Family Fueds

13 1 0
                                    

Bismillahir rahmanir rahim

          Karfe 4:00 daidai a kofar gidan su ma'u tayiwa Abdool, sallama yaitayi ba tare da yaji an amsa ba, har yana shirin juyawa kuma saiga ma'u ta fito sanye da hijabinta har kasa

"waalaikumussalam... Sorry yaa Abdool kana ta sallammaa tun dazu ina wanka ne. Ina yini " 

"ah ba komi da inama shirin juyawa kenan kuma sai gaki.... Mun yini lafiya? Ya mama? Yana ciki kuwa? "   

"lafiya... Ummah ta tafi kasuwa amma yanzu tana dawowa dan tundazu tafita.... "

"To shi kenan dama  wajenta nazo amma kuma tunda....."  yana cikin magana kuwa saiga mai adaidaita ya paka a kofar gidan

"ga ummahn nan ma ai" cewar ma'u tana karasawa dan taya ummah kwaso kayayyakin daga cikin adaidaitan

" sannu da dawowa ummahta"  cewar ma'u dake tattaro kayayyakin da ummah ta siyo, ita ummah sam bata ma lura da mutum a kofar gidan ba saida tazo shiga sannan ta kalleshi. Taso gane fuskan kam saidai ta rasa inda tasanshi, shiko tana karasowa kofar gidan ya rusuna

"Barka da dawowa mama, bari na tayaki" ya fada yana mika hannunshi da nufin karban kayan hannun nata, saidai sam taqi

"yauwa.... Ayi haka kuwa, ban tarbi bako na ba kuma saina hadashi da aiki? Karaso daga ciki  bismillah" cewar umma cikin fara'a da  sakin fuska. Ajiye kayan hannunta tayi a daki sannan ta fito da tabarma ta shimfida mai akan verandah sannan ta zauna akan wata yar kujerar tsakar gida

" Bismillahi... Zauna mana " bayan ya zauna ne suka fara gaisawa a mutumce (abdool kamar na kwarai lol)

" ina yini mama.... Munsameku lafiya?

" lafiya alhamdulillahi.... Ya mutanen gidan ya aiki kuma"

"suna lafiya mama"

"toh mashaallah.. " saikuma shiru ya biyo baya, ummah ce tai dan gyaran murya sannan taffara magana

"  sadai ban ganeka ba"

"eh, gaskiya ba lallai ki iya gane niba... Nine abokin wannan likitan da yayiwa ma'u allura kwanaki "

" eh... Tabbas anyi haka... Ina fatan lafiya dai koh" ummah tafaddaa cike da taraddadi tunda dai tasan an dade da gama alluran kam, hartama fara tunanin kila kudin jinyarsu suka biyo amma kuma ai... Saiya katseta da ga tunanin zucin data tafi

"kamar yadda na fadamiki mama..... sunana Abdulsalam Umar kuma nine abokin likitan da yayiwa y'arki allurah kwanaki sakamakon tsautsayin daya gifta..... toh dama magana nakeso muyi dake mama.... saidai abokin tafiyan nawa bai samu zuwa ba sabida wani uzuri mai mahimmanci ina fatan zaki fahimceni"

"inajinka dan nan... Allah yasa muji alkhairi"

"  agaskiya  mama abokina yaga yar wajenki yaji yana sonta so irin na aure... Yaso zuwa tun alokacin nina hanashi sabida bamusan yadda zaki dauki magaanar ba" ajiyar zuciya ummah ta sauke sannan ta dubeshi

" ikon Allah... " shine kadai abunda ta iya furtawa abubuwa da dama suna kai kawo aranta dan ita takasa gaskata zancen ma ina su ina wayannan mutanen masu arziki haka.   Abdool ne ya kayseta daga zancen zucin da take

" shiyasa ma nace kada yafara yiwa ita ma'un magana tukunna ya bari sai munzo munji ta bakinki, kin amince mana... Amma dan Allah mama inaso ki fahimcemu sannan ki dan samu kiyi tunani akai, inshaallahu zamu sake dawowa bada dadewa ba"

"to shikenan... Bakomi zanyi shawara tukunna da iyayenta da ita kanta tunda kaga ni uwace bazaiyu na yanke hukunci ni kadai ba batare dana shawarci yan uwan mahaifinta ba"

"haka ne mama... Bakomi Allah ya sa muji alkhairi. Nizan koma mama, sai mun juyo"

"toh allah yabamu alkhairinsa... Gashi ko ruwa ma baka sha ba" tafada tana mikewa

UADWANWhere stories live. Discover now