_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461🅿️.......34
Alhamdulillah biki ya tashi anyi walima lafiya amarya tasha kyau,anyi hotuna kala kala har kuka nai da su ummi suka zo yiman bankwana........lallashina taitayi tana shiman Albarka nan akabar mimi wajen maah zata kara mata sati biyu,yah imran kamar yayi kuka baison tafiyar,sai tsogumi yake mata har ya kureta ta haushi da fada, dama ummi abu kadan zai tun zurata taita masifa,
"Tun yaushe kake man maganar inace maka dan uwanka ne zaiga likita amman kaki fahimta,ko so kake ya mutu anan ne."
Hakuri yaita bata don ya manta shaf da batun ganin likitan Areef din.Kowa ya watse dagani sai husna da yah meenah,suna jiran Ango sai su wuce gida.
Hirarsu suke nikuwa nayi tagumi,duk na firgice nasan dr bazai daga man kafa ba yau,yadda yake wannan rawar kafar tun kan akawoni abun tsoro yake ban,duk jikina yayi sanyi harga Allah inason dr Amman banson making love dashi,hakanan nidai zuciyata bata son bashi kaina........jinake kamar ace ba yau banezai tare,sai kuma naga ai koma yaushe ne dole zai tare ni nabani wlh bana so.
Hawaye na share husna ta ankare dani tayi murmushi tace,
"Yah meenah mutuniyarfa da alamu dai atsorace take,wallahi nikaina tausayi take ban,ganin yadda dr ba sauki ne dashiba."Murmushi tayi ta matso kusa dani tace,
"Sorry my qanwa,babu fah wani abu idan baki saki jikinki bane zakija har wani abun ya sameki,amman inkin sake lafiya lau dan zafin baida yawa."Kallonta nai idona yana zubar da kwallah nace,
"Yah meenah ni wlh banson ya kusanceni kwata kwata,nidai bana so wlh."Ajiyar zuciya tayi tace"bakison shi kenan."
Girgiza kai nai "aa ina son shi kwai banson making love dashine pls ya zanyi wlh ina iya mutuwa akan hakan."
"Subhanallahi!khairat kina cikin hankalin ki kuwa,kinsan mekike fada,mijinki nefa halal dinshi ce ke komi yayi dake baida zunubi sai tarin lada,kifitar da duk wani tunani cikin ranki kicire son zuciya ki cire wani can kisaka mijinki cikin zuciyarki,
Na riga na ganoki khairat kina son ki kaurace ma mijinki saboda wani ko, kiji tsoran Allah.
kinsan kuwa tarin zunubin da kike shirin kwasar ma kanki,shi wanda kike shirin yin wannan wautar yayi biyayya ya dauki kaddara saike,kike shirin wargaza rayuwarnki kansa, auren da kwanansa guda,to ki maida hankali,wlh muddin bakiji maganata bakika aikata har wani abun yabiyo baya,wallahi khairat bakina dana Abbu zan fesa mashi komi."Kuka nake ina cewa
"Yah meenah ni wallahi badan shi zanba kuma ni bakiji nace zan kaurace mashi ba,kawai na gaya maki abunda yake raina ne,banson kusancina dashi ba kuma don bansonsa ba.....katseni tayi cikin fad'aa."Dallah can rufe man baki,keda bakida hankali bakida wayau,to inba haka kike nufi ba mekike nufi kenan ehy,so haukane kanki akafara irin wannan,to ki bada himma,shida yake namiji har zai iya danne son da yake maki ya bi maganar iyayensa,saike ce zaki bijire to Allah yabaki sa,a."
Ranta yayi matukar baci da khairat din shiyasa ta cewa husna tatashi su wuce,inba haka ba nan zata barta bata ga anfanin zamansu ba.
Kuka riris nakeyi ina rokonsu karsu tai amman basu sairareni ba husna dai tace "inyi hkr inyi biyayya,ba kowa yake samun abunda yake soba inkika kwantar da hankalinki khairat zakisha mamakin irin dadin zaman da zakiji da shi,daurewa ake cijewa ake kiyi hkr kiyi biyayya."
Inaji ina gani suka barni nan sukai tafiyarsu,haka nasha kukana har kaina yafara wani azabebben ciwo,gawata masassara ta sauko man dandanan..........haka na koma cikin gidan na shege bedrom dina inda aka fara saukardani,kuka nacigaba dayi har baccin wuya ya saceni.

STAI LEGGENDO
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda