17

90 11 1
                                    

*...BASHI!*
   _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*K.W.A*

_Sadiya S. Adam🌸✍️_

                   Page 17

__________🖌️Ji tayi gaba ɗaya ta kasa ƙara motsa ƙafarta, a take a gun ta suma.

*20 Minutes Later*

A hankali ta buɗe idanunta, ta sauke akan Badiyya, ɗaya daga cikin masu aikin gidansu. Zumbur ta miƙe saboda tuno abubuwan da suka faru. "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" Ta faɗa tare da dire dogayen ƙafafunta a ƙasa. "Baki jindaɗi, Doctor ya ce jininki ne ya hau"  "Waye ya kasheta?" Aziza ta furta hankalinta a matuƙar tashe. "Ba mu sani har har yanzu 'yan sanda na kan gawar"
"Miƙe min gyale na" Ta yana sannan ta fita.

Tana fitowa ya ɗago ido ya kalleta "Meyasa ta fito yanzu?" "Dole na fito saboda ina son sanin abinda ya samu waccan yarinyar." Ta faɗa tana gyara glass ɗin idanunta sannan ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun gidan. "Aziza..." "Officer Yayana baya nan, dan haka zargi kuma dole ya bar kansa" "Bamu taɓa zargin Muhasin da kisa ba, shiyasa zaki ga bamu taɓa kama shi ba" "A yanzu waye ya yi kisan?" "Har yanzu basu sani ba, amma bincikene kaɗai zai tabbatar mana da wanda ya yi" Miƙewa ya yi, itama da sauri ta miƙe tana kallonshi.
"Akwai fa baƙuwar da mukayi jiya, tana ina?" Aziza ta tamvaya.

"Bamu samu kowa a gidannan ba, sai ma'aikatanku, sune ma suka shaida mana kun tafi asibiti tun a daren jiya."

"Badiyya jeki ɗakin baƙuwar nan ki kira mana ita." Aziza ta faɗa tana kallonta. Da sauri ta nufi ɗakin, sai kuma ta dawo "Babu kowa"
"Ko dai tana toilet"
"To ai tun safe naga ta fita da akwatinta, dan nine ma ta saka na tarar mata napep"
"What...?" Mahmud ya furta yana zare glass ɗin idonsa.

Kallon Aziza ya yi ya ce "Zamu tafi da ɗan abinda muka samu, in yaso a hankali zamu cigaba da bincike, itama gawar da ita zamu tafi asibiti a ƙara bincika, dan haka kafin a gama bincike sai ku kira 'yan uwanta." Maganar yake yana kallonta amma gaba ɗaya hankalinta ya kai ƙololuwar tashi.

        ***** ***** ******

"Ban yarda da auren nan ba" Ya faɗa tare da miƙewa a fusace.
"Haba Arɗo ni fa ina son shi"
"Malamina ya shaida min muddin kika aure shi sai ya mutu. Wannan annoba ce tazo mana dan haka shaidai ya tafi ya bar mana gari, domin muna zaman lafiya ba zai zo ya birkita mana al'amura ba." Muhasin dake durƙushe a ƙasa ya kasa cewa komai. Ita kuma Zaliha kuka take.

"Yanzu ke kin ajje kunya ta fulani kina kuka dan na hanaki auren saurayin da baki san daga inda ya ɓullo ba."

"To ka hana nayi masa magani kuma sannan ka hanani aurensa, gaskiya ni dai Arɗo ina ƙaunarsa kuma zan aure shi dan in masa magani"

"To sai dai ki zaɓa, ko dai mu iyayenki ko kuma wannan baƙo"
Jin haka ya saka Muhasin cewa "A'a Baffa ba za ayi haka ba, zan tafi kawai kuma ba zan yarda Zaliha ta saɓa muku ba" "A'a sai dai mu tafi tare" Ta faɗa tare da miƙewa.
"Yanzu kin zaɓi wani a kanmu Zaliha?" "Inno gaskiya ni ba zan zauna ba, saboda ni na san ba zan auru a nan ƙauyen ba, ki duba fa kowa guduma yake, shikenan haka zan ta zama ina cuttuwa" "Shikenan kije inda ba zaki cuttu ba"

Arɗo ya ya yi shiru bai ce komai ba lokacin da Zaliha ta miƙe ta bar gurin a fusace. Muhasin ya kalli Arɗo sannan ya sauke kai ƙasa. "Kuyi haƙuri dan Allah na san zuwana gaba ɗaya ya zame muku matsala da kuma rashkn kwanciyar hankali, amma insha Allah gobe da sassafe zan bar nan"

"A'a, karka tafi" Arɗo ya faɗa sannan ya zauna. "Tabbas ina tsoron in aura maka Zaliha, domin ita kaɗaice 'ya a gareni, shi ɗan uwan nata ɗan ƙanena ne, shiyasa ban yarda na salwanta rayuwarta. Yadda ka bani labarinka na tsorata ainun, sannan kuma na faɗa maka dalilina na hana Zaliha zama mai magani. Amma dai tunda ta dage akan haka zan yarda tayi maka magani muka ko Allah zai sa a dace"
"Na san yadda kake ji a ranka Baffa, duk sa ba shiga zuciya nake ba, to amma ina ganin hakan akan fuskarka, idan har baka gamsu da tayi min magani ba, ka barshi kawai, ni kuma zan nisanceku dan gudun kar Zaliha ta ɓata muku rai"
"Nima uba ne, zan so ka samu lafiya ka kuma koma cikin ahalinka, dan haka zaka zauna anan tare damu har zuwa lokacin da zaka samu lafiya" Shiru ya yi bai ce komai ba.

You'll also like

          

              **** **** ****

"Ga Habib yazo fa" Inna ta furta tana kallonta. Ita kuma ta kalleta tare da ajje littafin Tauhid dake hannunta, tare da jan dankwalinta ta ɗaura a lokacin kuma ya yi sallama ya shigo.

Ɗan harararshi tayi, shi kuma ya yi murmushi ya zauna. "To bara ni na ƙarasa aikina" Inna ta faɗa tare da barin ɗakin.
"Sai yau ka tuna dani ko?"
"Na san dama shi ne dalilin hararar da ake min ko?"
"Eh mana, ba kaine kace duk bayan kwana biyu zaka riƙa zuwa ba na san wata rana ma ba zan ganka ba"
"Am sorry ƙanwata, ai shiyasa nake so ki dawo Kano da zama, dan anan sai kin gaji dani"
"Kenan sai ina Kano zaka kula dani, kar fa naje ka karya min alƙawari"
"Ba zan karya ba, nafi so ki dawo Kano, ta yadda zan riƙa ganinki har sai kin gaji ma da ganina"
"Ka san mene?"
"Sai kin faɗa"

Shiru tayi na ɗan lokaci kafin ta ce "Ina son karatu, amma a raina nake jin ba zan yi ba"
"Meyasa kike faɗar haka?  Ki daina faɗa, za kiyi karatu har zuwa matakin da kike son ki kai a rayuwa"
"To shikenan, naji kuma na yarda da abinda ka faɗa kums na san za kayi, to amma da wace ƙafar zan yi karatu?"
"Sadiya..." Kallonshi tayi ba tare ta ce komai ba.
"Bana son ki riƙa karaya a al'amuran rayuwarki, duk abinda mai ƙafafu zai yi kema zakiyi Sadiya."
"Ba komai ba Yaya Habib" Ta saka hannu ta goge hawaye.
"Sarkin kuka zaki fara ko?" "Shikenan rayuwata a haka zata ƙare, ba zan cika buri ko ɗaya daga cikin burikan rayuwata ba." "Za ki cika, nayi miki alƙawarin zan kula dake, kuma zaki cika burinki"
"Taya ya?" Ta furta hawaye wanke a fuskarta. "Bani da ƙafafu, kuma bani da kowa a Kano, idan karatu zan yi waye zai kula dani? Wa zai kaini makaranta wa kuma zai dawo dani? Wa zai iya wahala dani akan kujera, kuma a garin nan babu wata babbar makaranta da zan yi, koda Wudil ce tayi min nisa daga nan, ba masu kuɗi bane mu da za a ce kullum za a sakano a mota a kaini kuma a dawo dani, ni gurgurwa ce ba zan iya yawo a motar haya ba, kuma Inna ba zata tsaya jiran in fito daha lecture ta dawo dani gida ba, bama In a ba ko Umma ce ba zata iya ba, n haƙura kawai da karatun, ni na san gaba ɗaya rayuwata ta gama lalacewa"
"Bata gama ba, kuma yanzu rayuwarki ta fara daidaituwa Sadiya, duk abubuwan da kika faɗa nine zan miki su"
"Taya kenan?"
"Ta hanyar aurenki, na san idan na aureki ina da kusanci dake, kuma zan miki duk abinda kike buƙata, in kaiki makaranta in kuma ɗauko ki, saɓanin yanzu da na san bani da wannan ikon. Za ki aure ni?"

Gabaɗaya ta fito da idanunta tana kallonshi. "Amsarki nake buƙata" Ya maimaita yana kallonta.

Zoben hannunta ta kalla, ta saka ɗayan  hannun ta riƙeta sai kuma ta sake fashewa da kuka tare da faɗin "A'a ba zai yuwu ba, zan cutar da kai ne"
"Saboda zoben hannunki shiyasa kike tsoron auren ko kuma ni ɓe baki so?"
Kai ta girgiza. "Tambayoyi biyu nayi miki amsa nake buƙata." Bata ce komai ba ta cigaba da shashsheƙar kuka.
"Idan har dan zoben dake hannunki ne na san labarin abinda ya faru, Baffa ya faɗa min komai akai, Sadiya ni ban damu da komai ba sai rayuwarki, ina son ganin rayuwarki tayi kyau, dan Allah ki bani dama"

Ajiyar zuciya kawai ta sauke, ita bama ta san me zata ce masa ba, kawai dai ta ɗaga kai ne, dan bata iya soyayya ba bata san mene soyayya ba, dan ko lokacin tana secondary school 'yan class ɗinsu masu soyayya kawai haushi suke bata, tana ganin suna ɓata lokacin su ne. Ta dai san dole watarana ita ma zata yi soyayya ta kuma yi aure amma ita bama ta san ta ba, Habib ne mutum na farko daya fara cewa yana sonta, a kuma yadda take a cikin damuwa bata san amsar da zata bashi ba illa ta amince dan cikar burinta. Batayi tunanin kalmar so daya furta mata zata wullata duniyar tunani har ma taji tana kewarsa ko kuma tana son ganinsa, sai dai abin mamakin shi ne a wannan ranar kasa baccin kirki tayi, kawai Habib taji ya faɗo cikin duniyarta, shekara sha shidda bata taɓa tunanin a wannan ƙarancin shekarun nata zata faɗa duniyar soyayya.

Ko da dare bayan ta gama cin tuwon dare da Inna tayi, sun sha waya da Habib domin ƙaramar wayarsa ya bata, kuma ya mata alƙawarin zai kawo mata babba idan zai dawo. Sim ɗin sa wanda baya amfani dashi sosai shi ya saka mata a cikin wayar.

...BASHI!Where stories live. Discover now