page 2

4 1 0
                                    

GOBE NA
            (MY FUTURE)






                 ✍️

             *AISHA*
        *GALADIMA*


'''Follow me on Wattpad @Ayshagaladima666'''


'''GAISUWA TA MUSAMMAN ZUWA GA'''

'''Hassan Atk
Hussain 80k'''




2️⃣

___________________________

Jiki a mace ta mayar da wayar a cikin Jakarta ,Hasbunallahu wani'imal wakeel dai take Mai Mai tawa a cikin ranta, har suka karaso Bata San sun karaso ba se da taji karar cin birkin me Adaidaita tukunna ta dawo hayyacinta ,sauko wa tayi tare da Mika Masa gudar #200 karba yayi ya ciro canjinta ya Bata  yaja kekensa yai gaba , daga kanta tayi tare da kallon ginin makarantar Wanda a sama a ka rubuta ma
*QUEEN SAUDAT ACADEMY* dunfarar makarantar tayi cike da zulumin cewa wata kil yau Ranar barin makarantar ta ne yayi ,Tura get din tayi ta shigo ganin ba kowa a harabar makarantar yasa ta Sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da hanzari ta nufi class dinta Bata ma bi takan signing book din dake office din headmaster ba, Tana shiga class din turus tayi tsaye ganin mutumin dake tsaye rike da marker Yana rubutu a white board din dake ajin ,wani kakkauran mutum ne dake sanye da black suit a jikinsa se katon cikin dake garesa kamar an kifa kwarya ,fiye da Rabin kansa kuwa sanko ne, wani kallo ya watsawa Nadiya tare da cewa "follow me" ya fita daga Ajin biyar bayansa tayi Dan Bata da wani zabin da ya wuce haka,Kai tsaye office din headmaster ya nufa Yana shiga da sauri headmaster ya Mike Yana fadar "welcome sir" be bashi Amsar komai ba ma face Zama da yayi Akan kujera ,Nadiya Ahankali ta shigo office din tare da sallama a bakinta , headmaster ne yai karfin halin karba Mata ,Dan ganinta kadai ya fassaramasa abunda ke faruwa yaga director ransa a bace , "good morning sir" Nadiya Tace Tana kallon Director yaja wasu sakanni kafin yace "Ba gaisuwa ce ta kawo ni ba ,dama haka kike zuwa aikin a duk lokacin da kika ga dama yanzu fa After 8 first period har ta shige Yara su ka dai a aji ko makarantar government ban tunanin malamansu na zuwan ganin dama ballantana private school babba kamar wannan ki dinga zuwa school duk sadda Kika ga dama " katse shi tayi ta hanyar cewa "am very sorry sir ka gafarce ni Insha'Allah hakan baza ta sake faruwa ba " idonta har sun cika da kwallah ,kasan cewar Director din dama saurin fushi ne da shi dama Ammah Yana da saurin sauka Dan jimm yayi kafin yace "ok this is a last warning da Zaki zo makarantar Nan a wannan lokacin " godiya ta shiga yi Masa yace ta wuce class kawai ,ficewa tayi tana ma Allah godiya tsallakar da itan da yayi ,Bayan fitar ta fada ya shiga yima headmaster shima ,hakurin dai shima ya basa tare da sanar dashi zuwa latti ba halin Nadiyar bane se dai yau din akwai abunda ya gifta
Tana shiga Aji karantar da yaran ta ci gaba dayi har zuwa 9:45 da aka kada kararrawar tashinsu Tara ,daga Nan Daya Bayan daya suka fita ,se sannan ta samu sukunin Zama akan kujearar Roba da aka tanada don malami , zamanta kenan se ga Aysha ta fado ajin Tana cewa"yadai Nadiya ba ku hadu dashi  bane ?" Murmushi ta sakar Mata tukunna Tace "mun hadu Mana" Nan ta kwashe yadda sukayi ta sanar Mata , dariya tayi tare da cewa"lallai kin tsallake rijiya da baya baya"
Tsagaitawa tayi da dariyarta Tace "nikam me ya tsayar dake yau kikayi latti"  yanayin fuskarta a take ya sauya sannan Tace "na tsaya neman abunda zan sawa cikina ne fa" ta Kare maganar tare da kallon Aysha da manya idanuwanta da kwallah ta Fara taruwa a ciki ,ita ma Aysha fuskarta ta ba walwala Tace "Ammah Nadiya ba nace ki bar tsayawa ba ki dinga fitowarki Ni zan dinga zuwa Mana Da abincin Breakfast ba" ruwan hawayen da suka saukowa Nadiya a fuska tasa hannunta ta goge sannan ta Kuma kallon Aysha Tace "Habah Aysha Dan kince haka Niko se na biye Miki sannan kin San fa ba zaman kaina nake ba aure fa nake Kinga hakanan zan daure nayi Amfani da abunda ya ajiye din" ita kanta Aysha goge kwallarta tayi sannan Tace "ok idan an tashi nidai ki tsaya na sauke ki a gida  ,to Tace Mata tare da cigaba da marking littafan yaran
Fita Aysha tayi daga class din Tana tunanin wane irin mijine Allah ya had a kawarta da shine , Wanda Allah ya Azurta da mace kamar wannan Ammah yake wulakantata yadda yagga dama duk da Nadiyar ba komai take fada Mata ba Ammah Ramar da Nadiyar keyi ya Isa ya sanar ma kowa ma Bata cikin kwanciyar Hankali
Kowace aikinta ta ci gaba dayi kasancewar private school din teacher per class ne a  primary session din da suke ,se karfe 2:pm aka kada kararrawar tashin malaman yaran tun 1:30 aka sallamesu , Tana fitowa ta tarar da Aysha school premises itama ta fito , motar Aysha duk suka nufa suka shiga, kunna motar tayi suka fito daga makarantar ,se da suka Fara tafiya akan titi tukunna Aysha ta dubi Nadiya Tace "Ni Kam Nadiya Wai har yaushe Zaki ci gaba da Zama da wannan mutumin marar tausayi ne? Shiru ne ya ratsa motar na 'yan sakanni tukunna Nadiya Tace "Har zuwa lokacin da Allah ya kawo karshen zaman Addu'ar da nake yi a kullum ina da yakinin ubangiji na Yana jina Kuma da sannu ze kawo ma Rayuwata mafita"
Ajiyar zuciya Aysha tayi Tace "Hakane Kuma ki Kara dagewa da Addu'a na San cewa Ubangiji gyangyadi baya  kamasa balantana har yayi bacci " murmushi Nadiya tayi Tace "Hakane" tafiyar mintuna 15 ce ta kawo su kofar wani Dan matsakaicin gida me get black , parking din da Aysha tayi a kofar gidan yayi dai dai da fitowar wani mutum Wanda akalla shekarunsa na Haihuwa zasu Kai 37 years dogo  chocolate colour skin ke dashi Yana sanye da shadda brown colour ,motar ya tsaya Yana kallo , Nadiya da hankalinta ya tashi a lokaci Daya balle murfin motar tayi ta fito ,ganin haka yasa Aysha fitowa itama , "Ina wuni "Tace dashi kamar an Masa dole yace "lafiya Lau " maganar Nadiya ce ta katse Aysha da tai yunkurin yin wata maganar Tace "Nagode se gobe idan mun hadu " Tana fadar haka ta nufi get din shiga gidan ba tare da jiran jin me Aysha din zata ce ba,ganin haka yasa Aysha komawa cikin motar ta ta wuce ita ma , da harara yabi motar Aysha din sannan yayi kaycci ya shiga gidan ,a bedroom ya isko Nadiya Tana rage Kayan jikinta Bata San da shigowar shi ba se maganarsa taji Yana cewa"ke wane rainin hankaline wannan da Zaki dawo 2:30 Bayan nasan 2pm ake tashinku Zaki shiga motar waccan ku dinga yawo to Wallahi bazan daukar Miki ba ,daga yau Kar na Kuma ganinki a cikin motarta ,Kuma ki fito ki Samar Mana Abunda zamu ci Ni da my love Kar ki ja min Asarar Abunda ke cikinta 
................✍️

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 18, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GOBE NA (MY FUTURE)Where stories live. Discover now