JALLI JOGA

8 0 0
                                    

JALLI JOGA

            NA

     MAMAN AFRAH
First Class Writers Ass.
  
  HAƊAKA PLACE GROUP
Wannan ƙungiyar masu posting ce ba ta marubuta ba.
  
  Assalamu Alaikum
Ina sanar da masoyana makaranta littattafaina, cewar WHATSAPP sun  dakatar (Banned)  accaunt ɗin number ta da kuka sanni da ita wato *09030283375* yanzu da wannan nake amfani *09013181851      Ni ce dai na ɗishaɗantar da ku a *ƳAR ZAMAN* *WANKA* na sanya ku dariya a *ƘARA'IN INNA* *DELU* yanzu na dawo muku da sabo mai abin dariya *JALLI JOGA*

  FUA Hijjabs and More
We deals with jilbas, Egyptian jilbab,hoodie hijjab,normal hijjab and More.
Location:Zaria kaduna state and gumel jigawa State.
Contact address:08065777095

         Page 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣

  Jin ya ce za a rufe mata ɗuwawu ta daina tusar ma bare wani kashi, da sauri ta ɗauke hannunta ɗaya daga dafe ƙasa da ta yi. Miƙa hannun ta yi bayanta daitin ƙofar da tusar ke fitowa  ta saka tafin hannun nata ta toshe ƙofar dan ta san idan har aka ce ta daina tusa da kashi ai babu lafiya yo ina za ta saka ranta a ce ka daina tusa da kashi ai ta san to kuwa akwai gagarumar matsala bare kuma a ce aljannu ne za su toshe maka ɗuwawu to a ina ma za a gansu bare a ce su buɗe to tabbas dole ta yi iya yinta dan ganin ta yi yaƙi da usjar tusar da take fitowa tana ƙoƙarin mata shamaki da yin kashi ma gabaɗaya wanda ta san ko likitoci ba lallai su iya ɓarke toshiyar da aljannun za su yi sai dai ta haƙura da yin tusa da kashi, idan kuwa haka ta kasance to tabbas ko abinci sai dai ta haƙura da ci tun da babu inda za a kasayar da shi.

" Yallaɓsi ai ita tusar da kanta ta yi kaɗan ta ci ƙarya ta kwana da yunwa ta ƙara ƙetara umarninka tajawarka lafiya ai na done kafar da tusar takw fitowa babu yadda ma za a yi ta kufce ta fito.

"Da dai ya fi tsohuwa mai rangwangwan, ga ki da tsoron jinsin aljannu kamar farar kura amma kuma kina fitowa tsakiyar dare lokacun da rundunar mu suke fitowa dan zuwa gidan biki da zuwa kasuwa ku kuma lokacin bil adama duk kuna bacci amma saboda kankanba kika fito, to yanzu da ke za mu shiga kogon kukar nan a yi shagalin bikin ɗan ƙundalo da ke"

  Ɓiriɓiiiiiit Ƙaran wata tusar da iskarta  ta zarce a kan hannun da Inna ta toshe ta fito abinta sariri dan ƙaran har ya fi na sauran tusosin da ta ɓurɓurka ɗazu.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, amma ke kuwa tusa mai ya kai ki wannan ɗanyan aiki an ce ki daina fitowa su yallaɓai basa son jinki amma kika fito gaba yo ai sai ki bari idan na koma gidan Yaya Lado na shiga ɗaki sai ki yi ta keto hazo kina fitowa haba amma dan jan jafa'i za ki...

"Ai kin zo kenan a nan za a sama miji a haɗa shagalin bikinki da na ɗan ƙundalo a kai ki can birnin sin"

"Wallahi matar aure ce ni, Uwani ce matar Malam Ashiru mai almajirai na unguwar tudun tsira" Cewar Inna tana sakin kuka mai sauti.

"Yanzu kuma za ki samu cigaba ki auri Sarkin aljannu kin ga kin tashi daga matar bil adama Malam za ki koma matar mutanen ɓoye a mutanen ɓoyen ma.

" Wayyo Allah ni Uwani yau cuta ta ɗakko cuta akuya ta ɗakko akwatin miciji, dan Allah ku mini rai ku barni a jinsina wallahi ina da jikata marainiya bata da uwa bata da uba Lami ni kaɗai take da ni"

"To kin ci sa'a amma yanzu za ki mana adungure bakwai kafin ki tafi" Ya faɗa yana sauka daga bayan Innar.
 
  Wani irin sagewa bayan Inna ya yi har ƙara ta ji ƙashin bayanta ya yi.


"An gama indai adungure ce amma a caɓalin nan zan yi?"

"To ko na kwanta ki yi a kaina?"

"Ni shegiya Uwani wace ni, ƙaryata ta sha ƙarya" Ta faɗa tana wani bashi girma. Bai ce komai ba dan har lokacin ma ya kasa tsayuwa da ƙafafunsa dan kayan mayen basu saka shi ba.

JALLI JOGAWhere stories live. Discover now