_*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_
📃Littafi na 1
By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*
*GAWURTATTU 5*
-----------------------
*wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
---------------*Arewa book user*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
--------------------*Sirrinmu* manzon Allah (s.A.W) ya hanemu da gujewa mazajenmu a shimfiɗa yin hakan babban laifi ne kuma tsinuwar mala'iku za ta tabbata akanki. --------------------------------
3🟪4.. .Dukansu suka haɗa baki wajen ce wa "umma lafiya me ya faru?".kukan ta ƙara fasawa tana ce wa"yanzu har lokacin wulaƙanta ni agidannan ya yi?gaskiya zan bar muku gidannan ku zauna ku da matanku tunda haka kuka zaɓa".
dukansu shiru suka yi sai malik ne ya ce"Umma ki faɗa mana abinda ya faru,don mun shiga cikin duhu wallahi".
"To matarka ce inya mura ita ce ta ɓata min rai,wai ga masifaffiya nan ta iso,don ubanta gidan inyamurai ne nan da za ta tara mana ƴan bariki suna muskuta ɗuwaiwaka kamar gidan maguxawa?to wallahi ni nagaji xan barmuku gidanku".sai ta fashe da kuka sosai har da majina,Hajiya Iklima ta ce"kaka don Allah ki yi haƙuri ki daina kuka"sai kuwa kaka ta Juyo a fusace ta ce"indai na kuka ko?tunda ba uwarki ce taka kukan ba ai dole ki ce haka?ni tashi ma shi ki barni in yi magana da ƴaƴana bana son bare awajen.
wani malulun baƙin ciki ne ya cika zuciyar Hajiya iklima ta Kalli fuskar hajiya kaka ta harareta,ita ta rasa wacce irin mata ce ba ta ɗaukar zuga ko kaɗan,amman ta yi alƙawarin muddin tana raye sai ta haɗa Hajiya kaka da dukkanin surukanta ta zama ita ce ta gaban goshi.
Tashi ta yi ta fita tana mai ƙara jin haushin cin fuskar da Hajiya kaka ta yi mata,sai kuwa kaka ta ce"to as dai a fita don bana son ina shawara da ƴaƴa na a zo asakamin idanu irin na fulanin daji".
wannan magana da kaka ta faɗa ba ƙaramin mugun haushi ya bawa Hajiya iklima ba,don tasan sarai da ita take don asalinta fulanin daji ce,don itama kafin ta bari a aurota ba ƙaramin gwagwarmaya aka sha ba.
"Umma insha Allsh daga yau Zulaihat ba xa ta ƙara yi miki wani abu da zai ɓata miki rai ba,yanzu ma ba sai anjima ba za ta baki haƙuri",yana faɗar hakan ya yi saurin fita.
Usman autan Hajiya kaka ya ce"gaskiya umma ki daina yi wa wannan baiwar Allahm haka,gaskiya ba a ƙyauta mata wallahi saboda ita ba yaranmu ba ce sai kuma ace za abi a tsaneta".
"ah lallai ƙanin Zulai ka ce kaima an jiƙa an baka,kamar yadda sukayi wa ɗan uwanka a da cen baya,yanzu kuwa Allah ya dawo min da hankalin ɗana jikinsa,yanzu muna nan da kai za kaga caccakar da zai yi musu shegu masu cin arziƙi,tunda suka zo ina kula dasu babu abinda suke sai dafa nama daga an sauke wancen a ɗora wannan,ɗana yana ta kawowa suna cinyewa".
dukkansu shiru sukayi har Alhaji Aliyu wato babban ɗan ta don shima ba'a bar matarsa ba,don haka haƙuri kawai ya iya bawa Hajiya kaka yaja bakinsa ya yi shiru.
A ɗakinsa ta samesa yana kaiwa yana kawowa hannayensa ya rungumesu a baya,sallama ta yi ta samu waje ta zauna kanta a ƙasa sai ta ji ya ce cikin zafi"Yanzu Xulaihat abinda ki ka yi wa mahaifiyata ya yi miki daɗi kenan? ki tara ƴan uwanki suna zagar min mahaifiya ta to wallahi ba zan lamunta ba,kowa ya haɗa kayansa ya barmin gidana don ba zan lamunci cin fuskar kowaccenku akan mahaifiyata ba.
Muryarta na rawa zata yi magana da sauri ya ɗaga mata hannu ran tsohon soja ya tashi ya fita yabar mata ɗakin,ya koma wajen mahaifiyarsa ya cigaba da lallaɓa ta,don yana fatan ya gama da ita lafiya.
Kuka sosai ta yi awajen kafin ta tashi ta fita,tana tunanin ta yadda za ta gayawa ƴan uwanta wannan maganar garinsu da sai a yini a kusan ƙwana ana tafiya sannan sai da yamma ta yi sannan za a ce su koma da yamman nan ko kai amarya ba ayi ba sunga gida.

STAI LEGGENDO
ABIN CIKIN ƘWAI
Narrativa generaleLabarine akan wata zazzafar Ƙiyayya,ban dariya,ban tausayi da sauransu.