*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_Page 10
"Bab...baiwar Allah wace ce? Ban gane ki ba?" Ta faɗa cikin sarƙewar harshe.
Daga ɗayan ɓangaren kuma cikin jin zafi aka ce "Ba sai na tsaya ja miki aji ba Zeenat dan baki kai wannan matsayi ba; Rafi'a ce, kuma ke baki isa nayi gasa dake akan muradina, dan haka ba shawara nake baki ba, umarni ne kan ki rabu da Irfan ko kuma ki ga abinda zai biyo baya."
Jin haka ya saka Zeenat murmushi tare da faɗin "To ai ba ni za ki kira kiyiwa warning ba, shi ya kamata ki kira dan shi ne ya ganni ya ce yana so bani nace ina son shi."
"Kardai ki nemi ki faɗa min magana dan wallahi zamu iya kwasar 'yan kallo"
"Ni bani da lokacin wannan, akan me zan yi faɗa bayan nice naci wasan, ina dai miki fatan samun wanda ya fi shi"
Tana gama faɗar haka ta katse kiran tare da jan tsaki.Zama tayi a tsakar gida, abubuwa duk sun jagule mata, ga maganar da Irfan ya yi akan virgin, ga Nabiha ta sako ta gaba, sannan daga gefe guda ga kuma Rafi'a ta kunno kai.
**** **** ****
"Gidan zan je Mammy" Ta faɗa tana goge hawaye. Cikin rarrashi Mammy ta ce "Haba Princess ai ba girmanki bane, wallahi kin fi ƙarfin faɗa da talakawan nan, ki kwantar da hankalinki auren nan insha Allah ba za a yi ba, ba dai mahaifinki ya faɗa wa mahaifinsa cewar ɗan shaye-shaye ne Idin kuma ga Caca sannan ita kanta Zeenatu tayi ciwon hauka, na san uba nagari dai ba zai aurawa ɗanshi irin wannan ahalin ba."
"Mammy kar fa ki manta Daddyn Irfan ba bahaushe bane, taya kike tunanin har zai yarda da irin wannan maganganun; su in dai 'ya'yansu na son abu suna basu ne no matter what"
"Nice nace miki kar ki damu na san abin yi, amma kar ki je gidan wannan matsiyatan" Kai kawai ta gyaɗa sannan ta tashi ta fita.Kai tsaye ɗakinta ta koma, tana shiga ta dokawa Diana kira, har ta kusa katsewa ta ɗaga "Na gode Diana, ashe cin amanar har ya kai haka?"
"Haba Princess me nayi miki"
"Munafurci..."
"Ke Rafy dakata, kar ki yarda ki jefeni da wannan mummunar kalma"
"Amma ai kin san Brother ɗinki na soyayya da cousin ɗina shi ne ko ki faɗa min sai kawai gani nayi a status ɗinshi."
"To me kike so na faɗa miki bayan ba ƙaunarsu kuke ba, kuna wulaƙantasu saboda su talakawa ne, bayan ku ba dabararku da wayonku ne ya baku arziqin ba"
"Oh hakan ne ya baki damar haɗata da wanda nake so? Kenan kin yi ne dan ki ƙuntata min"
"Ban da abinda zan iya domin ance matar mutum kabarinsa"
"Lallai Diana I never expect this from you"
"Hmm! Rafi'a kenan da alama har yanzu baki san rayuwa da abinda ke cikinta ba"
"Ni kuma nayi alƙawarin zan nuna miki rayuwa da kuma yadda take, zan tabbatar miki da bana taɓa rabuwa da abinda nake so sai na samu, duk runtsi"
"Ba zaki iya raba soyayyar data riga ta daɗe da kafuwa ba"
"Babu ta inda zaki iya hana faruwar hakan, ke dai mu zuba mu gani" Kashe wayar kawai tayi tare da fashewa da kuka.Wani irin so take yiwa Irfan wanda bata san lokacin da ya yi mata shigar sauri ba, duk tarin samarin da take dasu wasunsu har wulaƙantasu take, amma kuma Irfan da take bege sai ga shi ya ƙi saurarenta, bai taɓa bari sun keɓe ko sau ɗaya ba duk da tana yawan faɗa masa tana so suyi magana su biyu kaɗai, amma koda yaushe uzuri yake bata, ashe ba ta ita yake ba, dame Zeenat ta fita?
Hannu ta saka ta sake goge hawayen takaici tare da alwashi kala-kala akan Zeenat.**** **** ****
Auwal ya taimaka masa ya tashi, sannan ya karɓi crutches ɗinsa "Wai ina zuwa haka?"
"Gurin Zeenat mana, yau sati na ɗaya da dawowa garin nan, amma kun hanani naje gareta, kuma itama ban ganta ba"
"Ai ina ganin da ka bari ka ƙara warwarewa"
"Zan warware a hankali Auwal ina dai so naje na faɗa mata irin nasarar da aka samu"
"To ka bari Mama ta dawo mana"
Murmushi Mustapha ya yi sannan ya ce "Mama za ta raka ni wurin Zeenat ne?"
Shiru Auwal ya yi sam baya son abokin nashi yaje ga Zeenat sannan kuma baya so ya faɗa masa cewar saura sati ɗaya bikinta, ga Mama bata nan bare ta hana.

YOU ARE READING
RAINA FANSA(Complete)
Historical FictionƘaddara ta kan zo wa mutum ba tare daya shirya mata ba, wala mai kyau wala akasinta, sai dai Zeenat ita ta yakicowa kanta mummunar ƙaddarar da mayar da ita rabi mutum rabi dabba. Ablah musaka ce, tana da dogayen hannuwa sai dai dungulmi ne, ma'ana b...