Page 1

13 2 2
                                    


HAREES~

PAGE 1

      Babban waje ne a tsare da kayan motsa jiki wato "Gym center" mata da suke ciki kowacce ta mayar da hankali kan abinda take ,a hankali ta turo kofar glass door din ta shigo kai tsaye ta nufi inda ta hango macen da ke tsaye sanye da ba'kin kayan sport sun bi jikinta  duk wanda ya kalleta  sai ya sake so ya  kalleta ya kuma kallonta sabida kyawun sura ,hips dinta ya fito sosai kamar zana mata akai haka kirjinta a cike .Murmushi tayi ganin yarinyar da ta karaso gunta  ta rungumeta da sauri.

  A shagwabe ta turo baki "Mommy yunwa".Ta fad'a tana sauke hand bag dinta ,sanye take cikin uniform na makaranta farin shirt sai skirt dark blue da V shape hijab gajere.Gira ta dage wacce ta kira da mommyn tace.
 
  "Baki jin ko kunyar mutanen gunnan ,ji be ki sangama ba ki ci lunch dinki ba yau ma bayarwa kikai kenan?"

    Ba tace komai ba don kuwa haka din ne ta girgiza kai "Nikam ba zaki sani girki ba daga nan saloon zanje ,sai dai mu yi takeaway ".

"Mommy pizza"Ta fad'a  wacce ta kira da Mommyn ta girgiza kai.

  "Kayan kwalama ,no pounded yam ma za a saya".

Kamar zatayi kuka ta turbune fuska wanda ya sa Mommyn murmushi.

  "Oya zan siya Amma sai kin ci abinci sosai".

"Yes Mommyna".

  Abaya ta sanya kafin suka fito ta ciro key din motarta tana Bude kofa itama ta shiga suka dauki hanya.

  
~~~~~

Kwance take tana daddanawa waye ya shigo d'akin ,tayi suarin gyara kwanciyarta tana me rage hasken wayar ta Yi wani shuumin murmushi.

"Alhajina ina ta jiranka na shiga kewa sosai".

  Baki ya washe yana me yaye babbar rigarsa irin zabgegen mutum ne ga cikar jiki katoto ne Alhaji Aminu kenan mai dolar babban dan kasuwa kuma shahararre a 'kasar Nigeria.Tasowa tayi tana mai kifa wayar bayan ta rubutun sako "Ya fa dawo ,muyi magana anjima".

_ "Zanyi kewa ,har na ji kishi bye love"_ Aka rubuto da chat din da tayi saving JK
  
   Tana kwarkwasa ta 'karaso gun shi ta dora hannunta a kafadunsa zuwa wuya tayi fari da ido "Sweet pie ganinka kadai ya buwaye duhun da ya lullube ni na kewarka zakina abin alfahari yau nayi maka tana di"Ta karshe magana tana kashe ido.

Ya washe hakoransa yana cakumota ta fad'a jikinsa "Sarauniya abar kaunata na kosa na ga wannan tanadin".

  "Ga fili ga mai doki...."Ta furta tana masa wani shuumin murmushi.

   "Ehihihi saura sukuwa hajiyata".Ya furta da wata siririyar kucakar dariya cikin zuciyarta wani haushi ya rufeta dashi ba abinda ta tsana sama da wannan washe bakin a fili kuwa ta murmusa tana taune lips ta juya tana rausayawa ya bi bayanta da kallo kamar dolo ya bita.....

   ~~~~~

      Babban d'akine ne mai dauke da kayan alatu tsaddadu masu duhu ,tsaye yake jikin madubin yana cire agogon hannunsa wayar da ke kan drawer ce tayi vibration ya duba sunan da ke kan wayar.

   "Aisha"

    Cigaba da abinda yake yayi har ta katse kafin wani kiran ya sake shigowa yayi picking a handsfree ya Saka.

  "Hello".Aka furta daga wancen bangaren.

  Bai ce komai ba ,aka sake fadin "Please kayi hakuri don Allah wlh bansan haka zata faru ba gidane suka min kiran gaggawa amma next time zan sanar maka kafin na tafi dan Allah".Ta furta cikin siririyar muryarta mai nuni da tayi nadama.

 
    "Sorry for yourself in kin gama bani hakurin ki kashe Ina da abin yi".

  "My boss pleassss".

HAREES Where stories live. Discover now