31

13 2 0
                                    

AL'ADARMU🏇
Page 31
©FADILA IBRAHIM

ABHI yayi gyaran murya sannan ya cigaba da cewa," *AYMAN yana da damar auran mata biyu, tsakanin ke da Khausar*

Sosai zuciya ta take bugu, jin maganar Abhi ta karshe, *kishi da khausar kuma*, meyasa khausar ta shiga rayuwa ta ne haka, munyi sharing Uba, sannan kuma har da Miji........dafe goshi na nayi ina jin wani yanayi mara misaltuwa, jiki na yana min babu daɗi.....Da taimakon Ammi naje ɗaki ta kwantar dani saman gado, ta jima zaune a gefe na tana kare min kallo, daga bisani ta min dai da safe ta bar ni cikin damuwa.

Hakanan ranar na yini a ɗaki rayuwa tayimin tsanani, har su Inna mune suka bar gidan namu.

Abhi ne ya shigo ya same zaune ina kallon wani series Amaya a laptop ɗina, ya zauna a gefen gado ya ɗaura hannayen sa akan nawa ya kirawo sunanaa.

"ANAM"

Abhi ya rike min hannuwa na gadagam, ya cigaba da cewa,"Anam ba zan yi abin da zan cutar da ke ba, amma zan so ki hakura da Ayman na zuwa wani lokaci wata kila ba rabon ki bane, saboda idan na cigaba da cewa ba zai iya auran nan ba yadda na fara faɗa musu tun jiya to zamu iya samun matsala da su, sannan idan na hana daga baya kuma aji labarin Ayman zai aure ki to ban san yaya mutane zasu kalli abin ba, ke ƴa ta ce shiyasa nake lallaɓa ki, yau idan khausar ce a halin da kike ciki shima zan iya lallaɓa ta ke ki aure shi....Duk da soyayyar da nake miki bai kai wanda nake yi ma Khausar ba, amma matsayin dana ɗauka na uba akan khausar shiyasa ba zan iya hanata abu ke kuma na ɗauka na baki saboda son zuciya ba, daga ni har ke zamuyi hakuri mu bar wa Allah lamarin sa, bamu san daidai ba.

Anam kiyi hakuri kinji, ki kara hakuri,........Murmushi na saki na kwanta a jikin Abhi ɗina ina zubar da wasu zafafan hawaye masu zafi, daga bisani ya tashi ya fita yana min sallama da fatan alkhairi, Yana fita waya ta tana kara, Ayman ne amma ban iya ɗagawa ba.....kasancewar karfe 4 ne na yamma, duniya ta yi min zafi tashi nayi na bar gidan kai tsaye Restaurants ɗina na nufa, babu kowa saboda ko sati ba'ayi ba dana kulle resto ɗin.

*****
"Ayman ya naga kana ta packing kayan mu, ina kuma zamu je ne? Umma ke tambaya fuskar ta cike da mamaki ganin Ayman ya shigo ranshi a ɓace yana kwashe musu kayan su yana ce su tashi zasu koma zaria.

"Umma na faɗa miki zaria zamu tafi a yau yau ɗinnan," Ya karasa ya kai duban sa ga Inna ya cigaba da cewa" Ban taɓa tsammanin haka gidan Daurawa suke da son zuciya ba, da son kan su sai yanzu, ban kuma taɓa tsammanin za'a chusa min akidar da zuciya da gangan jiki na basu aminta da shi ba"

Tuni Ayman ya gama jera kayan su Umma tsab a akwati, ya kai su bakin kofa ya dawo ya samu daga Umma har Inna suna zaune suna bin sa da idanu, Inna ta ce,"Wai shin kan ka kalau kuwa Ayman tafiya zaria ba shiri kamar ana koran mu"

Idanuwan sa sun canza launi daga fari kal zuwa ja ja alamar hawaye sun taru, kallo ɗaya Umma ta kara yi masa ta hango damuwar da ke damun ɗan nata, amma wannan wacce irin damuwa ce haka, a hankali ta isa wajan Ayman ta kamo hannun sa ta zaunar da shi saman wata kujera ta zauna a kasa ta zuba mishi idanu......tsahon dakika goma yayin da hawayen sa ɗigo ɗaya ya zuba a tafukan hannun Umma, hakan ya sake tabbatar mata da cewa Ayman ɗin ta na cikin damuwa.

Inna tana ta salati tana tafa hannuwa,"Aymanu wa ya taɓa min kai, aradu in ɗauko takobi na na wasa shi mu shiga fili....billahillazi sai na rama maka"

Ta faɗa tana karasowa in da suke, hannun ta rike da kananan wukaken nan wanda ake anfani dasu a kitchen, tayi tsaye kaman wata dogari...Tsabar takaici yasa Umma tayi shiru tana....daga bisani ta ce da Ayman, "Babu in da zamu je, kira min Abhi yanzu nan"

Babu musu haka ya kirawo Abhi ya bata sukayi magana...bayan ta kashe wayar ta ce,"Yanzu Abhi zai zo zanji komai daga gare sa, so please ka dakata da haɗa kayan nan mu jira shi ya karaso.

Tamkar mara lafiya haka yake jin sa, tuna hukuncin da suka yanke akan sa abin yayi masa babu daɗi ko kaɗan, ta yaya suke tsammanin zai iya yin rayuwa da wacce ko ɗigo ɗaya na soyayya babu, babu kamar sa cikin zuciyar shi.......Idan kuwa suka takura mishi to wallahi zasu neme shi su rasa , ya sani ma babu ta in da zasu uzzura ma Umma akan wannan maganar, Domin Umma na goyon bayan sa akan komai, kuma bata yadda taga anyi zalunci a gaban ta ba....don wallahi wannan zalunci ne da son kai, wai su Al'ada.

Da wannan yanayin ya jiyo sallamar Abhi.....jin Umma da Abhi sun fara maganar ya sa kai ya fice daga gidan Baba Huraira.

Kiran duniya yayi wa Anam amma bata ɗaga wayar ba, yaje gida bai same ta ba Riya tace mishi ai ta fita, amma tana kyautata zaton babu in da Anam za taje face Restaurants ɗin ta.

******
Kwance take saman cinyar Inna mune babu abin da take sai shagwaɓa da kananan koke koke, Inna mune tace,"Haɓa Khausar sau nawa zan faɗa miki ki kwantar da hankalin ki, In Sha Allah tun da muka tsaida magana ɗaya to babu makawa sai ya tabbata"

"Inna wallahi kallon da Yaya Ayman yamin ne ɗazu ya tsorata ni"

"Tsoro kuma? Yo dama ba soyayya kukeyi da shi ba, taya zai miki kallon da zai tsorata ki Khausar"

"Uhmmm "Inna ba zaki gane bane, amma wallahi da so samu ne ku gaggauta ɗaura mana auran nan, saboda akwai ƴan hassada fa Inna"

"Su waye mahassadan, ke khausar ban hana ki irin waɗan nan maganganun ba" Mummy khausar ta faɗa a yayain da take saukowa daga kan matakalar da zai sada ka da sashen Grandpa.(Baban sulaiman) ta karaso wajan Inna tanɓ zauna tana mai hura iska ta ce,"Inna na fahimci Ayman baya son Khausar ana chusa masa soyayya da aure ne, kuma a tunani na ban taɓa tsammanin zaku bi bayan karya ba saboda soyayyar jikar ku, koda yake ma kece kike goyon bayan ta Inna......kuma wallahi.......

"Dakata Salima, ke kika haife ni ko nina haife ki?

Mummy khausar tayi shiru, jin Inna zata mai da martani....Inna ta cigaba da cewa,"Ba goyon baya ba, in ma akwai abin da yafi goyon baya ma zan mara ma jikata baya, ke ba ƴar ki bace, baki son kiga tayi aure ne, kaf dangi akwai nustsassen mutum kamar Sulaiman ne, kwanan sa nawa a shigowa amma ba muga saurayi mai hankali kamar sa ba....don haka Khausar ta fito ta nuna shi zata aura, kuma naga lan uwan ta ne, so banga dalilin da zai sa wasu su nuna basa so ba, Aure kam ko ana muzuru ana shaho sai anyi.

Mummy khausar ta ji haushin maganar Inna, amma babu yadda ta iya hakan yasa ta zare wa khausar idanuwa tace,"Dan ubanki manya na  magana kina zaune kina bin kowa da ido, mu sa'an ki ne.....Zaki tashi ko sai na zo na daka ki a wajan".....Mummy ta faɗa tana mai niyar tashi, tuni Khausar ta bar falon da gudu.

Inna mune ta ce,"Ha ahn, Ha ahn miye haka kuma Salima bana so fa, ki dena takura mata, ni kam zo ki koma gidan ki, kuma ki turo min Zakariyyah( wato mahaifin Khausar), anjima ya zo ina son ganin sa akan maganar.

Mummy Khausar ta sabi gyalen ta tana cewa,"Dama sakon kayan ki na kawo miki, sai na tadda wannan al'amarin, da ban zo ba Inna da baza ku sanar dani ba kenan sai kun gama yanke hukunci?

"Taya za'a sanar da ke, ke ta fara samu da maganar kika hanata fitar da abin da ke cikin ranta, yanzu ta same ni ta faɗa min, kuma zan share mata hawaye"

"Allah ya baku hakuri Inna, bari naje gida"

"Allah ya bamu alheri".

©FADILA IBRAHIM

AL'ADARMU ✔Where stories live. Discover now