6

413 12 0
                                    

_~ALƘALAMIN JIKAR NASHE

YA  ABIN  YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387


Follow me on wattpad

Nazeefah381

ELEGANT ONLINE WRITERS

(Haɗin kai shine takenmu.)




Ya Abin Yake? Daban yake da sauran.

✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽

6

Duk tunaninsa lefen Gadanga ake haɗawa, shi yasa bai damu ya tambayeni ba.

Sai ana gobe ɗaurin aure kamar an jefo su sai ga su sun zo da yamma. Fuskata babu wani alamun damuwa na tareta da murnata da komai, na malala mata tabarma a rumfa, ta kuwa zauna ranar kamar abin arziki har tana gaisheni cikin gwarancin hausarta. Lauratu da ta dawo daga islamiyya ganin ta yasa ta faɗawa jikinta a guje sai naga ta tureta a fusace tana kaɗe jikinta, mamaki ya hanani cewa komai sai janye Lauratu da ta fara kuka nayi. Lokacin bata wuce shekara goma ba, cikin lallashi nace mata yi haƙuri daɗin abin burinmu daf yake da cika."

Sai naga ya kalleni da alamar neman ƙarin bayani, ni kuwa na galla masa harara. Muna zaune Malam ya dawo fuskarsa fal ɗauke da murmushi da katinan aure a hannunsa. Shi kansa Malam ɗin ba fara'a ba girmamawa ta shiga gaisheshi, shi kuwa ya amsa ba tare da komai a ransa ba. Ya miƙe ya shige turakarsa yana faɗin "Idan ka tashi tafiya ka sameni."

Ƙasa yayi da kansa kafin ya ce "Malam ai tafiya zamuyi jirgin dare yau zamu bi." Daga ni har Malam ba wanda bai firgita da jin zancen ba muka ji tamkar saukar aradu a ka. Ni dai har razana nayi.

Malam ya dawo da baya yana masa kallon tuhuma kafin ya ce "Da kazo mai kace min? Ca nake cewa kayi wata guda zaku yi?" Ya ɗaga kai kawai, idanunsa sun nuna yana cikin wani yanayi na ƙaƙa ni kayi. Malam ransa a ɓace ya ce "To menene dalilin canjin zancen?" Daburcewa yayi sosai kafin ya ce "Kawai dai zafin garin ta ce ya isheta." "Shine kai kuma kabi abinda tace wajen ruguza shirinka kuka ɗaura aniyar tafiya yau?"

Na faɗa raina a ɓace da tunanin sun canja min ainahin Ummaruna wannan ba nawa bane wani ne can daban. Zufa ya goge kafin ya ce "Duk ba haka bane,jarrabawa zata je ta zana." Malam Yaja ajiyar numfashi a kufule ya ce "Jarrabawo ba jarrabawa ba, ta bakin uwarka ne duk an canja maka halaye, to albishirinka ungo nan."
Ya faɗa yana manna masa katin auren a tafin hannun da ya miƙo "Ɗaurin aurenka gobe da Sadiya, sai ka sanar mata idan taga zata tafi sai tayi gaba ita kaɗai." Sam bamu san zufa bace take karyo masa, sai da na kai idona kansa sannan na ankare. Na kuwa saka salati ganin yarda ya durƙushe a gaban Malam yana faɗin "Kayi min rai wallahi ba zan iya haɗa Sakna da kowacce mace ba."

A zafafe Malam ya ce idan an ɗaura ka saketa, amma ka tabbatar in dai ni na haifeka to babu shakka aure ya ɗauru." Yasa kai ya fice Lauratu da take gefe sai dariya take zuciyarta fal farin ciki, duk da umbolar da nake mata bata fasa ba. A zuciye Ummaru ya jawota zai fara jibga. Na kuwa saka
Hannu na janyeta ina cewa kada ma ka fara, don wallahi ba zan ɗauka ba. Ina kallo tana tambayarsa daga yanayin fuskarta na gane tambayarsa take masifar mai muke? Sai naga ya saki murmushin dole ya girgiza mata Kai.

A daddafe ta bari suka cika awa guda cur, naga ta miƙe hannunta ɗauke da Jakarta ta kalleni a banzace naji ta ce "Good bayi." tana ɗaga min hannu shima ya mara mata baya bayan ya ajiye min wata leda yasa kai ya fice da sauri.

Shikkenan daga ranar bamu sake ganinsa ba, amma haka Malam yasa aka d'aura auren kuma Sadiya ta tare a shiyyarsu da aka gina mata ita da Umarun da
Ya wuce ya koma Ƙasarsu ko salaam babu.

Ya Abin Yake?Where stories live. Discover now