page 3

6 1 0
                                    

*ƳA KO JIKA?*

*SAFNAH ALIYU JAWABI (HIS NOOR)*🥰

*PERFECT WRITERS ASSOCIATION*

Follow the PERFECT WRITERS ASSOCIATION channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vad1bE05a249vbEcab0r

'''Ga link nan na kungiyar mu mai suna Perfect writers ku shiga domin samun sabbi da kuma tsofaffin littatafan mu.

Ku kasance a tare damu lallai ba za kuyi da kun sani ba.'''

'YA KO JIKA?
Wataƙila idan na ce: 'Na yanka wa kare ciyawa' labarin ya zamto abin mamaki. Idan kuwa na ƙarasa labarin da cewa,'Karen ya ci ciyawar da na yanka masa' mamaki ya rikiɗe zuwa takaici, ta yadda za a yi mini kallon wadda ta rasa hankalinta. Saboda da'awar da na zo da ita ta saɓa da lafiyayyen hankali. Ko da yake a yanzu ne da na dawo cikin hayyacina na gane haka, duk da dai na gane a ƙurarren lokaci, amma na san idan na rubuta tarihin rayuwata zai amfanar da al'umma domin dai an ce gani ga wane, ya ishi wane tsoron Allah."
Da wannan na fara rubuta wani al'amari da ya faru gare ni a daren wata ranar lahadi, a ɗaya daga wuraren shaƙatawar da nake ziyarta.
Kamar ko da yaushe, na zo joint ɗin misalin ƙarfe sha biyu saura na dare, na zauna tare da bayar da umarnin a haɗa mini shisha. Kafin a kawo mini tawa na lura da wasu samari da 'yammata da ke gefena waɗanda ko ba a faɗa ba, cikin kallo ɗaya na fahimci sun afka wata duniyar ta daban, sam ba sa cikin hayyacinsu. Nakan sha shisha sosai, amma ko kusa ba na haɗa ta da wasu kayan maye. Shi ya sa lokuta da dama nakan yi mamaki idan na ga wasu cikin maye, musamman mata.
Ban ƙara jin takaicin maye ba, sai yadda na ga ɗaya daga cikin 'yammatan ta gaza ɗaukar robar lemo, ta yi mata nauyi, shi ya sa duk sa'in da ta ɗauka sai ta suɓuce ta faɗi. Har dai ta haƙura ta tafi ta bar lemon da ta fara sha, lokacin da na ɗauko lemon don ganin abin da ke cikinsa, ya yi daidai da kawo mini tawa shishar. Don haka na ajiye robar lemon na durfafi abin da ya kawo ni.
Ban jima ina sha ba, sai kawai na ji kaina ya fara juyawa. Bugu da ƙari sai na ji a daidai wannan lokacin babu wani abu da nake so a duniya tamkar namiji ya kusance ni. To da dai na lura yanayin ƙaruwa yake yi, sai na yanke shawarar tafiya gida. Don haka na haɗa kayana na ɗauki jakata na nufi gida.
Abinku da tautsayi wanda akan ce ba ya wuce ranarsa. Lokacin da zan taho sai na ɗauko ragowar lemon nan na saka a jakata. Rashin sani ya fi dare duhu, da a ce na san ragowar lemon nan zai jefa ni a nadama ta har abada, da ban ɗauko shi ba.
Da ƙyar na samu na kawo kaina gida saboda mayen da nake ciki. Ko da na iso gida kuwa sai na yi cilli da jakar a falo, ni ma na faɗi, sarkin ɓarayi ya yi awon gaba da ni. Lokacin da na farka maye ya sake ni, sai na ji kamar na kashe kaina na huta saboda abin da na gani. Fasiƙanci na aikata da mahaifina!
Ashe asalin abin da ya faru shi ne, mai sayar da shisha ya saka mini flavour da ke tayar da sha'awa ne saboda ya yi amfani da wannan damar ya haike mini, to da na taho gida da lemon da na ɗauko a can ashe shi ma yana ɗauke da wasu ƙwayoyi masu cire mutum daga hayyacinsa. Shi kuwa mahaifina ya ɗauka ya sha, hakan kuma ya sa muka aikata mummunar ta'asa.
Mahaifina yana kuka ni ma ina yi. Na yi ta tuno yadda mahaifiyata ke ta samun saɓani da shi a kan yadda yake sangarta ni, nake fita lokacin da na so na dawo lokacin da na so, shi kuwa yana nuna mata ai yarinta ce wata rana zan daina. Har dai a ƙarshe silata aurensu ya samu matsala, ya sake ta.
****

Bayan wasu watanni na haifi jaririya mace, wadda a wurina na kasa gane ɗiya ce, ko ƙanwa? Kamar yadda mahaifina ba na jin zai iya gane ɗiyarsa ce, ko kuwa jika?
Zuciyar mahaifiyata ta yi matuƙar raunin da ta gaza ɗaukar wannan lamari, ta kamu da matsanancin ciwon zuciya. Yayin da mahaifina kuwa ya yi layar zana, sama ko ƙasa aka neme shi aka rasa.
Hakan ya haifar mini da matsananciyar cutar damuwa (depression) ta yadda sai da aka kai ni rehabilitation center domin na rasa yadda zan yi na dawo da nutsuwa tare da walwala kan fuskata. Ko da yake kafin a kai ni na ba wa nurse amanar ɗiyata. Duk da haka damuwa ta kasa barina. Da larurar mahaifiyata da ke kwance a asibiti rai a hannun Allah zan ji, ko kuwa da ɓacewar mahaifina, ko kuma da tunanin amsar da zan ba wa ɗiyata a lokacin da za ta girma ta tambaye ni wane ne babanta? To ba ma wannan ba, shin yaya zan fuskanci fushin Ubangijina a lokacin da na isa gare shi?
Na san da yawan mutane irina muna ɗaukar shisha ba kayan maye ba ce; ko da a ce haka ne, ya dace a ƙaurace mata domin dai tana zubar da mutunci, har ma a yi wa duk wani mai tu'ammali da ita kallon ɗan shaye-shaye kamar dai yadda wannan azal ɗin ta afka mini silarta. Babu mamaki kuma idan aka yi bincike a kimiyance a gano hayaƙinta yana yi wa huhu illa kamar yadda na cigari yake yi.
Abin da ya faru da ni a iya cewa kuskure ne ko ganganci. Bayan ƙwaƙwalwata ta samu waraka daga ciwon damuwar da ya yi silar zamana a cibiyar lura da masu matsalar da ta danganci ƙwaƙwalwa wato rehabilitation centre kuma duk a dalilin ɗabi'ata ta shan shisha ne na fahimci haka. Ko ma dai mene ne, bayan da na dawo hayyacina na zaɓi na rubuta shi saboda ya zama darasi ga wasu."
Suna zuwa ƙarshen labarin suka fashe da kuka. Sun jima suna kuka an rasa wanda zai rarrashi wani. A haka Hajiya Jummai ta shigo ta same su, don haka Amira ta share hawayen da ke fuskarta duk da dai hakan bai hana wani sake fitowa ba ta ce:
"Umma na gode da kulawarku, kuma babu ɗaya a cikin ahalinku da za a hukunta da wannan laifin. Laifi nawa ne ni kaɗai kuma zan karɓi duk hukuncin da ke biye da shi.
Amir ne ya dakatar da ita sannan ya sanar da Umma komai a kan yadda suka fara wannan baƙin kasuwancin, da ta lura ashe ma ɗanta ne ya ɗora Amirar a kan karkataccen layi amma duk da haka ta amince za ta karɓi hukunci ita kaɗai, sai tausayinta ya kama ta.
"Umma, ina mahaifiyata take?" Amira ta tambaye ta, tana kuka.
Ita ma Umma kuka take yi sannan ta ce: "Lokacin da ta haife ki, ni ce malamar asibitin da ta ba wa amanarki. Kuma bayan ta dawo hayyacinta sai ajali ya ritsa ta, kafin rasuwarta ta bayar da wannan littafin a ba ki."
Ana cikin haka wata malamar asibiti ta shigo hannunta ɗauke da wata takarda sannan ta miƙa wa Hajiya ta ce dattijon da suka yi haɗari da 'ya'yanki ya rasu, kuma ya bayar da wannan takardar a ba ki. Ko da ta buɗe sai ta ga gajeren rubutu ya yi kamar haka:
"Na saurari duka tattaunawarku, a cikinta na gane ni ne mahaifin Amira da ya ɓata. Ina roƙon ta yafe mini don Allah."
****

Ranar litinin jami'an tsaro suka gurfanar da Alhaji Mamman Bukar a kotu bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi, inda a ƙarshe 'ya'yansa suka zo a matsayin shaidu, suka sanar da dukkanin ta'asar da suke aikatawa ba tare da saninsa ba.
Ko da yake Hajiya Jummai ta ji daɗin yadda aka wanke nagartaccen mijinta, sai dai daga ita har shi babu wanda ya bar kotun da walwala a fuskarsa domin an yanke wa 'ya'yansu hukunci daidai da laifukansu.

Ƙarshe !

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 26 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ƳA KO JIKA?Where stories live. Discover now