page 3

7 1 0
                                    

🧟‍♂️ *FATALWA* 🧟‍♂️

*BY MEEN@T A YANDOMA*

*JIN JINA A GAREKI BABBAR MARUBU CIYA BISA KIRANA DA KIKAI KIKA MANI GYARE_GYARE, INA GODIYA SOSAI WALLAHI ALLAH YA ƘARA BASIRA DA ZAƘIN HANNU*

*SADAUKARWA*

Na sadaukar da wannan littafin ga yayyena,ina matuƙar alfahari daku a koyaushe.

*RUƘAYYAH A YANDOMA*
*KHADIJA A YANDOMA*
*AISHA A YANDOMA*
*SARAT A YANDOMA*

*PAGE* 3️⃣0️⃣To4️⃣0️⃣

...ƙiƙiniyar ida shigewa yake amma ya kasa,

"Wae Meemah bazaki taimaki mijinki ba?,wallahi Meemah ta! nayarda dake bazani ƙara ƙaryata kiba taimaka man in ida shigewa"

Da ƙyar ya ida shigewa, Abbah Maheer ne ya shigo yana dingishi,

"Mai Jidda! ina kika shige?,ashe zaki iya ganin abincutatwa kitai kibarni?"

"Abban maheer mubar wannan maganar, yanxu dai fadaman miya korosu Meemah?"

Su Meemah dake bayan gado dasukaji haka sai suka fito ido ya raina fata musamman Marwan yayi tsuru_tsuru kamar an kama bera a buta

"Subhanallah!"Marwan kai ne har dakina! Miya Koroku haka?"

Nan Marwan ya zayyana mashi abinda ya faru, sallallami Abban Maheer ya hauyi,

"Yanzu kuna da wannan matsalar kuke zaune,kamata yai kunemi malamai ayimaku karatu a gidan"

"Yanzu kuwa wurinsu zamu"

Yafada yana sosa ƙeya,Maman Maheer da taji abinda ya faru da sauri ta bude ƙofar ta fito,

"Meemah yanzu kunada wannan matsalar baki taba fadaman ba?"

"Maman maheer ina cikin bala'i ko Marwan bai yarda da maganata sai yau da'aka fara taboshi"

Abban Maheer yai masu wa'azi da nasiha yace su fito ya rakasu sukoma gida

Harsun kawo kofa Maman maheer ta jawo mayafi ta goyo Maheer
Ta rugo

"Mutai murakaku nima bazaku barni ni daya ba"

Suna fita sukaga saude na fitowa daga gidansu

"Meemah wai ina kuka je? nashiga na duba ko ina bakowa gidan sai mai gadi"

"Saude yanxu ba lokacin wannan maganar bane,mushiga ciki"

Shiga sukai gidan Marwan har yanxu a tsorace yake yana tafe yana ƴan dube_dube.

"Wai miya faru ƙawata?"

Nan ta zayyano mata abinda ya faru, tashi tai ta dafe ƙirji

"Nashiga ukku ni jikanyar mutum hudu,kinsan kunyi haka da fatalwa kuma kika barni Nashigo gidannan?"

"Saude!" nidai jirani in shiryaa mutai wurin nakan tudu shine kadai maganin matsalar mu"

(Wa'iyazubillah, Meemah kun manta da Allah kuna ganin wani zai iya maku magani matsalar, abinda wasu ke aikatawa kenan da tsanani yayi yawa sai su kauce, Allah duk tsanani katabbatar damu akan tafarkin ka)

"Marwan! Dan Allah ka rakani in sauya kaya sai mu tafi rana ta fara"

Kallonta yai galalah!

"Wai Meemah baki tausayina bakisan bala'in dana gani ba?,"

"Rakani kawai xakai in dauko mayafina"

"Basai kin dauko ba ai nine mijin na yarje maki yafa kalbi mutafi ahaka"

"Ƙawata dan Allah keki rakani"

"Waceni shegiya inji dan daudu,ke nifa ƙawata baxani iyaba yanxu ma in baki gaggauta tahowa muka tafiba yanxu xanibar gidannan"

"Miyai zafi mutai a haka, tafada tana yafa kallabinta"

Fita sukai harabar gidan Marwan ya bude mota suka shiga mai gadi yabude suka fice

Tafiya suke har suka bar cikin gari suka dauke hanya sukai cikin wani ƙasurgumin daji parking sukai suka fito domin hanyar mota batabi saboda lalacewarta

Uwar tafiya sukai sannan naga sun isa wani wuri mai yawan duhuwa gawani babbah dutsi a gabansu

Ta saman duten suka hau da kyar

Babban wurine mai dauke da kawunan dabbobin daji, an zagaye wurin da jajayan gyallaye, kutsakai sukai ciki

Wani burki sukaja! Ganin mutum ya bayyana agabansu

Sanye yake da bante gashin kanshi yayi tsawo duk ya dunƙule saboda dauɗa, fuskarshi zagaye take da dogayen gashi ,Fashewa yai da mahaukaciyar dariya,

"Sannunku da zuwa! Kurufe idanunku ku zauna"

Zama sukai Meemah zata fara mashi bayani ya tari numfashin ta

"Nasan miya kawoku, maganar fatalwace, dama na fadamaku kafin ai maku aiki kan ahmad cewa komi yabiyo baya kanku zai ƙare, kai Marwan kai zai fara daukar fansa kanka, sannan ke Meemah, ya kyalkyale da dariyar mugunta"

"Amma akwai mafita, kuma tanada wahala zaku iya?"

Eh nakan tudu zamu iya suka fada tare jikinsu na kyarma!

Kwarya ya daga ya dauko wani garin magani

"Amshi wannan! Kutabbatar sai dare ya raba zaku turarashi, kada kukuskura kubari hayakin da kuke yafita waje ku fure duka kofofin dakin, in kuka sake yafita kun ƙara jefa kanku a bala'i

Hannunta na rawa ta amsa

"To mizamu bayar?"

"Kubar kudinku aina saba maku aiki kuna biyamasu buƙatunsu yau anyafe maku, maza kutashi kufita da baya_baya"

Tashi sukai suna godiya

Harsun fara tafiya saude tace

"Nifah ku saukeni a gidanmu gaskiya bazani koma gidankuba"

"Haba saude kibiya sai in munci abinci kin tafi"

"Ina!" ai in kinganni lahira kai ni akai, bafa xani koma ba"

Shiru motar tayi kowa yai tsit! Har suka isa gidansu saude aka ajeta ta shige gida

Hanyar gidansu sukayi kowa da abinda yake saƙawa aranshi

Birki yaja ya tsaya batare da yayi hon ba, bare mai gadi ya bude masu,

Kallon_kallo suka hauyi shida Meemah.

*YAU BANYI NIYYAR YIN TYPING BA AMMA DAMUWARKU DANAGA KUN NUNA YASA NAYI, GOBE BANI YI SAI KUMA JIBI INSHA ALLAH*

*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅

FATALWA COMPLETEWhere stories live. Discover now