8

23 2 0
                                    

_*ABIN CIKIN RUHINA*_

*{RE-POST}* ©2019

Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira7531

          🅿️.......8

Rayuwa mai cike da k'alubale, wannan haka yake dukan nin wanda kake gani, to fah kowa da irin yadda rayuwar take zuwa mashi,don babu Wanda zaice tana yimashi 100%,babu shi wallahi dole akwai ta Inda Allah zai jarabceka.

Haka yake ga Khairat Allah ya jarabeta da matsanancin son yayanta, Wanda ita kanta bata san lokacin da hakan ta faru da ita ba,gashi bata da masaniyar wace irin ak'akace tsakaninsu, shin ita dashi Waye bare kuma Waye d'angida,idan ta fahimci Maah yadda tayi mata magana ya nuna akwai aure tsakaninsu, Amman to Miye dalilin yi mata shamaki da shi.

bata da mai bata wannan ansar, zata bita yadda tace tayi alkawarin bazata sab'ama umurnin taba, zata yi iyakar iyawarta don ganin duk wasu feelings da takeji nashi ta yi yak'i dasu.

Tsakanin ta da salma yanzu zakayi mamaki, sun koma y'an biyunsu sak,kaya kansu Iri d'aya suke saka wa,duk wani Abu na shawara zasuyi da juna, kowace nayin iyakar k'ok'arinta wajen ganin ta guje b'acin ran y'ar uwarta.
B'angaren karatunsu yanzu komi successful duk da ba class d'aya suke bah,suna tsananin taimakon juna wajen karatu, shahid da shahida Suke guarding d'insu sosai Idan suka dawo gidan, koda salma zasuyi jsce Khairat ce tayi mata time table tana sake fahimtar da ita wasu abubuwan da bata gane bah,hakan ba k'aramin dad'i yayiwa su Maah da Abbu ba, ganin haka yasa yace zai saka asa sunan ta cikin masuyin jsce d'in.

Amman tace Aa yabarta ita ba tajin komi, hakan ma yana mata dad'i don tana koyar da y'an class d'in su, dole suka k'yaleta haka salma tazo tayi jsce d'inta cikin sa,a.

B'angaren yayansu kuwa babu ranar banza da baya bugo waya, kuma kowa Ana gaisawa dashi banda Khairat,duk yadda Abbu zai yi ta ansa su gaisa saidai tace Aa Abbu Kace dai ina gaidashi.

Salma kuwa saboda Shak'uwar su da Areef yasa Abbu Ya siya mata waya 7+ da tayi jss d'inta, tun mutanen gida na mamakin shak'uwarsu har suka daina, don idan suna Waya kamar wata zararra dariya da shagwaba,idan kuwa sukai fad'a Khairat ce ke gaya mata yadda zasu shirya.

Yawan sanar da ubangiji damuwarta da take, yasa cikin ikon Allah duk wani zafi da kunan zuciya da takeji idan taga yadda salma Suke waya dashi yanzu ta samu sauk'i sosai, don wata sa,in ma dariya take musu.

Cikin k'ank'anen lokaci salma ta rufta tarkon kaunarsa,wanda ita kanta bata sani ba Amman Khairat ta Ganota,mamaki take tana jiran taji Maah tayi ma salmar gargadin hakan amman taji ko Uffan batace mata ba, tambayoyi ne cike cikin cikinta,amman baiyuwa tayi ma Maah su don bazata fad'a mata bah.

Ta tattara duk wasu abubuwa ta watsar da su gefe guda, ta d'auki karatunta da muhimmanci,indai ka ganni Zaune to ko dai karatu nake ko kuma ina duba wasu words ga dictionary,na saka Kaina busy da ko hirarshi da salma kemun some times bana ma zaman d'akin balle tayi mun, Ina falo cikin mutane Ina d'an saka baki cikin hirarsu Anni.

Su Anty shidah da Yah shahid Sunyi candy,yanzu su Yah kusan shekararsu d'aya da rabi da tafiya, Yah meenah yanzu mate d'in juna muke,shiyasa k'awancen mu yazo d'aya,komi tazo wajena Khairat kaza Khairat kaza, har karatu meke tare.

*shekara kwana inji y'an hausa.*
Har y'an matan uku sun kammala secondary school d'insu, don har Dadyn meenah ya fara hidimar samar masu admission xuwa jamia,yah shahid yana spain yana karantar engineering,Anty shahida tana katsina tana karantar business administration,ta dad'e tana masifar son harkar kasuwanci,maah taita fad'a akan me zata ce shi zatai, saida Anni ta fahimtar da ita cewa, yaro idan yace zai iya had'iye gatari sai asakar masa k'ota,saboda idan aka matsa mata kan wanda ba taso baza tayi karatun bah, wannan maganar ta anni ce yasa su Abbu suka barta tatafi, y'ar aduwa takeyi amman wajen kanwar Abbu take zaune, don dama goggo baraka tana son Anty shidah.

Manyan k'asa su Yah mujahid da Yah Areef suna can UK  an rik'esu tunda suka gama, wai sai Sunyi masu aikin shekara uku,yanzu cikin ta biyu Suke next year suna gida war haka.
Salma kamar tayi tsuntsuwa taje inda suke,zuwa yanzu Anni tayi mun bayanin yadda muke da yah Areef, sai hankalina ya kwanta, ganin yadda sweetheart d'ina ke masifar kaunarsa Idan aka rabasu inajin tsoron halin da zata shiga,don ba zata iya jure abunda nake jurewa bah, yanzu kam zance Alhamdulillah duk wasu feelings da nakeji nashi narasa, saboda na farko bana ganinsa, ko waya ba muyi, don cikin shekarun nan da basu nan sau d'aya mukai waya Shima ina kwance kan cinyar Maah, naji suna Waya yake tambayata da yi mata k'orafin bana gaidashi,tunda nai waya shine ta bani Shima kuma bai wuce y'an seconds ba.

"yah ina wuni."

muryarsa ta sake zama ta y'an Gayu yace,

"ai da fushi nake dake Khairat,amman dai na huce ya kike ya karatunku."

Nace,
"Alhamdulillah karatu ka gaida yah mujahid."

Na mik'a mata wayar, ita kanta tayi mamakin yadda Nayi, bata ce komi ba, suka cigaba da wayarsu har nayi bacci.

Nida salma kowa ji yake da kyansa,bawai batun son kai bah, zan iya cewa nata b'angare d'aya ne, ni kuwa duka b'angaren biyu na d'auko, don Maah fulanin yola ne na usil, Abbu kuma buzune Amman kuma k'ar yake kamar Jini zaifito jikinsa, yayinda Maah take ruwan tarwad'a amman hutu dajin dad'i yanzu yasaka takoma jawur,
Na biyo Abbu ta wajen haske da manyan idanu wanda idan ina magana suke kunshewa,ga zara zaran eyelashes har wani kwanciya suke, sai tsawonsa don Maah bazadai Kace mata guntuwa ba, kuma ba gajeraba.

Amman am sure ni doguwace kuma tsayina ma daidaici, komina mai tsarine,amman cikar fuskata da cikar halittar jikina duk na Maah ne,da kyawawan hakoranta,da wushirya,masha Allah dai kawai za,ace komi yaji.

Sweetheart kuwa komi na Abbu ne har rashin kib'arta, Idan tayi dariya sak Abbu.
sweetheart kamar kwalin omo take ba nauyi,ga kuma fara,a ko bacci take.
Shiyasa tafini qawaye dayawa don ni k'awayena basu wuce biyar bah, itako lodi lodi haka zaka gansu,in fita mukai kan na had'u da Wanda na sani ta had'u da mutun goma........ Kai sweetheart akwai kwashe kwashe wallahi.

yah meenah ma ba laifi don Itama tubarkallah, Allah yayi mata halitta maikyau, komi yaji kenan don tun yanzu har samari sun fara mata yawa,saida na bata shawarar korarsu don inhar tace yanzu zatai soyayya ba makawa Dady aure zai mata, duk ta firgice don tana son boko kamarni.

An tambayeni me zan karanta nace I like medicine Shima kuma b'angaren hakori,da farko Abbu da maah sunce Ina karatun yayi tsawo,kuma zansha wuya, saida nayi masu kuka sannan suka barni, Shima saida sweetheart taga dagaske baza su barni ba,yasa ta kira Yah Areef tana kukan shagwaba take sanar mashi, dafari cewa yai tabani wayar ya lallasheni, Amman nace tace nafita.

Shi yayi magana aka barmun cause d'ina, Yah meenah kuma, nursing.
kuma nace bazan je wata k'asa ba anan gida Nigeria zanyi.

Yanzu har mun cike komi an bamu admission anan Abuja zamuyi karatun, kuma day zamuyi, sweetheart kasancewar karatun bai wani d'a d'ata da k'asa ba bata wani d'auki cause mai wuya ba, don education ta d'auka fanin intergrated science.
Yanzu registration za muyi mu fara zuwa,b'an gare guda kuma cikin satin nan su Yah mujahid zasu dawo,sweetheart kamar tayi hauka don dad'i nikuwa da naji Ana maganar ma gabana fad'uwa yake sosai.

*wannan kenan.*

  Mu had'u next page.






Mom muhsen ce

ABIN CIKIN RUHINATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang