PAGE 1

10 1 0
                                    

GOBENA
          ( MY FUTURE)





               ✍️

            *AISHA*
         *GALADIMA*


'''Follow me on whattpad
@Ayshagaladima6666'''

'''THE ONLY ONE WHO WILL NEVER FAILED YOU IS ALLAH
'''

1️⃣

__________________________
Tsaye take a gefen titi kallon gefe da gefen titin take Wanda hakan  ke nuna tsallaka titin take son yi se dai motoci kamar hankado su a ke duk da kasancewar safiya yace , tsintsiyar hanunta ta Kuma kalla inda black agogon ta ke daure ta kalli time 7:15 ta gani Dan siririn tsaki taja ,kamar ance ta dago kanta wani karamin yaron da baze haura 6years ba ta ga ya nufo titin gadan gadan ,zare idonta tayi sosai zuciyar ta na harbawa da sauri ba tare da tunanin komai ba ta kalli gefen damanta wata motar ta gani a guje tana kokarin kawowa yayin da yaron ya Riga ya kawo kusan tsakiyar titin ba tare da tunanin komai ba ta yi saurin Hawa titin da sassarfa ,horn din da mamalakin motor din yayi da karfi ya ankarar da yaron ,rudewa yayi Yana zarar idonsa tare da rashin sanin abun yi ganin mutum a kusa da shi ba tare da tunanin komai ba ya   fada a jikinta , itama rungume sa tayi tsam tare da runtse idanunta ,zuciyarta na wani kalar harbawa, ta Riga ta sadaqar da ba abun da ze Hana motor din tabi ta kansu, rawar da jikin yaron keyi da kirjinsa ke harbawa da Kuma tsittt din da taji titin ya Dauka shi yasa a hankali ta Fara Bude lumsassun idanunta ,fitilun motar ta Fara cin Karo da su Dab da su ,Wanda hakan ke nuna ba karamin birki me motar ya ci ba da ba abunda ze Hana yabi ta kansu ,da ga Nan se wasu kafafu guda shida dake sanye da  Talkamin sojoji Army green ,tun daga kafa ta Fara kallonsu har zuwa kan fuskokinsu giant bakaken sojojine karfafa ko wane cikinsu dauke da gun dinshi a kafada ,wasu miyau ta hadiye jin kamar makoshinta ya bushe "muqut" karar hadiyar ta bayyana ,kokarin zaro yaron take daga jikinta Yana Kara nanike Mata ,ganin da gaske baze jawu ta wasa ba yasa ta sa Dan karfi ta cirosa , tsaye yayi fuskar tasa har yanzu da alamun tsoratar da yayi Bata sake shi ba ,kallon wadanda ke zagaye da su yayi ya juyo ya kalleta kokarin komawa jikinta yake tayi saurin rike hannunsa Tana kallonsa ,raurau yayi da ido har kwallah ta Fara tarar Masa a hankali kamar me koyon magana Tace Masa"ya akayi " a hankali tayi maganar shi Kam gefen kunnanta ya Kara kansa yace yace "Don't let them take me to Abbuh" ya Kare maganar cike da tsoro ,A hankali ta Mike tsaye ta gyara zaman Jakarta ,ta Bude Baki da niyyar yin magana se ga wani sanye da kayan sojojin , Kyakyawa bakin bafulatani yace "Areef are you okay?"

Daga kansa kawai yayi "ok let's go" cewar sojan

Kamar ze saki kuka again ya juya ya kalleta ganin har lokacin Bata yi magana ba

Kallon sojan tayi cike da dauriya ta ce "please Don't take him to Abbuh and don't tell him what happened just now"

"Okey" yace Yana murmushi yana mamakin karfin halinta

Juyawa tayi ta kalli yaron da aka Kira da Areef Tace "Areef yace baze fada ba and kaima karka sake shigowa titi haka baka diba ba I don't want to loose you " ta Kare maganar Tana murmushi ba tare da ta kawo komai a ranta ba
Wani Kyakyawan murmushi ya Areef din ya sakar Mata ,yayin da sojan dake kokarin Jan hannun Areef yayi tsaye Yana kallonta cike da mamakin kalmar da tayi Amfani da ita ta I don't want to loose u ,hannunsa ya saka cikin na Areef din suka Fara takawa, tsaye tayi Tana kallonsu har Bayan sun Fara tafiyar Areef juyowa yayi Yana Mata bye bye itama daga nata hanun tayi Tana Masa bye har suka shige cikin babban Hotel din dake gefen titi

Karar horn din motoci ya dawo da ita hayyacinta ,jiki a mace ta tsalakka titin ,yayin da jikinta duk yayi Mata sanyi Tana me kokarin kawar da tunanin Abunda zuciyarta ke kokarin tariyo Mata
Suna shiga cikin hotel din Direct wani VIP side suka nufa  step step suka Fara Hawa bayan sun gama Hawa suka nufi wata babbar kofa ,Dan Dakatawa yayi Jin Kamar hannun Areef din na rawa ,dago lumsassun idanunsa da suka Fara Tara kwallah yayi  ya kalli sojan dake rike da hanunsa ya Bude Baki zeyi magana ,se shi sojan yayi saurin Dora yatsanshi a Baki yace "shiiiii, don't utter a word or Abee will hear u and wipe those tears" Jin haka da yayi yasa ya saki wata Ajiyar zuciya ya tabbatar da uncle Khalil baze ya fadawa Abee din nasa ba, hannu yasa yayi saurin goge kwallar dake son sauko Masa ya Kuma kallon Khalil din murmushi ya ga ya Masa shima ya saki nasa murmushi n take wata siririyar wushiryarsa ta bayyana
A hankali ya daga hannu yayi knocking din kofar ,shiru yaji se da ya Kuma knocking a Karo na biyu yaji ance "come in" cikin wata husky voice ,Tura door din yayi suka shiga bakinsa dauke da sallama

Cikakken matashi me Kamala ne zaune a Daya daga cikin kujerin dakin ,jikin sa sanye da Arab jallabiya white colour ,hankalinsa gaba ki Daya Yana ga television ,inda ake haska wani hari da Yan bindiga suka Kai a wani kauye a cikin jihar zamafara , Khalil sakin hanun Areef yayi shima ya nemi Daya daga cikin kujerin ya zauna , ganin gaba Daya Abee din nasa hankalinsa baya kansa yasa ya sauke wata boyayyiyar Ajiyar zuciya ya nufi abincin da ya gani a dinning table din dake gefe ya Fara cin abincinsa
Bayan ta tsallaka titin adaidaita sahu ta tare ta shiga se bayan ta zauna take fada Masa inda ze kaita tsuwwar 'yar karamar vivo dita da taji yasa tai azamar Bude Jakarta ta fito da wayar kallon screen din wayar tayi ,ganin sunan Aysha na yawo a wayar yasa ta Dan zaro Idanunta tare da dagawa ba ta Kai ga magana ba taji daga can Bangaren ance "Nadiya ina Kika tsaya ne yau kin kuwa duba time Kinga ko karfe nawa ,ga Director can ya shigo gashi har an gama Assembly Yara duk sun shiga Aji ,Ammah yaran Ajinki kamar wadanda ake kadawa ganga, har korar su nayi suka shiga Aji Ammah wlh gasu can sun fito ,Kuma shi me kan kwakwar Yana zuwa wurin su ya nufa ko office din headmaster be nufa  ba" tunda ta Fara maganar se yanzu ta tsaya ,ita ko Nadiya Banda faduwar da gabanta keyi har wata zufa ce ta keto Mata a lokaci Daya , Tana ji Aysha na cewa"Nadiya kina jina kuwa?" Ammah Bata bi ta kanta ba kiiiit ta kashe wayar........✍️

Aysha galadima ce
In Naga ruwan comment zan ci gaba😂

GOBE NA (MY FUTURE)Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz