17_18

4 1 0
                                    

JARABTAR MU
Wattpad_Qurratou
Page-17-18

_Bisssimillahir Rahmanir_ _Rahim_

--------------Walkiyar da akayi ne yasa nace daman akwai hadari a garin? Haba shiyasa yau akayi zafi,mu kuma muka samu chini ki,ashe hadari ne.
Kafin na ida tunanin saidai naji sab kowar ruwa!!
Alhamdullah!! Yau na tsira da zuwan Lado,duk nacin shi ai bazai fito cikin ruwa ba,iska na kadawa lokaci guda naji zuciyata tamkar an wanketa, Wani sabon littafi ne da Baba ya siyoman na dauka,nafara karan tawa sosai littafin ya dauki hankali na tun farkon fejin littafin,mai littafin ya fadi tayaya zaki zabi mijin aure,ya kawo hadisai da kisso shi.
Littafi yayi dadi sosai komai yabi shi daki-daki, juya bayan littafin nayi,dan ganin sunan littafin,FANNUL TA'AMULI BAINAR ZAUJEN,murmushi nayi nace"lalle Baba na sona duk abinda yasan zan karu shiya keyi man,ko ya azani hanya,ina mai bukatar a barni na zabi miji,mai irin suffofin da mai littafin nan ya saka,ba irin Lado,da ace kowa ce mace zata karanta tashi lalle kam da ta karu da yawa.
Ya kamata iyaye su sani koda addini ya basu damar zaba ma 'ya 'yan su miji,to hakan ba yana nufin kowa ne namiji ba,ai addini ya bada kalar mijin da ya dace,yanzu idan aka aura man Lado,Inna bata tunanin mako mata da yaran da zan haifa, anya nayima yaran da zan haifa adalci idan aka zaba masu Lado a matsayin Uba??
shiru nayi ina tunani lokaci guda hawaye suka wanke man fuskata.

************
Wanka Kursim ta fito,cikin sauri ta shirya,ta kira ma aikatan part dinta,tabasu gyaran zogalan suyi mashi hadi kamin ta dawo.
Ta wuce part din Umman ta cikin fargaba mizata ce mata game da raunin fuskarta.
Tana isa masu kula da part din Umman ta suka ce tayi wajen Abban ta,hamdala tayi dan batason Umma tasan akwai matsala,dan tasan halin Umman ta yadda take sonta ace wani ya fitar mata jini,kila idan Umma taji,tasan bazata barta ta auri Annuwar ba.
Waya tayi aka kawo mata zogalan,ta kalli zogalan yayi kyau kamar wani abincin kasar waje.

Tace"Nasan zaka soshi,tunda ita komi nata mai dadi ne,lalle wadan nan mutanen Aljanu ne"kai tsaye tayi sashen shi.

Kaf..!!sukayi karo,saura kadan zogalan ya zube,tayi saurin rikewa,tare da ja daga baya!!
Kallon shi take cikin mamaki!!
Tace"Ina zakaje bayan ruwa akeyi tun dazun??kuma ai daka kirani nazo na kaika"juyawa yayi ciki tabi bayan shi.
Zauna tayi kusa da kujerar da yake zauna,ta aje mashi zogalan,tace"gashi nan na kawo maka"kallo yabi zogalan dashi,kamar baita ba ganin zogala ba.
Spoon ya dauka yafara chii,yana ya mutsa fuska yana tamnewa sai yayi murmushi yana kallon zogalan.
Mutuwar zaune Kursim tayi,lalle sun gamu da Aljanu.
Miyasa yake son komi nata??hadda zogalan ma,hadda sakar ma zogalan murmushi,lalle zata saka a bin cika mata mutane ne ko Aljanu.
Inama Hanan zata gane,maganar da take fada mata da gaske ne,akwai matsala fa akan mai furar nan, ko ka min ta gama tunanin da take,har ya chinye babu komi.
Cikin sauri ta zuba ruwa ta aje mashi,baiko kalli ruwan ba.
Dauka tayi ta mika mashi ya amsa,tareda sakar mashi murmushi.
Juyar da fuskar shi yayi wani waje.
Yana gamawa ya mike tsaye,ya juya zaiyi hanyar bedroom dinshi.

Cikin sauri tasha gaban shi,ta langwabar da kai,tare da aza kanta bisa kirjin shi,tana shafawa tace"please Prince mu koma mu zauna fira fa nazo muyi,kuma inaga har yanzu ba'a dauke ruwan ba"tana maganar kamar zatayi kuka.
Tana gamawa yasa hannu ya fizge ta daga jikin shi,ya saketa ta fadi TUSS...!!
Yayi gaba kamar ba mutum yayi ma haka ba.
"Wash"Kursim tace,tayi saurin tashi daga m da tayi tabi bayan shi lokacin har ya shige cikin daki, a bakin Wardrobe ta iske shi,zai cire kayan jikin shi yana cire rigar suka hada ido.
Kallon shi take tamkar yau ta fara ganin shi.
MmCikin sauri ya maida rigar ya tako inda take tsaye.Ganin yadda ya chanza yasa hankalin ta tashi.

Kuma yanzu mitayi mashi??

Kallon ta yayi tun daga sama har kasa kana yace"ke wace irin mutum ce??na tsani ta kura,bani son a cika matse man,sannan dan yana gidan ku zaki shigoman daki bata reda naiman izini ba,haka aka koya maki"kallon shi take idon ta cike da hawaye.
"Bana son ganinki kada ki kara shigo man daki inba da izini na ba,idan nan gidan kune,banda iko dashi saina kama daki a Hotel"kuka Kursim take sosai wannan wane irin kaskan cine??
"Fita"yace cikin tsawa!!
Cikin sauri tabar dakin tana kuka da gudu.

Zama yayi bakin bed dinshi ya rike kai,mizaima yarinyar nan tabar zuwa inda yake jin shi yake tamkar wanda yayi shekara.
Wayar shi ya dauko ya danna kiran Abie.
Yau kamar zaiyi kuka,babu ko gaisuwa yace"Abie wallahi zan maka biyayya akan duk abinda kace,amman kabar ni nadawo gida na gaji"shiru Abie yayi.
Sai chan yace"wani abu akayi maka?"cikin sauri yace"a'a kawai dai ban saba da garin bane"Abie yace"to ai bakayi abinda aka turoka ba dan har yanzu banga alamun so ko shakuwa ba".
"wallahi Abie zanyi duk abinda kakeso na tuba"cikin sauri Abie yace"harda auren Kursim kenan"shiru yayi ya kasa magana.
Abie yace"nabaka nan da kwana biyu kayi tunani"daga haka ya kashe wayar.
Shiru yayi ya rasa abinda ke mashi dadi bayan yayi shirin kwanciya bacci yaki zuwa.
Tashi yayi ya tsaya bakin window yana kallon taurarin dake a sama ya rasa minene mafita yanzu.
Kode ya amince idan antashi auren ya gudu yaje wata kasa ne?.
Haka za'ayi,Sai kuma ya tuna wani abu sai yayi tsoki.

A ban garen Kursim tana komawa korar masu aikinta tayi ta fada tsakiyar gado tana kuka lallai kam duk wahalar da take bazai taba sonta ba, Bai taba yaba mata ba kullun a kwayar idon shi idan ta kalla babu sonta a ciki ko kadan hakatayi ta kuka har dare yayi nisa.
Kode ta yafe Prince dan babu alamun sonta gashi bai dauke ta da daraja ba,bata da muhimman ci kenan a rayuwar shi?
Kila idan na aure shi ya chanza,to taya zan aure shi??
Haka tai ta ihu ita kade tana bazan iya ba har barawo bacci yayi gaba da ita.

A ban garen Annuwar ya kasa samun mafita har dare yayi nisa

************

Koda na tashi da safe yauma kamar kullun nasan aiki na,haka nayi nagama,na fara aikin fura.
Na daka sai ga Ma'u ta fito daga dakin Inna tana mika tare da hamma,ta kalle tace"Nanan duwa"nayi shiru tasan na tsani sunan tace;"kibar wannan abun kizo ki sayawo man waina tashar Ado.
Nace"amman ai'kin ga aiki nike,sauri nike da fita tallah da wuri,gashi zanje diban zogala"shiru tayi tana kallo na,yaushe har nayi bakin da zan fadi mata magana.
Juya wa tayi cikin sauri ta koma dakj,sai gata ta fito tare da Inna.
Wata katuwar muciyar tuwo Inna ta dauko tayo kaina tana fadin.
"Daman jiya da bakin cikin ki na kwana na rashin zuwan Lado,kuma yanzu dan na kyale ki shine zaki bata ma yar tawa rai,yarinya mai Uwa da Uba,dakuma gata gaba da baya,shine saboda bakin ciki kike so ta zauna a cikin hawala,yunwa ta kamata da gatan ta"ganin da gaske tayo kaina tana kara fadin"ai gwara na sabattaki da ki sabatta min ita da yunwa,ko kin mutu Uban ki kade keda takaici,itafa?"
Nayi hanyar waje ina cewa"Dan Allah Inna kiyi hakuri"ganin idon ta ya rufe yasa nayi saurin fita.
Tace"idan kika fita,kika dawo kinsan sauran kizo ki idaman fura ta,yar bakin ciki da Lado yazo jiya,niyyah ta yau ko tallah bakiyi,dan yadda Lado ke kashe ma Mace kudi idan yana neman aure shine ni kike mani bakin ciki,to wallahi gwara na sabatta ki,dawa ne bakin ciki zanji kenan?kibata man kibata ma diyata baki isa ba zaki dawo ki iskeni".
Nide ina labe jikin katan ga inajin ta.

***************

"Morning Princess I'm back wooo"ta ida maganar cikin waka.
Yadda taga Kursim yasa tayi saurin karasawa bisa godan!
Bubbuga bayan ta take tana cewa"Kursim Hanan ce bude idon ki,miya same ki"a hankali Kursim ta bude ido tana kallon Hanan.
Da fuskar ta wadda hawaye suka bushe.
Jikin Hanan Kursim ta kwantar da kanta tace"Hanan ina tsanar kaina saboda son da nike mashi,bazai taba sona ba,kiyiman addu'a,Hanan yace kada na kara rabar shi,baison ganina,dami zanji da son shi,koda kiyayyar da yake man?"ta ida maganar cikin kuka.
Hanan tace"miya farune?"nan Kursim ta fada mata komi.
Cikin sauri Hanan ta zame jikinta ta mike tsaye!!
Idon ta sun rufe ranta a bace"Kursim tace minene haka ina zaki?"kai tsaye tace"Umma zan fada mawa,chin kashin yayi yawa koda ke ba Princess bace,wulakan ci yayi yawa,baison darajar dan Adam ba,Umma zan fada mawa nasan zata taka mashi burki,yasan dawa yake tare"cikin sauri Kursim ta rikota tace"ki rufaman asiri kada kowa yaji,wannan sirri nane,nafa da maki,idan har kina sona da gaske,kawai kitaya ni da addu'a,idan kuma kika fada ma Umma baki man adalci ba,kinfi kowa sanin Umma".
Dawowa tayi ta zauna tare da yin tagumi ranta a bace.
Kallon Kursim tayi tace"wallahi na rantse maki sai Prince ya duka da kafar shi yana rokan ki,akan ki aure shi,kiba shi jikin da yake wulakan tawa,sai ya nemi hada jiki dake,na rantse naki"shiru kursim tayi.
Tana tunanin taya za'ayi hakan ya faru,lalle kam har yanzu Hanan bata san waye Prince ba, taya za'ayi ya duka mata har yana rokan ta wannan maganar bazata yiyu ba.
To amman mi Hanan zatayi ne??


*************

Tashi nayi ina lekan Inna dake tsaye da muciya taki koma daki nasan idan Inna ta buga man muciyar nan kila ai ban iya tashi yanzu ya zanyi kenan,gashi Inna batajin lallashi idan ranta ya baci zuciyar ta makan cewa takeyi.
Ju yawa nayi,karaf idona suka hadu dana Lado!!
Yana bisa jakin shi,rike da sanda wadda yake bugun jakin da ita.
Washe man jajayen hakuran sa yayi,yana niyyar sabko wa.
Haba ai bansan lokacin da nayi cikin gida a guje ba dan nafi son azabar Inna akan kallon Lado.
Kaf...!!mukayi karo da Inna!!
Zaroo ido nayi waje tamkar zasu fito...!!

MAIRO ANKUDIE {QURRAH}

JARABTAR MUWhere stories live. Discover now