23

6 2 0
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 23
©Fadila Ibrahim

GIDAN DAURAWA ESTATE
Sashen Baaba Huraira.

Kamar wacce aka yi ma raɗa mun koma gidan Abhi da kwana biyu, na shirya tsab na tafi gidan su Baaba Huraira, dama ban taɓa zuwa ba, ni da Riya muka je gidan.

Muna zuwa kuwa muka iske Aunty Lubabatu tazo wajan Ƴar uwar ta, Tun wancen ranar da naga Umma naji Matar ta shiga rai na, amma sai na rasa dalilin jin nauyin matar, mun same su suna breakfast ne daman, muma aka bamu kuma muka ci....daga bisani muka ji suna tattaunawa akan zasu gyara ɗakin Umma Asma'u wanda ta bari lokacin tana budurwa.

Cikin madaidaicin sashen nasu ita da Aunty lubabatu, dama kowa da Ɗakin sa, ɗakin da ya kasance ɗakin da aka rufe da kwaɗo/padlock tsahon shekara da shekaru, shi aka buɗe mata, komai na ɗakin yana nan a ma'ajiyar sa akwai ban ɗaki babba a ciki, Yana da kura sun cika ɗakin, da taimakon Riya da Aunty Lubabatu dani kai na muka yi ɗammara muka fara gyara ɗakin.

Aka wanke labulaye, Masu aikin Baaba Huraira suka wanke carpet, daga bisani na bar su suna aiki ni kuma na shiga kitchen ɗin Baaba Huraira na fara kiciniyar ɗaura girki, wanda dama masu aiki ne suke dafa mata abinci, ba wani tsufa tayi ba duk da takai shekarun Inna. amma ciwon zuciyar da take da shi ne ya sa ba komai take yi ba.

Dambu nayi niyan yi.....Zan fara aiki ne sai ga Inna ta shigo ita da Riya, Riya tace min,"Inna ta ce na kawo ta wajan ki wai"

Nayi murmushi ina ɗaura apron na bata kujera ta zauna, na ce ma Riya zata iya tafiya.

Da blender na barza shinkafa, Baaba Huraira ta fitomin da busasshen zogale, Inna ta gyara mun tana ta min hira har da cewa, ""ni na rasa wannan wani irin abu ne, banga jikana ba, Asma'u tace Jikana yana nan garin, amma tun da muka zo yau kwana uku ban sa jikana a ido ba"

Na ce,"Umma Asma'u tana da yara ne daman? "Ta ce,"Eh mana yaro babba ma, ya baki shekaru da yawa ma"

Na gyaɗa kai ina zumbure baki, alamar uhmm lallai ta jima da aure kenan.....Na cigaba da aiki na nayi madambaci sannan na haɗa nayi aiki na a hankali mai aiki ɗaya ce take taimaka min da miko kaza ɗauko min kaza har na gama haɗawa, sannan na haɗa kunun aya, mai garɗi da daɗi, na ɗura a gora na sanya su a freezer sannan na koma ɗakin wanda tuni sun gama gyarawa abubuwan da aka wanke suna waje suna shan rana, duk dama lokacin damuna ne ba kasafai rana ke fitowa ba.

"Inna ta ce,"Gaskiya girkin nan sai kamshi yake yi" ban taɓa jin Dambu yana kamshi haka ba, Asma'u bata mana mai kamshi.....Inna ta faɗa tana siɗe ludayi tana cewa ga kunun ayan ma yayi daɗi. "Kina da aure ne ƴan mata?

Nayi dariya ina girgiza kai....sai ta ce,"Zaki auri Jikana ki rinka dafa masa abinci mai daɗi irin wannan, Amma fa shi talaka ne bawan Allah, baya da kuɗi"

Daidai lokacin Umma Asma'u ta shigo tana cewa, "Sannun ku da aiki Inna"

Inna ta ce, "Ni fa kar ki ɓata min rai Asma'u, eheeen a zaune kika ganni ba a tsaye ba, ga mai aiki nan tana jinki"

Na juya abu na na cigaba da aiki na, don na rasa dalilin da yasa nake jin nauyin Umma....Umma kam ta abin da tazo ɗauka ta tafi saboda yanzu Inna zata fara balbalin masifar ta.

Na zuba a manya manyan warmers na silver aka kai su palon Baaba Huraira, ana muka je muka ba je bayan kowa yayi sallah, muka ci muka hantse, muka sha kunun aya, ina jin yadda suke yaba girki na, da kunun ayan kuma kowa yana warwaso wai wallahi basu taɓa shan kunun aya ma daɗin wannan ba.

Sai dare Abhi yazo shi da Ammi na, suka kwashe mu ni da Riya muka koma gida, sai da na je naga Grandpa ɗina na kai masa Dambun dana ajiye masa, Inna mune na harara ta, shi kuma yana dariya yana cewa,"Lallai Kakar ki da gaske kishi take dake"

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now