3&4

668 38 2
                                    

*'YAR ZAMAN ƊAKI*

     ©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Ban amince a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, don haka a kiyaye.⚠️

https://chat.whatsapp.com/HFVRd4aXG6A8v3OngGn29A

                 3&4

     Khalid zuru ya yi yana kallon Walida da take sakace tana lumshe ido, sai da ta gama sakace ta ɗago daga kishinɗe ta ce, "Uncle ƙishirwa nake ji." Ba tare da ya kalli wurin da yake tsammanin anan ruwa da yegot ɗin suke ba, ya miƙa hannu har lokacin idonsa na kan Walida, yana taɓa robar yegot ɗaya ya ji ba faɗi garam alamar an shanye abin da yake ciki. Wannan karon sai da cikinsa ya kaɗa amma don kar ya nuna mata ya ɗan tsorata ya hau borin kunya da cewar, "Wai me yake faruwa ne? Kaji tun ba a je ko'ina ba sun ƙare shi ma yegot ɗin an shanye shi duka, wallahi duk uban da yake aikata min haka daidai nake da zamaninsa."

   Amarya Zarah tana can zaune tana jiran dawowar Khalid ango, ƙamshin kazar ne ya gama cika mata hanci ban da haɗiyar yawu babu abin da take yi. Jin shirun Khalid ya yi yawa ya sa ta fara jin haushi saboda tana tuna Walida wani takaici yake mamaye birnin zuciyarta, a hankali ta miƙe ta isa bakin ledar kazar. Ta faki ido tana kallon hanyar shigo wa amma jin shirun da ta ji ya sa ta kai hannu da niyyar buɗe ledar, lokaci ɗaya ta ji kamar an ce. "Wayyo ni Amarya Kaza." A ɗan zabure Zarah ta ja da baya tana waige-waige don yadda ta ji kazar na magana raɗau a kunnenta, da sauri ta nufi sashen da ta ga Khalid ya bi.

  Tana zuwa ta samu Khalid tsugunne a gaban Walida yana cewa, "Walida ki yi bacci kin ga Auntynki na can tana jirana." Walida ta kwaɓe baki ta ce, "A'a ni dai ka kwana a nan." Ganin yanda Khalid yake lallaɓa Walida ya tunzura zuciyar Zarah, tun daga bakin ƙofa ta saki uban ashar tana faɗin:

  "Khalid me kake yi haka? Wai ni ce Amaryar ko yarinyar nan? Tun da ka shigo gidan nan ka taho wurin yarinyar nan ni ina can ina zaman jiranka, wallahi da na san wulaƙancin nan za a min da..." Tun bata ƙarasa ba Walida ta tashi zaune ta ce, "Don Allah ki yi haƙuri Aunty." A zafafe Zarah ta dakatar da ita da cewar, "Rufe min baki munafuka ƙanƙanuwarki da ke sai iyayi." Khalid ya miƙe jiki a sanyaye ya ce, "Don Allah ki yi haƙuri Zarah, ni fa ba wani abu ne ya tsayar da ni ba. Dubi ledar nan." Khalid ya yi maganar yana ɗago wa Zarah ledar kazar. Ganin taunannun ƙashi ya ƙara harzuƙata ta ce, "Eh to tun da kun cinye gani ƴar iska ai dole ka nuna min ƙashi amma gaskiya Khalid ka cuce ni da na san cin kashin da za ka min kenan da..." Khalid ya katse Zarah tare da zayyane mata abin da ya faru. Da farko ta so ƙaryatawa amma da ta tuna abin da ta ji sai tsoro ya sake kamata. Suna nan tsaye Walida ta ɗago ta ce, "Uncle ku je ni fa bacci nake ji."

  Khalid ba ƙaramin daɗi ya ji ba, cikin shauƙi, so da ƙauna ta riƙo hannun Zarah suka wuce sashensu. Suna zuwa Khalid ya rungumo Zarah yana kashe mata ido ɗaya ya ce, "Habibity kin ga yadda kika yi kyau kuwa?" Kafin Zarah ta yi magana suka ji magana kamar raɗa an ce, "Duk kyawunta ta kai kaza." A firgice duk suka waiga, Khalid ya fara leƙe ta window ya ce, "Zarah amma dai babu wanda aka bari a ƴan kawo amarya ko?" A daƙile Zarah ta ce, "Sai ƴar zaman ɗaki waya sani ko laɓe take mana." Khalid ya wayance da cewar, "Haba dai Walida ba za ta yi haka ba. Yanzu dai miƙo min ledar kazar nan ki ga."

   Zarah ta yi baya cikin zaro ido tana faɗin, "Wa ni? Ai idan ka ganni a lahira kaini aka yi. Jin kunnena na ji kazar nan ta yi magana, kai anya Khalid gidan nan ka sa an yi masa sauka kuwa?"  Khalid ya ƙarasa ya ɗauko ledar kazar yana cewa, "Ban da almara ya za a yi Kaza ta yi magana kina son dai tsorata kanki ne." Yana gama maganar ya baje musu kazar suka zauna sai dai har lokacin Zarah bata gama sakin jikinta ba."

  Katuwar cinyar kaza Khalid ya ɗauko ya gutsira sannan ya miƙa wa Zarah ya ce, "Buɗe baki My love." Zarah ta buɗe baki yana miƙa mata a baki sai ji ta yi zuwait an zuge tsokar sai ƙashi. Zarah da take baki a buɗe ta kalli Khalid, shi kuma sam bai lura da abin da ya faru ba. Wata tsokar naman ya sake ɗauko mata ya miƙa mata, a wannan karon Zarah ta cinye amma tana yin tauna ɗaya taji an ce. "Wayyooo cinyata ni kaza." Da sauri ta kalli Khalid ta ce, "Hubby ka ji me na ji kuwa." Khalid ya tura tsoka baki yana tauna ya ce, "Zarah don Allah ki kwantar da hankalinki, na fa gidanki ne karki tsorata kanki." Babu yadda ta iya haka ta ja bakinta ta yi shiru don ta ga Khalid bai yarda da abin da ta faɗa ba, yana sake bata kazar ta nuna masa ta ƙoshi. Sai lemo ta sha kaɗan amma har lokacin zuciyarta wasu-wasi take.

   Bayan sun kammala Khalid ya tuna da wani magani da abokansa suka bashi, da sauri ya tashi cikin dabara ya nufi kitchen acen ya buɗe jarkar ya shanye gabaɗaya. Ita ma Zarah yana fita ta zuge jakarta ta ɗauko wani tsumi da aka bata ta shanye, tana jin motsinsa ta wurga jarkar ƙarƙashin gado. Khalid na zuwa ya cire kaya ya ɗaura towel yana faɗin, "Dear bari na watsa ruwa sai mu ɗaura alwala mu yi sallah." A kunyace Zarah ta amsa tana sunne kai ƙasa ita a dole kunya take ji, tana nan zaune Khalid ya faɗa banɗaki.

  Shigar Khalid ba wuya ta fara jin kyarkyara a kofar ɗaki kamar kaza za ta saki ƙwai, a hankali ta tashi ta leƙa ta window ga mamakinta sai gani ta yi gasasshiyar kaza na rawa babu kai a jikinta. Ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta na lugude ta ji an furta, "Mu kashe mu binne mu sha amarci da angona."

  Khalid da ke toilet ɗin cikin ɗaki bayan ya sakale towel yana shirin kwara ruwa a jikinsa kamar almara ya ji an ce. "Sannu mijin kaza." Da sauri ya waiga yana dube-dube nan take ya ji ƙamshin gasasshiyar kaza ta game hancinsa, yana shirin janyo towel don ya fita ya ji an shafo bayansa. Da gudu ya fisgi towel ya hau kiciniyar ɗaurawa, hannunsa har rawa yake zai buɗe ƙofa ya ji an sake cewa, "Mijin Kaza yau fa ranar farinciki ce." Wani tunani ne ya faɗo wa Khalid ya ga idan ya yi ƙarfin halin magana koma waye zai tsorata shi za su dawo daidai. Tsayawa ya yi a wurin ya ce, "A gidan uwar wa na zama mijin kaza ga matata can Zarah a ɗaki." Yana rufe baki ya ji an ce, "Gashi har magani ka sha min don mu sha soyayya, ka ga daga yau zuwa ƴan kwanaki zan fara sakar maka ƙwai zo ka ji angona." Kafin ya yi wani yunƙuri ya ji an fusgi towel ɗin ya ji alamar yatsun kaza na tsikarinsa a jiki.

NA BARKU HAKA DA MIJIN KAZA😂 SU SHA AMARCI LAFIYA.

Ummou Aslam Bint Adam.🌚

'YAR ZAMAN ƊAKI CMPLTWhere stories live. Discover now