa aljanna makoma garesu da mu baki ɗaya.

Da wannan nake ƙara bamu shawarin tabbatuwa akan aikin alkairi da sada zumunci tsakaninmu da zuriyyarmu, sannan mu ɗau izina akan rayuwar duniya kamar yadda rayuwar take koyarda mu darasi.

Allah ya karawa rayuwarmu albarka ya azurttamu da tabbatuwa kan ingantaccen aƙida da dorewa kan ayyukan kwarai kuma ya azuratamu da samun yardarSa. Amin ya hayyu ya qayyum.

Assalamu alaikum.

Fatima Saje ✍🏾

Taƙaitattun labarai (short stories) Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ