ƳA KO JIKA

0 0 0
                                    

*ƳA KO JIKA?*

Page 2

*SAFNAH ALIYU JAWABI (HIS NOOR)*🥰

*PERFECT WRITERS ASSOCIATION*

Follow the PERFECT WRITERS ASSOCIATION channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vad1bE05a249vbEcab0r

'''Ga link nan na kungiyar mu  mai suna Perfect writers ku shiga domin samun sabbi da kuma tsofaffin littatafan mu.

Ku kasance a tare damu lallai ba za kuyi da kun sani ba.'''

Ƙarfe goma da mintuna na safe aka kira wayar Alhaji Mamman Bukar aka sanar da shi 'ya'yansa sun yi haɗari a mota. Hankali a tashe suka nufi asibiti shi da Hajiya.
Wani ƙarin tashin hankalin da ya ziyarce shi wanda yake fatan da ma mafarki yake yi shi ne, wani saƙon kar-ta-kwana da ya shigo wayarsa cewa: 'Ba lallai ne ka yarda ba idan na ce ɗiyarka tana safarar ƙwayoyi ba; amma ka duba ma'ajiyar kaya na motarka.'  Ko da yake dai ya ji maganar tamkar almara, amma da ya tuna mutum ba ya ƙin ta mutane, in ji ɓarawo da aka ce ya gudu, sai ya tashi da sauri da nufin ya je garejin da aka kai gyaran motar tasa. Hajiya tana ta yi masa magana, amma ina, wanda ya yi nisa wai aka ce ba ya jin kira!

A ɓangaren Hajiya kuwa tana da yaƙinin duk abin da zai koro ɓera daga rami, ya faɗa wuta, tabbas ya fi wutar zafi. Lallai ba lafiya ba! Babu yadda za a yi idan lafiya ya bar 'ya'yan nasu a asibiti cikin mawuyacin hali, ya tafi har tana masa magana bai ko kula ta ba. Tana so ta bi shi don ta san abin da ke faruwa ko ta samu nutsuwa a ruhinta, sai dai ba za ta iya barin 'ya'yanta a asibitin babu kulawar da ta dace ba, domin dai duk wani likita da zai yi ƙoƙarin ceto rayuwar 'ya'yanta da jini ke ambaliya a jikinsu ba kamar ita da ta haife su ba, tun da an ce kowa ya sha inuwar gemu bai yi ya maƙogoro ba!
Tana cikin ƙoƙarin shirya kayan aiki don ceto rayuwar 'ya'yanta sai saƙo ya shigo wayarta kamar haka: 'Ɗiyarki ta jawo wa mijinki masifa, domin safarar miyagun ƙwayoyi take yi da motarsa. Yanzu haka ana dab da kama shi a matsayin mai laifi.'
Dam! Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, gumi ya fara tsattsafo mata. Ɗaukar wayar tata ta yi, ta yi ta kiran lambarsa, sai dai ko sau ɗaya ba a amsa ba, tamkar an shuka dusa ana jiran ta yi fure. Sai daga baya wata malamar jinya ta kawo mata wayar tasa, ashe a asibitin ya manta wayar ya tafi.
*****
Ko da Alhaji Mamman Bukar ya isa gajerin, sai da ya tabbatar idanu ba sa kansa sannan ya buɗe boot ɗin motar a hankali. Ba ƙaramar kaɗawa hantar cikinsa ta yi ba da ya yi arba da abin da aka faɗa masa. Idan ya ce sai ya yi dogon bincike kafin ya gane hodar iblis idanunsa suke gani, tabbas ba shi da ƙwarewar aikinsa.
Baki a buɗe ya riƙe murfin ma'adanar motar; shi bai rufe ba, sannan kuma bai saki murfin ba. Tuni zuciyarsa da ya amince ba ta yaudararsa ta fara bijiro masa da wasu zantuka: 'Tabbas akwai lauje cikin naɗi, wannan ɗanyen aikin ba halin 'yata ba ne, 'yata mai ceto rayukan al'umma ce, ba mai cutar da su ba. Dole wasu ne suke so su shafa mata kashin kaji, su ɓata mata suna.'  Haka zuciyarsa ta yi ta jinjina lamarin tana mai matuƙar amincewa da 'yar tasa. Bai san adadin mintunan da ya ɓata yana karanta wasiƙar jaki ba, shi dai kawai ya san ya daɗe. A wannan daɗewar ne kuma kamar daga sama ya ji wata murya mai razanarwa.
"You are under arrest." Yana juyawa ya ga Jami'an Hukumar Yaƙi Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA. 'Ta faru ta ƙare, an yi wa mai dami ɗaya sata.'  Ya faɗa a zuciyarsa sannan ya bi su zuwa ofishinsu.Sosai Hajiya Jummai ta samu sassauci a zuciyarta da ta iske Amir bai samu rauni mai yawa ba, Amira ce dai take ta suma tana farfaɗowa.
To a daidai lokacin ne kuma ta samu labarin mummunan al'amarin da ya faru ga mijinta. Hankalinta a tashe ta bar asibitin ta nufi ofishin NDLEA, sai dai ba ta samu nasarar ganin sa ba, domin sun hana ta. Don haka ko da ta tuna da saƙon da ya shigo wayarta ɗazu, sai ta nufi gida ranta a ɓace ta je ta ɗauko wani littafi ta nufo asibitin sai huci take yi tamkar ƙadangaruwar da ta haɗiyi kunama.
Zuwanta asibiti ya yi daidai da fitowar Amir wanda ya yi ƙarfin hali duk da zugin da yake ji ya fito don ganin lafiyar ƙanwarsa.
Ganin mahaifiyarsa ta nufo wurin tana ta sauri sai ya tsaya yana jiran ta. Ko da ta zo sai ya ce:
"Umma ina aka kwantar da 'yar'uwata?"
"Wannan butulun ba 'yar’uwarka ba ce." Tana faɗar haka ta yi gaba ta bar shi tsumu-tsumu cikin mamaki. Jin maganar ya yi bambaraƙwai, wai namiji da suna Hajara. Lokaci ɗaya kuma ya fara zargin ta yiwu abin da ta faɗa daban kunnuwansa ne ba su ji daidai ba.
Amma saboda korar kokwanto sai ya bi ta a baya zuwa ɗakin da ta shiga wanda yake da yaƙinin a nan aka kwantar da Amira.
Lokacin da suka shiga ɗakin, Amira ta farka ko da yake dai cikin kallo ɗaya mutum zai lura da azabar da take ciki.
"Amira!" Hajiya ta kira sunanta cikin wani yanayi mai kama da tsawa.  Daga ita har yayan nata mamaki suke yi.
Ita kuwa ta cigaba da cewa: "Na yi nadamar ɗauko ki! Ashe da ma za ki saka mu a rana a lokacin da muka saka ki a inuwa? Ashe da ma lokacin da muke ƙoƙarin rufe asirinki ke burinki tona namu? Idan za ki yi safarar miyagun ƙwayoyi sai kin jefa mijina a musifa?"
Ko da yake tun da ta fara maganar babu wanda ya samu damar cewa komai, amma da ta zo wannan gaɓar sai Amir ya karɓe zancen da cewa:
"Umma duk fa abin da kike tunani ba haka yake ba. Idan ma laifi ne, ba 'yar'uwa ce ta aikata ita kaɗai ba...."
"Dakata!" Ta katse shi sannan ta ɗora: "Ba ka da wata 'yar'uwa mace, wannan da kake gani...."
Amira ta buɗe baki da ƙyar ta fara magana a hankali: "Umma me kike faɗa kamar....""Kul! Kar ki ƙara kira na Umma. Ni ba mahaifiyarki ba ce. Sannan mutumin da kike wa kallon mahaifi, shi ma bai da alaƙa da ke."
Tana faɗar haka ta jefa mata wani littafi sannan ta ɗora: "Da ma an ce tsintacciyar mage, ba ta mage. Wasiyyar da mahaifiyarki ta bari tana cikin wannan littafin."
Tana faɗar haka ta fice ta bar su cikin kogin mamaki. Shi dai Amir tun tasowarsa ya san Amira ƙanwarsa ce wadda ya girma da shekaru huɗu, haka ita ma iya abin da ta sani ke nan.
Cike da hawaye ta buɗe shafin farko na littafin suka fara karantawa tare kamr haka:

ƳA KO JIKA?Where stories live. Discover now