Page 7

392 13 1
                                    

*A DAREN AURENA*

            BY

MissDmk✍🏻

Page 7

*FARKON LABARI*

Tsaye nake bakin titi ina jiran driver ya iso, gashi gari na ruwa an hada hadari, nafi minti goma tsaye bai iso ba, daga karshe dai fara takawa nayi da naji horn din mota a bayana, har da na jiyo dan yi mai matsifa na shanya ni da yayi, kawai sai naga wani daban..

Juyawa nayi na cigaba da tafiya ta, still yana bina a baya, ganin da gaske yakeyi na juyo a fusace nace lafiya? Fitowa yayi daga motar yace haba yammata ke ko kya amsa sallama koh?

Nace banyi niyya ba to, don Allah malam kadaina bina, ina cikin magana sai ga idi ya karaso, cikin tsiwa nace zaka yi bayani idan muka koma gida nayi magana na shige motar ba tare da sake waiwayar shi ba...

Mun isa gida kenan sai gashi shima a bayan mu da mamaki nake kallon shi bance komai ba na shige cikin gida..

Amma kuyi wa Idi warning kullum sai ya shanya ni a waje sai kace kayan shanya?

Yi hakuri auta, nice na aike shi kasuwa kinsan yau Abban ku na hanya tayi magana tana murmushi,

Tsalle na daka nace can't wait to see him, ina cikin murnan naji horn din motarsa, aguje na fita naje nayi hugging insa, nace Abba I missed you so very much..

Yace I missed you more baby na, ya hadda ana zuwa ko?

Eh Abba dawowa na kenan ai ka shigo..

Masha Allah, Yariyar babanta, Allah yayi maki albarka. Na amsa da Amin.. Abba ya mikamin tsaraba yace ga naki bara nagana da bako a waje, shigewa ciki nayi cike da murna. Direct daki na nufa na bude box din I was astonished by what I saw.. Tube Hijab nayi na gwada gold necklace din ina kallon yadda yayi min kyau ta mirror, saida na bi komai na box na bude kafin na wuce toilet to freshen up, coz nasan tare zamuyi dinner da Abba yau..

Bayan sallah isha muka hadu a dinning table, Amma tace ah bashakka shine ko a nuna min saide nagani a jikin Fa'izah?

Murmushi nayi Ina shafa necklace din, nace Amma how did you see it? Isn't it beautiful?

Amma tace it is baby, a tsofe lafiya, muna cikin haka Abba ya shigo tare da Ya Saleem wato yaron limamin masjid din mu..

Gaisawa mun kayi kafin nayi serving ma kowa, mun ka fara cin abinci, Abba yace daga jin wannan zobo juice yarinyan Baba tayi, murmushi nayi nace yes Abba...

Abba yace ashe yarinyan Baba ta girma ban sani ba? Amma tace wana girma kuma? Yarinya da saura 2ys takai 20 ai saide ace ta tsufa.. Turo baki nayi cikin shagwaba nace nide ban tsufa ba..

Dariya Abba yayi kafin yace that reminds me of something baby, dazun na hadu da wani a gate kuma yace min gunki yazo, nan take naji gabana ya fadi nace ni kuma Abba?

Eh yace ke ya biyo yana so abashi iznin yafara zuwa gunki, kuma daga ganin shi mutumin kirki ne though na bashi appointment da yazo gobe...

Ajiye spoon nayi nabar dinning, girgiza kai Amma tayi tace kaji gara daka bashi dama yazo Idan muka biye ta nata ba zata kula kowa ba indai mutumin kirki ne ka bashi dama...

Abba yace in shaa Allah, nace masa yazo gobe by 2pm zamu zauna dashi.. Amma tace Allah ya kaimu gobe ya amsa da Amin...

Washe Gari dasafe tun 8 na safe na wuce hadda, na sauka a mota sai ga Hafiza cikin fushi nake kallon ta, murmushi tayi tace haba K'awa ta afuwan,

Nide bazan miki magana ba, jiya kka ki zuwa hadda kuma baki  kira kin sanar dani ba..

Hafiza tace afuwan K'awa ta labarin da tsawo, nuna min ring inta tayi tace kalla ki gani, rike yatsan nayi nace Laaa zoben azurfa? To letter F dake kai na menene?

A DAREN AURENA Where stories live. Discover now