eleven

98 7 0
                                    

*GENERAL NASEER ZAKI*
(When a Soldier falls in love...)

Top-Notch...season 03
Arewabooks: Azizat

                           Page 011


"Three, two, one, Action"

Director na faɗin Action sabuwar jarumar ta fara magana tana farfari da ido cikin camera. Wannan farfari da yanga-yanga da take yawan yi shi ya sa mutane ke sonta.

Jaruma Munira Bawa da ake kira da MoBaby tun a film ɗinta na farko da ta kira kanta da MoBaby tana tsaka da ɗaukar shirin film ɗinta na bakwai kenan a cikin wata uku.

Jarumar ta shigo masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood da sa'a dan kuwa tun a film ɗinta na farko da ta yi da jarumi Ali Nuhu mai suna MUNIRA tauraruwarta ta fara haskawa a duniyar film.
Sai ga shi tun daga film ɗin Munira Directoci da yawa suka fara rige-rigen saka Munira Bawa a film ɗinsu.

Munira Bawa 'yar Asalin jahar Kano ce amma tashin Lagos. Wannan yasa ko lokacin da ta shigo Kannywood ta zama daban a cikin sauran jarumai mata.
Na farko kasancewar ta yi Sakandare mai kyau a can Lagos sai ya kasance tana ɗan jin turanci, dan ko a film ɗinta na farko Munira ɗan turancin da ta ke sakewa lokaci zuwa lokaci shi yasa mutane suka ji suna sonta. Haka nan directors ke ganin tana da wata dama da wasu jaruman basu da shi.
Na biyu kasancewarta tashin Kudu sai ya kasance babu irin kayan da bata iya sakawa.
Ko da producer bai ware kuɗin kaya ba za ta sako ƙananan kaya ta saka gashin wig ta fito a film tana ƙwalisa babu ruwanta.

A shekarar 2002 da 'yan Izala ke ta wa'azi suna ƙorafe-ƙorafe akan masana'antar film ɗin ba kowacce jaruma ba ce ke iya saka irin kayan da Munira MoBaby ke sakawa.

Daraja ta uku da ta ɗaga MoBaby tun shigarta  film industry shine iya rawarta. Ta taso tun tana yarinya take son kallace-kallacen fina-finan India wanda yai tasiri a rayuwarta ya saka mata sha'awar shiga film tun ma bata kammala sakandare ba.
Idan tana kallon films ɗin Indiyawa ba abinda ta ke kwaikwayo sai yadda matansu ke rawa suna kwarkwasa.
Lokacin da ta fara film mutane suka ga yadda take rawa sai aka fara dangantata da Madhuri dixit ɗin Kannywood saboda iya rawarta, wasu kuma su ce mata Aishwariya Rai. Manyan mutane da suka taso suna kallon fina finan Indiyawa na 80's kuma suke dangantata da jaruma Hema Malini.

Kafin MoBaby ta yi film goma har sunanta ya shahara ya fara fin na tsofin jaruman da ta zo ta tarar a masana'antar.

Ba zaka ce MoBaby tana da kyau na shiga rai ba amma tsantsan iya kwalliya da kwarkwasa shi yake jawo hankalin mutane gareta su ke ganin tana da tsananin kyau. Bata cika shekara bama a masana'antar ta ɗan fara shafa mai dan ta ƙarawa fatarta haske duk dama ita ɗin ba baƙa ba ce, tana da hasken fatar da a turanci ake cewa caramel skin.

Jarumi Ali Nuhu da ke tashe a duniyar film ɗin Hausa shi ya kawo MoBaby cikin masana'antar. Mijin yayarta da Ali Nuhu abokai ne na ƙut da ƙut. Wani zuwanta hutu daga Lagos zuwa Kano lokacin tana SS2  ta haɗu da Ali Nuhu a gidan. Tun daga lokacin ta sanar da shi tana sha'awar shiga film ya ce mata ta bari ta kammala karatunta tukunna. Ai kuwa tana gama zana jarrabawar WAEC ta niƙo garinta ta taho Kano ta bar iyayenta a can Lagos.
Duk da mahaifinta ya so ta cigaba da karatu ita kam ta shafawa fiskarta toka akan film za ta yi ba karatu ba, koda zata cigaba da karatu sai a gaba.
Gashi yanzu ta ji daɗin yadda tauraruwarta ke haskawa ta ajiye maganar karatu ta kama sana'ar film haiƙan.

***

*2003, Ekiti State*

Cikin shigarsa ta khakin sojoji ya fito daga ɗaki ya kalli ƙaramin falonsa wayam babu komai a saman center table da ke falon. Yau ma haka zai fita ba tareda ya yi breakfast ba. Gaskiya dole ne ya je ya taho da Fatima. Zaman gauro da yake a wannan garin ya ishe shi.
Ya shiga kitchen ya duba flask ɗin ruwan zafi ko tea ne ya haɗa ya sha kafin ya fita amma babu ruwan zafin a ciki. Yai tsaki ya fito daga kitchen ɗin ya ɗau brief case ɗinsa da keys ya fito.

Second Lieutenant N. M. Zaki kenan, soja ma'abocin tsayi da kaurin jiki.
Yana fitowa ya haɗu da maƙocinsa Christopher ya fito riƙe da ƙaramin kwando da aka saka masa kular abinci. Wannan ya sake tunzura Naseer ya ji cewa dole ne wannan karan ya taho da Fatima ko tana so ko bata so.
Dama tunda aka tura shi garin Ekiti da ya nuna yana so ya taho da ita ta fara masa ƙorafin idan ta tafi za a bar Iya Abu cikin kaɗaici sai ya haƙura. Shima dai rashin sanin yanayin garin ya sa bai takura mata akan dole sai sun taho tare ba.

Kamar yadda yai niyya da ya samu sarari ya je gida ya ce da Iya zai taho da Fatima. Bata hana shi ba amma tace ya bari a yi bikin Hauwa'u tukunna tunda bikin ya yi kusa. Da haka dai ya haƙura ya sake dawowa babu matarsa.

Ƙarshen shekara da ya je bikin ƙanwarsa Hauwa'u ya taho da matarsa da ɗansa.
Ita kam Hauwa'u bokon dai bai yiwu ba dan samarin da take tarawa ma ba zasu barta ta yi karatun ba. Tun data sake zana paper bata ci ba ta watsar da maganar karatun ta rungumi ɗinki. Alhamdulillah lokacin da Ogarta ta mata freedom ta ƙware sosai a iya ɗinki.
Naseer ya kashe mata kuɗi sosai a bikinta ya kuma siya mata keken ɗinki akan idan ta je can gidan mijinta a Bauchi sai ta fara sana'ar ɗinki a can.

Ita kuwa Aminatu bayan ta gama Health Tech Ningi sai ta sake samun gurbin karatu a BUK ita ko maganar aure bata yi ta sa a ranta sai ta cimma burinta na zama ƙwarriyar Likita.

Koda Naseer ya taho da Fatima Ekiti gaba ɗaya zaman barrack yai mata banbaraƙwai. Ta fara kewar su Iya saboda kaɗaici.
Ita dama tun can ba mai son hayaniya ba ce, ga shi barrack ɗin yawanci Yarabawa sun fi yawa.
In dai Naseer ya fita to tana gida ita da ɗanta tana kallo ko karatun novels wanda ta taho da su tun daga Azare.
Cikin matan maƙotansu wata Bahaushiya bakatsiniya ce Maman Iklimah kawai su ke ɗan magana, ita ma ba sosai ba.

Abinka da aikin Soja ko wata shida bata kai ba a garin aka sake yiwa Naseer transfer zuwa Ondo. Haka suka sake ɗunguma suka wuce barrack ɗin Akure.
Da suka je ta fara ji ina ma a Azaren kawai ya barta ya ke zuwa mata duk sanda ya samu dama. Har ta ɗan fara sabawa da mutanen Ekiti kuma sai ga shi sun dawo Akure.

Lokacin da Naseer ya samu ƙarin rank zuwa matsayin First Lieutenant sai aka sake tura shi jihar Calabar. Wannan karan kam sai da Fatima ta koma Azare ta ga 'yan'uwa sannan wani zuwansa hutu ya ɗauketa suka wuce Calabar. Ita dai wannan tashi-tashin da suke ya fi komai bata wahala. Sai ta ɗan fara sabawa da waje sai a sake tura shi wani wajen.
To ya za ta yi. Ita fa ke auran Soja.
Hatta Al'amin abin sai da ya shafe shi. An sa shi makaranta a Akure ya ɗan fara kama karatu aka sake tisa ƙeyarsa zuwa wata makarantar a nan Calabar...

*ko kun hango abinda na hango?*
*ga Munira MoBaby ga Kyauta Ngwatam🤔*


***

Top-Notch season 3 wannan karan sun zo muku da daɗaɗan labarai guda uku.

NAZNEEN...exquisitely beautiful (Mai Dambu).
BINTUN BATUL (Shatuu).
GENERAL NASEER ZAKI (Azizat)

Za ku samu labarai ukun ta whatsapp a farashin 1300
Ɗaya #500
Biyu #900

Ku tuntuɓe ni ta whatsapp 08137311900.

*Account Details*

0008219237
Jaiz Bank
Azizat Hamza
08137311900

Ko kuma ku bibiyesu a manhajar Arewabooks.

@ Azizat
@Shatuuu095
@maidambu41












GENERAL NASEER  ZAKI (Book 1)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora