page 10

5 0 0
                                    

🧟‍♂️ *FATALWA* 🧟‍♂️

*BY MEEN@T A YANDOMA*

*GAJEREN LABARI*

*MANAZARTA WRITERS  ASSOCIATION*

*SADAUKARWA*

Na sadaukar da wannan littafin ga yayyena,ina matuƙar alfahari daku a koyaushe.

*RUƘAYYAH A YANDOMA*
*KHADIJA A YANDOMA*
*AISHA A YANDOMA*
*SARAT A YANDOMA*



*INA MIƘO SAƘON GODIYA GAREKU ƳAN FATALWA FANS COMMENT ƊINKU NA SANI NISHAƊI*

*BARKA DA RANAR  HAUSA TA DUNIYA* ✨🎊🎊

26-8-2021

*INA TAYA DUK KAN HASAWA MURNAR WANNAN RANA, UBANGIJI YA ƘARA ƊAUKAKA HARSHEN HAUSA AKO WACE AL'UMMA, ALLAH YA ƘARA HADE KANMU YA KAWO MANA CIGABA MAI AMFANI.*

*~BARKA DA RANAR HAUSA TA DUNIYA~*
🎉🎊🪄🎊

*PAGE* 1️⃣0️⃣3️⃣

.....Wata dauriya Allah ya sanya a zuciyar Mama addu'a tare da rufe mashi idananun shi.

Kukan da Rabi keyi ya sanya makwabta zagayowa suga mike faruwa, ganin Ahmad kwance jini ta baka ta hanci bai numfashi yasa suka gane rasuwa yayi, haka gidan ya koma gidan makoki, kowa ka kalla idanunshi hawayene ke zuba.

Bayan angama yima Ahmad wanka ake fito akace Mama taje tayi mashi addu'a ta kuma yafe mashi.

Suna shiga ɗakin ita da Rabi ganin Ahmad kwace anrufeshi da likafani fuskarshi kadai ke bude.

Saurin riƙo Mama Rabi tayi ganin wani jiri ya kwasheta, muryar ta harta dishe sai yanzu taji wasu hawaye sun zubo mata, murya na kyarma tafara kwararoma Ahmad addu'a fuskarta hawaye na kwarara.

Da kyar aka samu aka riƙe rabi dan riƙe Ahmad tayi kam ajikinta tana dan Allah kada a raba ta da yayanta.

Mama tayi ƙarfin halin yimata magana, cikin muryar nasiha.
"Rabi'atu Allahn daya bani Ahmad shiya amshi abunshi, mu dauki ƙaddara mu roƙama Ahmad gafarar Allah, addu'armu kadai Ahmad ke buƙata a halin yanzu.

Suna kallo ba yadda zasuyi aka fitada Ahmad, sai dai muce Allah yajiƙan Ahmad da ɗaukacin al'ummar musulmi.

An kai Ahmad, Alhamdulillah yayi mutane ana dawo kai shi gidansu ma baya shiguwa saboda mutane.

Rabi yinin ranar in banda ruwa ba abunda take iya ci, anyi_anyi taƙi cin komi.

Wata mata ce ta shigo gidan,da ka ganta kasan hutu ya zauna ajikinta.

Bayan tayima Mama gaisuwa, take cewa ina Rabi taje Fahad zai yi mata gaisuwa.

*WAYE FAHAD❔*

Fahad ɗane ga Alhaji Mu'azzam shahararren mai kudi, Allah ya azurta Alhaji Mu'azzam da yara guda biyu Fahad sai kuma Siyama, Alhaji Mu'azzam irin masu kuɗin nan ne da basu kyamar talaka ko kadan ga taimakon talaka da masu naiman taimako, Mu'azzam abokin Baban Ahmad ne tun tasowar su, tafiyace ta zuwa Landon ta kama Alhaji Mu'azzam tun Mahaifin Ahmad na raye, shine sanadin rabuwarsu sai kuma yanzu dawowarsu suke samun labarin abinda ke faruwa.

A hankali ta isa cikin soron gidan, zaune yake ya sadda kanshi ƙasa, isowar ta yasanya shi ɗago kanshi idanunsu suka hadu, wani abu yaji ya daki zuciyar shi da ƙarfi, ita ma duk da halinda take ciki hakance ta faru da ita.

"Sannu Rabi! Ya ƙarin haƙurinmu, Allah yajikanshi yasa ya huta ya kai rahama a kabarinshi."

Da Amin ta amsa tare da yimashi godiya ta shige gida.

Bin bayanta yayi da kallo harta ida shigewa gidan, Aldala yayi tare da godema Allah, domin shi yaga matar aure, tunda yake har suka gama zaman turai bai tabajin soyayyar wata yarinya kamar yadda yaji ta Rabi ba, dan shi irin mazan nan ne da mata basu damesu ba.

Anyi zaman makoki inda sai ga Meema da Ladiyo sunzo gaisuwa, Meema hada kukan munafinci ana rirriƙeta.

Kullum a gidansu Fahad ake kawo abinci safe da rana har Ahmad yayi kwana arba'in, alokacin wata irin shaƙuwa da soyayyah suka shiga tsakanin Fahad da Rabi.

Ranar da Ahmad ya cika wata ɗaya da rasuwa ranar aka ɗaura auren Marwan da Meema akan sadakin dubu hamsin.

Anyi biki na gani na fada,ansha fati kala_kala, angwagwaje, yayi ma Meema lefe akwati dozin, ganin haka Ladiyo ta ƙara haukacewa da murnar ɗiyarta ta auri mai kuɗi.

Ankai amarya gidanta lafiya dake kusa da gidan iyayen mijinta.

*MAFARIN MATSALAR*
Ranar da aka kai Meema gidanta bayan su Saude sun tafi ita ɗaya cikin ɗaki tana ayyana irin rayuwar jin daɗin da zata yi a gidan aurenta, jitayi anja ja ƙofar palon kamar za'a shigo kuma sai taji shiru.

Ta sadda kanta tana tunani jitayi an dafa kafaɗarta ta baya, har wani murmushi take ta ɗauka Marwan ne amma tana juyawa taga ba kowa wurin, wani ƙuuu! Cikinta ya bada, a tsorace ta koma ƙarshen gadon ta hada kanta da guiwarta jikinta na kyarma.

Daukewa wutar ɗakin tayi lokaci ɗaya, nan fa tsoron Meema ya tsananta lalibe ta farayi tana son isa wurin ƙofar ɗakin, a hankali cikin sanda take tafiya, jitayi tacikaro da wani abu, cikin sauri tama ƙalƙakeshi ɗaukar ta Marwan ne, jitayi abun yacika taushi hannunshi ta kamo, abunda ya ƙara daga hankalinta kenan jin yatsu guda ukku rak! A hannu, lokaci ɗaya haske ya gauraye ɗakin.

Ƙadangare ne wanda ya kai girman mutum, tagani ta rungume, wata mahaukaciyar ƙara ta saki tare da faɗuwa ƙasa tana ja da baya.

Kofar ɗakin ta nufa da niyyar guduwa, da rarrafe take tafiya cikin sauri tana waiwayen ƙadangare, sai da shi daga inda yake tsaye ko motsi baiyiba.

Tana gaf da kaiwa ƙofar ta rufe da ƙarfi kamar an bankota, wata irin dariya mai ban tsoro ƙadangaren keyi yana nufota, da ƙafafunshi na baya yake tafiya ya miƙe tsaye kamar yadda mutum ke tafiya.

Ƙofar da ake bugawa ta sanyata dago da kanta, komi ya koma dai_dai kamar ba abunda ya taba faruwa.

Ƙofar ya buɗe yashigo ganinta zaune yasa shi dugowa.
"Masoyiyata miya faru na ganki nan."

"Marwan gidan nan tsoratani yake, ka taimaka ka canza mana gida."

"Hhh! Kai amma kin cika tsoro, zaman kaɗaicine ke damunki, a hankali zaki saba."

"Bazaka fahimceni ba ne wallahi ni kaɗai nasan minagani."

"Kinga nifa tunda nike gidan nan bantaba ganin komiba, kawai kin dai tsorata ne."

Ranar haka suka kwana Meema duk bata yadda da gidan ba.

Lokacin ne kuma tagane wane ne Marwan, bazai dawo gida da wuri ba inya fita, duk da dama ba wata sana'a da yake dan Mahaifishi cewa yayi bazaibar ɗanshi yayi sana'a ba tunda ya tara kuɗi komi yake buƙata zaiyi mashi ba sai yayi aiki ba.

Ga wasu halaye da yake mata abu kaɗan zai hauta da zagi, yana zagin iyayenta ga gori iri_iri.

Kamar kullum yau ma ta tashi tunda safe ta haɗa masu  breakfast tana jiran yafito, koda yafito inda take ma bai kallaba.

"Ga abin kari nagama amma naga kamar fita zakayi?".

"Kinada damuwa da fitar da zaniyi?, ko ni yaronki ne da in zani fita saina sanar dake?, to bazanici ba in ana dole saiki danneni ki ɗura mani."

Yana gama faɗin haka ya bangajeta yayi waje.

Ida zauniya tayi Wasu zafafan hawaye na wanke mata fuska, gashi dai ta auri mai kuɗi amma babu kwanciyar hankali da natsuwa.

Haka taci kukanta tagama ba mai rarrashi, tashi tayi taci kalacinta ta ɗauki sauran ta nufi mai gadi ta zuba Mashi, jitayi almajiri na bara harta nufi ɗakinta ta kirashi yazo ya amshi sauran, shigowa yayi yai tsaye yaƙi ƙarasowa.

"Ka matso ka amsa mana."
Fashewa yayi da wata irin dariya, daga inda yake ya miƙo hannushi ya taho wurin Meema yana ƙara tsawo luuuuu!.

*NOTE*
(NIDAI bance kudaina ba majirai Sadaka ba 😂😂 ko ina akwai nagari akwai akasin haka, ita Meema abinda ta shukane take girba 😜. Ita sadaka tana maganin bala'i in zakayi kayita da niyyar mai kyau, Allah yasa mudace.)



*BARKA DA RANAR HAUSA, ALLAH KA ƘARA ƊAUKAKA YAREN HAUSA AKO INA.* 🥳✨🪄


*COMMENT* ✅
*SHARE* ✅

FATALWA COMPLETEWhere stories live. Discover now