7

423 11 0
                                    

_~ALƘALAMIN JIKAR NASHE

YA  ABIN  YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387


Follow me on wattpad

Nazeefah381

ELEGANT ONLINE WRITERS

(Haɗin kai shine takenmu.)



********************************

Hankalinta a tashe take duban yarinyar kafin ta ce "Wannan karan ma Mace ce?"

Ina murmushi na amsa mata Macece kyakykyawa kuwa har tafi Najwa kyau." Wani tsaki tayi, kafin k'wallar da ta taru a idonta ta zubo mata cikin muryar kukan ta ce "Ya Allah yaushe Zaka cika min burin da na dad'e ina fata."

Da sauri na janyo  ista'aza raina a b'ace na ce "Sakina me kenan? Shin ba zaki godewa Allah ba da ya baki kyautar yara matan? ki kuma yi addu'a Allah yasa su zame miki sanyin Idaniya."

Hawayen fuskarta ta d'auke kafin Ta ce "Ni ban ta'ba son haihuwar mace ba, kullum burina da tunanina a haihuwar yara maza yake, sai gashi Sadiya tana samu ni ban samu ba."

A zafafe nace Allah ne yaso ya jarrabeki, sai kiyi ta istigfari, da kika samuma kike haihuwar wasu suna can suna rok'on Allah ya basu yaran ma kowane jinsi ne amma bai basu ba, Sai ke da kika samu har kike k'ok'arin tantance jinsin da kike so, ki tuba ga Allah kafin yayi fushi dake."

Na mik'a mata yarinyar ta karb'eta cikin halin ko in kula sai kuma ta saki d'an murmushi ba mamaki na ganin yarinyar kyakykywar gaske ce.


____________________________________ Bayan sunan yarinyarta ta biyu da sati biyu Najma Allah ya karb'i ran Malam bayan ya sha doguwar jinya, tabbas mun shiga alhini da tashin hankali kuma mutuwar ta shiga jikin mu sosai bare ni da nake ganin mutuwar tasa ni aka yiwa. Haka Rabbi yake baya barin wani don wani yaji dad'i.

A tsukun lokacin bayan na fita daga takaba mahaifinki ya kammala wannan ginin da muke ciki Muka tattara muka dawo, cikin birnin Kano.

Anan aka yi bikin Lauratu da Gadanga da ya auri k'anwar Sadiya Murjanatu.

Anan kuma iyayenki suka ta hayayyafa har zuwa sanda aka zo kan cikinki, Sakina ta dinga murna da fallasuwar cikin, mu dai bamu san dalili ba.

Wata rana taje asibiti ta dawo sai gata ta shigo d'akina da sauri ta zauna a saman kujera takarda a hannunta tana ta jifan Yayanku Hammad da murmushi, wanda bamu san dalilin da yasa ya tsaneta ba, duk da a lokacin bai zarce shekaru sha tara ba, yaro ne shi mai Kazar-kazar da fara'a ga son mutane amma tashi d'aya gaba d'aya halayensa suka canja ya zama mafad'aci, miskili da son kad'aicewa shi kad'ai ba kuma ya san ganin matar Babanku,
Ko me yake da zarar ya ganta yake barin wajen.

Kamar a tsorace yake da ita. Kuma tambayar duniya an masa ya ce "Bakomai" Ganin lamarin nasa kamar ya fara girmama Babanku ya tasa shi a gaba akan lallai sai ya fad'i dalilinsa, take ya sanar dashi son fita waje karatu aka ce ya zab'i k'asar da yake so ya ce "Birmingham" dake can a k'asar England.
Nan kuwa aka fara yi masa shirye-shiryen tafiya wajen.

Da murmushin ta mik'o min takarda tana cewa "Didi Burina zai cika, wannan karan cikin namiji nake d'auke da shi, bayan na k'i haihuwa har shekaru biyar saboda ina tsoron sake haihuwar mace sai gashi Allah ya cika min burina a wannan karan namiji zan haifa." Ta fad'a idanunta cikin na Hammad, gani kawai nayi ya mik'e da sauri ya fice daga sashen nawa.

Nima cikin murna nace mata "Masha Allah, abin Allah kenan da har kina cewa kin daina haihuwar?"

Da murna ta mik'e ta fice ni kuma na bi bayanta ina taajjibin lamarinta.

Ya Abin Yake?Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang