Page 37

130 6 3
                                    

*ℝ𝔸𝕀ℕ𝔸 𝔽𝔸ℕ𝕊𝔸*
   𝙱𝚢 𝚂𝚊𝚍𝚒𝚢𝚊 𝚂 𝙰𝚍𝚊𝚖
𝚆𝚊𝚝𝚝𝚙𝚊𝚍@𝚂𝚊𝙽𝚊𝚣_𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑
𝙰𝚛𝚎𝚠𝚊𝚋𝚘𝚘𝚔𝚜@𝚜𝚊𝚗𝚊𝚣𝚍𝚎𝚎𝚢𝚊𝚑

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[karamci tushen mu'amula tagari]_

Page 37

Idanunta a lumshe tana cije leɓe ya shigo ɗakin. "Sannu" Ya furta tare da samun gefen gado ya zauna. "Kin ga yadda na faɗa dai ɗaurin gida yafi ko, amma kika dage ke na asibiti kike so, da na gida aka miki ba lallai ya riƙa miki wannan zugin ba."
"Ni ban yadda dana gida bane, na shiga uku Abban yara wai daga gurɗewa shi kenan sai karaya"
"Tsautsayi ne idan yazo ba yadda ka iya"
"Hakane"
"Allah ya sawwaƙe ya kuma baki lafiya"
"Amin ya rabbi"

Turo ƙofar aka yi, Hamdiyya ce ta shigo. Sai data gaishe su sannan ta kalli Mustapha.
"Ya akai?"
"Abba Muktar ne" Sai kuma tayi shiru ta fashe da kuka.
"Me Muktar ɗin ya yi?" Nabiha ta faɗa cikin tashin hankali.
"Mami" Sai kuma ta fashe da kuka. Da sauri ta miƙe ta bar gurin.
"Abban yara dan Allah ka kira min ita naji mene yake faruwa, mun shiga uku"
"Ki kwantar da hankalinki ba lafiya ne dake ba kuma kina ƙoƙarin ɗaga hankalinki"
"Kana ganin fa yadda ta fara magana kuma ta katse wai mene hakan"
"Bari inje in jiyo ko mene amma ni na san ba matsala insha Allah" Tana kallonsa ya wuce gabaɗaya hankalinta a tashe yake.

A parlour ya tarar da Hamdiyya kwance kan kujera tana kuka. "Hamdiyya" Ya kira sunanta tare da zama kan kujerar da take. Tashi  tayi tana goge hawaye kanta a ƙasa.
"Mene ya haɗaku da Muktar ɗin?"
"Abba ya faɗa min cewa shi ya zauna ya yi tunani gaskiya ba zai iya aurena ba saboda wai kar ya kwshi cuta"
"Waye ya faɗa masa kina da cuta? Naga har test an miki amma babu"
"Abba kawai sharrin mutane ne, saboda abinda ya faru dani, yanzu ma ya ce zuwa gobe zai turo a amsar masa kayanshi"
"Ya ilahi. Kin ga share hawayen sannan ki daina ɗaga hankalinki komai da kika ga ya samu bawa muƙaddari ne, kuma zan yi mabana da Muktar ɗin" Kai ta gyaɗa tana zubda hawaye.

Duk yadda Mustapha yaso ya ga Muktar abin ya faskara, kuma kamar yadda Hamdiyya ta masa bayani hakan ce ta faru, dan da safe aka turo mata su karɓi lefe, hatta mahaifinsa sai daya so ya samu zama dashi amma suka ce a'a ayi haƙuri kawai, Allah ya zaɓa mata wani nagarin. Ɗan ƙaramin hauka Hamdiyya tayi musu a gidan tana faɗin Mami ce taja mata data dage sai ta auri Muktar, bayan Ablah ya fara gani yana so. Kullum cikin kuka da damuwa take, ga Nabiha a zaune da karaya babu damar ta tashi, su Haidar da Aslam ne suke rarrashinta, sai Mustapha daya kasa samun nutsuwa ko a kasuwa.

                     ***** *****

Da mamaki Mommy take kallonta har lokacin data kai aya.
"Diana, anya kina ganin maganar nan gaskiya ce, idan har a ranar da aka ɗaura aure ya ɗauketa zuwa gidanshi taya za a ce daga yi sau ɗaya har ta samu ciki?"
"Mommy idan ma ba 'yar shi bace DNA test za ta fayyace komai, amma mun yi magana da Fahad ya ce min yarinyar tana kama sosai da Irfan, kuma lokacin tana jinya anan akwai ranar daya taɓa shigo mana a gigice  ya ce kansa na tsananin ciwo ai a ranar ya faɗa mana yaga mai kama dashi kuma tana kama dani, har kika ce hakan zata iya faruwa tunda dole za a iya samun mai kamarshi"
"Hakane, to kenan yarinyar shi ce?"
"Ba mamaki Mommy"
"To yanzu taya zamu faɗa masa?"

Miƙewa Diana tayi ta koma jikin mirrow ta tsaya. "Mommy mun sani bayan rasuwar Yaya da kwana ɗaya rak aka ga kabarinshi ya tsage, aka sanarwa da Daddy yaje aka haƙa kabarin aka kuma fito dashi yana motsi, daga nan Daddy ya roƙi da a rufe abin har zuwa lokacin da zai samu lafiya, duk da cewar Daddy ya yi ƙaurin suna a garin nan amma kuɗin daya bawa maigadin maƙabarta da wanda suka haƙa kabarin ya saka kowa yaja baki ya yi shiru aka cigaba da zaman makoki, duk da tun a lokacin ya dace ace an sanarwa da Zeenat saboda tana da haƙƙi a kansa tunda an riga an ɗaura aure, Mommy duk da cewar Daddy ba bahaushe bane amma yana zaune a ƙasar hausa kuma shi musulmi ne, Mommy ba a yiwa Zeenat adalci ba" Ta saka hannu tana goge hawaye.

RAINA FANSA(Complete)Where stories live. Discover now