28

1.3K 45 20
                                    

💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

         ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣8️⃣

Ba karamin batama su Nura lokaci akayi ba, shi yana zaune bayan kanta kaman criminal, Alhaji Musa da Lawyer shi ke shiga da fita, ganin yanda suke da kudi aikuwa sun tatsu a hannun yan sanda dan kusan 650k suka kashe wanda duka Alhaji Musa yabiya daga pocket nashi, sannan aka sallamesu Nura yayi signing a some files haka sannan suka baro wajen sukai sallama da Lawyer Nura suka wuce, Alhaji Musa ke tuki bini bini yana kallon Nura, ganin baya iya magana ma yasa yace "nakira Maman Humaira tana gidan tareda su Aman da Amali tun dazu, koda school bus yakawo su already tana gidan" gyadamai kai Nura yayi ahankali, juyarda kanshi yayi yana kallon titi bayako kyafta idanu sunyi nisa sosai ahankali yace "Musa park the car please" parking motan Musa yayi yace "lpy"? Ahankali Nura yacemai "ina zuwa" bude motan yayi yafita yafara tafiya zuwa gefen titi, saida yadanyi nisa sai kawai ya tsugunna yabawa titi baya, Musa dake kallonshi ta cikin mota Nura ya bala'in bashi tausayi dan Nura is hurt da yanda Hadiza ta makashi a kotu dakuma mishi shairi, da wulakanta shi datayi, badadan lawyer shi ba da har handcuff za'a samai a hannu fa, he's heart broken sosai.

Wayanshi daya bari kan kujera ne yahau ruri hakan yasa ya kalli screen din ganin Hajiya ne yasa yadauki wayan tareda saukowa daga mota yawuce inda yake aduke yadafash tareda bashi wayan yace "koma mota kayi waya da Hajiya ita ke kira, bari na shiga super market din chan nasamo mana ruwa, ba ruwa a motan da dan abinci bamuci komiba tun safe" karban wayan Nura yayi yawuce mota tareda zama abaya shikuma Alhaji Musa yawuce super market.

Daukan wayan Nura yayi kafinma yayi magana yaji unsettle muryan Hajiya tace "Nura I've been calling you tun dazu wayanka baya shiga kana ina" cikeda dauriya gudun kada ta gane komi yace "inda nake ba network ne Hajiya" dan shiru Hajiya tayi jin muryanshi kafin tace "kanin yaron nan dake neman auren Meena yakira yayanshi yake fadi yaganka a kotu matarka takawo karanka shi yana aiki a Admin office ne kaman ku wai dayagani da Meena yasa yakira yayanshi, what is happening Nura? Kaine aka gani a kotu"? Dan lumshe idanu Nura yayi wato babu abinda yakai bad news spreading, jin yakasa magana yasa cikeda damuwa sosai Hajiya tace "what happen talk to me Nura, kasan how worried sick nake kuwa tun dazu nake kira waya ka baya shiga, meke faruwa Nurudeen"? In a very weak voice yace "Hajiya Hadiza takai karana kotu sabida na mareta shekaran jiya......." Da kyar dai ya iya bama Hajiya labarin sama sama, Hajiya tai shiru kaman wacce ruwa ya cinye tanajin muryanshi dake breaking sosai, ance tsakanin d'a da uwa sai Allah dudda he's trying to show her he's fine but she could feel pain din danta piercing through every organ na jikinta, she feel yanda voice nashi is so weak, shaking with lots of sorrow atattare dashi, cikin dauriya da kokarin so tabashi karfi dakuma tsananin so irin wacce mahaifiya kema danta tace "are you okay yanzu? Kun gama zancen kotun? Hope babu abinda ya sameka? Did anybody hurt you Nura? Tell me wani abu yasameka kun gama da kotun, are you fine Son?" Hajiya ya jeromai tambayoyin cikeda damuwa, da tausayi dakuma matukar son danta, baki Nura yabude zaiyi magana sai yaji abu ya tokaremai wuya, dagewa yayi cikin karfin hali irin na maza zaiyi magana yakasa sai hawaye sharrrr, duk yanda yaso ya danne kukan yakasa abinda he can't remember the last time yayi arayuwanshi sai kawai kukan yashiga flowing, cikin murya mai bala'in rauni da bata nuna kaman mutum na kuka but at the same time kuka yake yace "Hajiya I don't know why all this is happening to me?" Yadanyi shiru cus muryanshi na rawa kukan dayake yazama so obvious yace "Hajiya Hadiza hurt me deeply, she crushed my ego today, laifine dan na sota? Hadizan danai soyayya da ita harna aura was a hardworking obedient wife, muna dawowa Abuja ta chanza, I put up with every attitude nata cus idan akwai soyayya dole akwai sacrifice da hakuri da juriya, she did so many mistakes ina yafemata and overlook nama manta something like that ever happened, all because of one slap Hajiya wanda in all this years da muna tare ban taba mata ba can't she forgive me, I am human Hajiya, I get angry too, banfi karfin kofsawaba haka banfi karfin aikata kuskure ba babu abinda fushi baya sawa, but sabida a single slap ta makani a kotu tabatamin suna batare datayi tunani how this action will affect me ba, or my children, Hajiya mata yakamata tazama mai rufawa mijinta asiri, idan yamata kuskure ta rufamai asiri, tanuna min cewa ita ba matan da zata iya rufamin asiri bane and bata damu da self respect dina ba, I love Hadiza alot, I've done all I could but tunda abin yakai ga haka gwara na hakura da ita for good!" Hajiya jitayi kaman tayi kuka sabida yanda taji Nura is seriously crying, bazata iya tuna the last time da Nura yayi kuka ba maybe tun yana primary school, Nura grew up as a strong hardworking man, baida magana, ita badadan tazo Abujan nan sabida ciwon taba batasan kalan rayuwan dayakeyi da iyalinshi ba, ko sunzo kano babban salla Hadiza bata zama gidanta gidan su take zuwa to ta ina zata gane wani kalan rayuwa suke ciki? Nura ba gayamata zaiyiba, banda hakama is not proper tasa kanta arayuwan gidanshi, datazo Abuja taga zamansu saisa dayazo mata da maganan auren Ummi bata hanashi ba, saisa take sonshi da Ummi dantaga itane yarinyar dazai iya tankwarawa dan ayanda taga Hadiza wlh wlh tafi karfin danta, babu yanda zatayi ne dan yana sonta amman babu mahaifiyar da zataso taga mata na ganama danta azaban da Hadiza kewa danta, tun ranan farko data shigo Abuja taga kallan zaman dasuke ta dage sosai da yima danta addu'a kan Allah yakawo mai karshen wahalan nan, idan aurensu akwai alkhairi to Allah  ya daidaitasu idan babu Allah yakawo musu mafita su biyun. Anatse dakuma soft tone ganin danta is weak tace "Nura bazan maka karyaba auren ku dakai da Hadiza has become toxic, the space will do the two of good, burina shine Allah ya zaba maka abinda yafi maka alkhairi, Allah ya takaita muku wahala, ka kawomin yaran nan kano gobe" kaman maraya Nura yace "tohh" Hajiya jitayi zatamai kuka tadai daure no one can understand the pain of a mother idan taga danta na wahala, Nura is suffering sosai cus yanason Hadiza, Hadiza kuma ta maida Nuran kaman abokin fadanta, Nura yabata tausayi sosai daurewa kawai tayi hatası ta fashe da kuka damuwan takaramai yawa, ahankali tace "kazo kano gobe Ummi na nan wajena" dasauri cikin muryan da ba karfi har lokacin yace "eh"? Ahankali Hajiya tace "Ummi na gidana bataje kauyensu ba" lumshe idanu Nura yayi ahankali saikuma yabudesu baice komiba, Hajiya tace "you will get true this Nura, duk abinda bai ragazaka ba will only make u stronger, rayuwa yagaji haka, Allah ya kyauta ina kuma yima Hadiza fatan shiriya, Allah ya shiryata, Allah ya ganar da ita, sai kazo gobe kaji, Allah tamaka albarka Allah ya rage maka zafin dakakeji azuciyanka, May Allah grant you comfort my Son" ahankali Nura yace "Ameen Hajiya" Ahankali tace "kagama da kotun gabaki daya yanzu?" Gyadamata kai yayi yace "eh ina tareda Alhaji Musa ne zamu tafi gida" Ahankali Hajiya tace "to kuje gidan first I will call u later, don't forget ka kira mahaifin Hadiza koka turamai sakon message" gyadama Hajiya kai yayi ya katse wayan yashiga aikama Mahaifin Hadiza message dan baijin zai iyamai magana yanzu ba.

MATAN?? KO MAZAN???Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora