*...BASHI!*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_*K.W.A*
_Sadiya S. Adam🌸✍️_
*Afuwan nace inda mai buƙatar a saka masa talla, so masu turo talla ina rejecting kuyi haƙuri, gaskiya ba zan iya ɗora doguwar talla ba, wata ma har tayi rabin page ɗin😂 Guntattakin ba dogon rubutu ba, so na janye.*
*_Wannan shafin sadaukarwa ne ga mabiya wannan labarin._🥰*
Page 28
__________🖌️Bata sake magana ba har sai da Mommy ta ƙaraso gurin. "Yaya kai ne ka koma haka?" Ta faɗa tana ƙare mashi kallo. "Muhasin" Mommy ta faɗa da raunanniyar murya tare da rungumeshi.
*Bayan wasu mintuna*
Fa'iza na zaune a gefen gadon, Mommy kuma na daga tsaye, an sakawa Muhasin drip har ma ya samu barci. Ajiyar zuciya ta sauje tare da faɗin "Fa'iza muje parlour" Kallon shi Fa'iza ta sake yi sannan ta juya ta miƙe ta bi bayan Mommy. Suna zama a parlour Mommy ta kalleta ta ce "Fa'iza bana so ki faɗawa Muhasin komai game da Aziza, ko ya tambaya kice masa ta tafi Dubai saro kaya"
"Amma ko nan gaba ai zai sani Mommy"
"Eh na san zai sani, amma ba yanzu ba, a barshi ya ɗan huta na kwana biyu tukun"
"To shikenan, ba matsala"****** ****** ******
"Ban amince ki koma gidanta ba" Ya faɗa yana driving, ita kuma Janan tana bayan motar a zaune. Ɗan ɓata rai tayi bata sake cewa komai ba.
"Wato har kin ji haushi dan nace karki koma gidan Aziza da zama"
"Ni ba haushi naji ba" Ta faɗa kanta yana kallon titi.Ya ɗan juya ya kalli Janan sannan ya ce "Ƙanwata kina jin rigimar yarinyar nan, taya zan bari taje inda na san za ayi min snatching"
"Ban ga laifinka ba Yaya Habib nima na faɗa mata taƙi ji, matar da bata santa ba har tayi saurin yarda da ita har haka"
"Ki rabu da ita tayi fushinta ta gama amma ba zan yarda taje ba"Ita dai Sadiya bata ƙra magana ba har suka ƙarasa gidan su Habib, shi ya sauka ya buɗe gate, sannan ya dawo ya shigar da mota, sai daya koma rufe gate ita kuma ta fito, Janan ma ta fito.
"Nifa gabana faɗuwa yake"
"Ki nutsu babu abinda zai faru sai alkhairi"
"Amma amma me kike tunani da ta ce tana son ganina, ni wallahi tun jiyan nake tunani amma na kasa samun tsayayyar amsa"
Janan bata samu yin magana ba saboda ganin Habib ɗin ya taho."Ku mu shiga ciki" Shi ya yi gaba su kuma suna biye dashi.
Tunda suka shiga Sadiya ke bin ɗakin da kallo tamkar na amarya, ga daddaɗan turaren wuta da ƙamshinsa ke tashi. Ɓangare guda kuma faɗuwar gaba yana ƙara yawaita a ƙirjinta. Ya shiga kiran Maman tashi amma a cikinsu babu wanda ya iya magana.Tana fitowa Sadiya tayi ƙasa da sauri, ganin hakane ya saka Janan itama ta sauka ƙasan. Har sai da Mama ta zauna sannan suka gaisheta, Sadiya sam ta kasa kallok fuskarta, Janan ce ma take ɗan satar
kallonta.
"Ku koma kan kujera ku zauna" Mama ta faɗa tana nuna masu kujerar da hannu.
A kunyace suka zauna, Sadiya ta fara wasa da ytsun hannunta."Wacece Sadiyar a cikinku" Ji tayi gabanta ya faɗi, Janan ta nunata tare da cewa "Gata nan"
"Kece matar auren kenan, amma ba kama"
"Mam..." "Rufa min baki Habib ko in saɓa maka, da kayi tunanin na kirata ne dan in ji daɗi, to na kirata ne dan in mata gargaɗi" Sadiya ji tayi ƙwalla ta zo mata, amma tayi ƙoƙarin hanata zubowa, Janan kanta ta kasa ƙwaƙwƙwaran motsi bare shi Habib da ya fara dana sanin kawota gidan tun a yanzu."Dama a ƙauye aka san asirin, dan na fara tunanin sun asirce min kai" "Mama ni babu wanda ya yi min asiri, kawai ina sonta ne, kuma har cikin raina" "Habib ni zaka yiwa rashin kunya akan mace?" Shiru ya yi yana huci, ransa a matuƙar ɓace yake. Ita kuma ta kalli Sadiya ta ce "To duba kiga abinda kika aikata, kin dai gani ɗana yana son guduna a kanki. Wai ma me kika masa? Ya baki ƙoda? Ya kula dake lokacin kina gurguwa sannan kuma a yanzu da yaji da aure a kanki ya kasa haƙura jira yake wancan ya dawo ya sakeki shi ya aura, wannan aikin hankaline? Kin bi kin juya kan ɗana ya susuce a kanki, wallahi ji nake na tsaneki sosai, ni ban ga abin so ake ba" Ta ɗan yi shiru sai kuma ta cigaba da cewa "Akwai zaratan mata a family ɗinmu wanda babu abinda zaki nuna masu amma ya dage sai ke. Dama cewa nayi a kiraki na ganki naga uwar mene a tattare dake da har ya so ki? Ashe dai babu komai, sai tsagwaron talauci da idanu kamar na mayu" Jin haka ne ya saka Sadiya ɗago manyan idanun nata wanda suka zama jajir ta kalli Mama. Sai kuma ta ɗauke ido ta miƙe. "Janan...mu..tafi" Ta furta muryarta a sarƙe. "Umma ta gaida Assha amma ki sani zamanki surukata abu ne da zai baƙanta miki, kamar yadda ba zan taɓa ƙaunarki ba, saboda ba da son raina za a auro ki ba" Bata ce komai ba, ta fuzgi hannun Janan a fusace ta fita.

YOU ARE READING
...BASHI!
Historical FictionFyaɗe aka yi miki. Shi ne abinda zuciyarta ke ƙara nanatawa. Ban san waye ba, ban kuma san dalilinsa na aikata haka a gareni ba, ni a sanina bani da wani abokin hamayya, bani da izgili kuma bana wulaƙanta kowa, to waye ya yi min fyaɗe? Kuma mene...