_*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_
📃Littafi na 1
By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏**GAWURTATTU 5*
-----------------------
*Wattpad user name*
https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333
-------------------------*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
----------------------
*Sirrinmu*manzon Allah(S.A.W)ya hanemu da yiwa ƴaƴanmu zane kamar,kalangu,tattu da sauransu.domin canza halittar ubangiji.
5🟦6
. . .ture hannuwa na ta yi sannan ta ce"amman gaskiya khairat baki da hankali wallahi saboda me shi bai sonki ke zaki ringa tusa kanki,Allah ya yi miki halitta mai ƙyau duk da ke ba fara bace kamar sauran ƴan gidannan amman kaf ɗinsu kin fisu komai ilimi,haƙuri,ƙanƙan da kai,biyayya,tarbiyya,wallahi duk kin fisu wannan abubuwan dana lissafa,to me zaisa ki zaɓi wanda baya sonku?idan fa ki ka auresa ba zai taɓa baki haƙƙinki ba,kuma harga Allah bashi da laifi tunda ba shine ya ce yana sonki ba,dole aka yi masa kinsan dai Hajiya kaka tana ji yanzu ko yana so ko baya sonki saiya aureki don yadda take matuƙar sonki aduk cikin jikokinta,don Allah Khairat ki cire Bilal a zuciyarki don ba alkhairi ba ne kinji?na fi son ki auri wanda zai kula da ke sosai ba wanda zai zakunce ki ba".
kuka sosai na ke yi sannan na ɗago idanuwana da suka jiƙe jagab da hawaye na ce"ummu arman don Allah ki bani goyon auren Yaya na Bilal wallahi duk yadda ki ke tunanin irin son da na ke masa to duk ya wuce hakan,ina jinsa ne har cikin ƙoƙon xuciyata duk sanda zanyi numfashi to tabbas sai na tuna da Yaya Bilal,don Allah ki bani goyon baya duk gidannan babu wanda zan tunkara da wannan maganar idan ba ke ba,don Allah ki fuskanci yadda na ke ji don Allah".tana faɗar hakan ta ruƙo hannun Ummu Arman ta ɗora sai tin zuciyarta ta ce"Ummu Arman aduk sanda ki ka ji zuciyata tana irin wannan bugawar to tabbas Yaya Bilal na ke tunawa,na so in cire wannan mayen son da na ke masa amman abu ya ci tura,saboda da sonsa aka haifeni kuma har na girma dashi cire wannan son a zuciyata tamkar cire numfashi na ne".sai na rungume Ummu Arman na fashe da kuka mai tsananij gaske.
rungume ni ta yi tana dukan baya na a hankali itama hawayen yana fitowa sosai acikin idanuwanta,tabbas tana matuƙar son Khairat don tun tana ƙaramarta ta ke sonta kuma tun tana ƙaramar Allah ya jarabce ta da son Yayan na ta,tana tausayawa yarinyar sosai yadda ya kamata saboda Khairat yarinya ce mai haƙuri,tabbas da za ta iya da tuni ta sakawa Bilal son Khairat don da ya ke mutuminta ne bayan wajen Kaka akaf gidannan babu ɓangaren da ya ke shiga ya yi hira idan ba sashenta ba,tasha yi masa nasiha akan yaso mai sonshi kanar khairat amman abu shiru kamar ma turasa ta ke yi wani lokacin,idan ta yi masa maganar Khairat ba zai sa ke shigowa sashenta ba,har sai ta je ɓangarensa ta basa haƙuri sannan komai zaiyi dai dai.
Jikina babu ƙwari na koma ɓangarenmu don ƙwana biyu bana zuwa sashen Hajiya Kaka tunda munyi faɗa,ina shiga Hajiya Iklima da Anty Zeenat suka kalleni sheƙeƙe sannan Hajiya Iklima ta ce"ke zo nan tunda baki iya ganin mutane ki gaishesu ba".ina zuwa ta ɗaukeni tas da maruka har biyu sannan ta ce"na yi maganin mara kunya wuce ki bani waje da wata uwar baƙar fuskarki wacce uwarki inyamura tuban muzuru ta shafa miki".
Sosai abin ya yi min zafi zuciyata tana ƙuna bansan sanda wani kuka mai ƙarfin gaske ya zomin ba,daman abokin kuka na ke nema don daman a cikin matsala na ke yanzu gashi kuma an to noni.
Mama da ke ɗakin Abba tana gyara masa shimfiɗa ta jiyo ihuna ta fito da saurin gaske har tana tumtuɓe ta ce"ke Khairat lafiya me ya faru?".
ban iya ba ta amsa ba da sauri na rungumeta ina shesshaƙa kamar zan haɗiye zuciya,ta gane me ya faru don haka bata ce komai ba taja hannuwa na muka koma ɗakinta.
"Da mana ayi magana in zageki tsaf kema don daman akanki na ke son hucewa,da anyi magana sai miji ya ce Zulaiha! zulaiha!wai ita ga ta matar so,ko uban waye ba matar so ba oho".

ESTÁS LEYENDO
ABIN CIKIN ƘWAI
Ficción GeneralLabarine akan wata zazzafar Ƙiyayya,ban dariya,ban tausayi da sauransu.