Page 40

2.2K 143 53
                                    

Ustaz ya sauke numfashi mai huci ji yake kamar ya buɗe baki ya kurma ihu tare da kabbara ga Ubangiji, amma abinda ya ke ji ya danne duka wannan yanayin ya fi gaban ihu, balle magana domin ji yake kamar wutar lantarki ke jan shi tana fisgarsa tunda Umma ta haife shi har kawo yanzu bai taɓa jin abu makamancin haka ba.

Tun daren jiya har wayewar gari sabo yake jin kansa, yana ta son furta ko kalma ɗaya ne,amma idan ya kalli Ridayya da abinda ta bashi sai ya ji duk abinda zai faɗa ya yi kaɗan, Ridayyansa ta fi karfin hakan. Ya sauke numfashi a karo na babu adadi ya juya a hankali ya zuba idanunsa akan ta, ta kwaɓe fuska busassun hawaye duk a fuskar saman idanunta ya kumbura sosai.

Ganin tana ɗan firgita ya saka shi miƙa hannunsa zuwa wuyanta ya ji zafi sosai. Ba ki ya buɗe zai yi magana maimakon furta abinda ya yi niyya sai furucinsa ya zauya zuwa.

“Allahu Akbar, Ma sha Allah walihamdulillahi wallahu Akbar. Allahamdulillahi godiya ga uwar mataye, godiya ga baƙar mace godiya ga Ustaza data amshi budurcin Muhammad Bilal ta mai da shi mijin aure na sunna”

Sarai Ridayya ta ji shi amma ta yi shiru, wani irin kunyarsa ta fara ji,nauyinsa da kimarsa sun ninku fiye da kima a zuciyarta da idanunta. Ta sha wahala ƙwarai a wajan Zameer idan har zai yi tarayya irin haka da ita sai ya shaƙe mata wuya, kafin yanzu gabaɗaya shatin yatsunsa ne a wuyanta wani lokaci har hijira numfashinta ke tafiya. Bata taɓa jin wani abu ki sani wani abu wai shi emotions or feelings ba sai a daren jiya.

Abbiey ɗinta ya nuna mata mene duniyar soyayya da rayuwar auratayya ya bambance mata ƙauna da biyan buƙatar kai da kai, bata cikin haiyacinta amma ta ji muryarsa a jiyan bayan faruwar komai yana tambayar ta a hankali daidai kunnenta yana shafa kanta.

"Are You okay with me?
Kin gamsu or do you need more? Are u happy with me? Is there any problem with? Or am not romantic man, banda kunya Ustaza rayuwarmu ce wannan"

Sanda yake furta hakan ji ta yi kamar ta nutse, ta ko'ina Ustaz ya sha bambam bai yi son kai ba, bayan ya nutsu da ita yake tambayar ko ta gamsu saɓanin wasu mazan kansu kawai suka sani da son samu biyan buƙata shikenan.

He is so lovely! Her world.

Ya kasa fita daga ɗakin dukda yunwar dake damunsa ainun tsoro yake ko ya yi mata wani, kar Ustaza ta yi fushi da shi shi kam ya bi Allah da Manzonsa kuma ya bi Ridayya sau da ƙafa.

Motsin yatsun ƙafarta da suke riƙe a hannunsa ya ji, yana juya ta yi saurin rufe idanu daga kallon bayansa ya girgiza kai shi a duniya yanzu bai san mene bai sani ba don gane da ita idan har baccin ƙarya take yana ganewa.

Ya matse yatsun tare da girgiza ƙafar sai ta fashe da kukan ƙarya tana murza idanunta.

"Wayyo Baffa zai cire mini ƙafa, Auchiii"

"Sharri Ustaza"

Ya furta a hankali kuma a nutse yana matsawa daidai kanta inda take kukan wiwi. Ya dinga kallonta can ya ce

"Ki gasa jikinki"

Ta tattare duka duvet ɗin a jikinta ta fara ƙoƙarin sauka ya riƙe ta marairaice ta ce "Uhm ta ba zan wankan ba"

Ya sake ta yana ƙoƙarin tashi ta yi saurin shigewa toilet dukda ciwon da kwankwasonta ke yi mata hatta ƙirjinta a zabar zafi yake. Bayan ta shiga Ustaz ya tattare gadon ya gyara ya fito mata da wata blue ɗin riga iya qiwwa mai sauƙin nauyi a jiki. Fita ya yi zuwa sashinsa sai a lokacin ya ji gajiya ta saukar masa ainun shi kansa nasa kwankwason ciwo yake he wonder why? Maybe don ta amshi budurcinsa ne.

Wanka ya yi sosai ya shirya cikin English wear black colour suka ƙara fidda hasken fatarsa irin ta larabawa hannunsa rigar half damtsensa ya fito sosai wandon iya qiwwarsa gargasar jikinsa har ta yi yawa amma tai wa fatarsa kyau sosai da gaske ta yi kwance luf luf ya samu kansa da ɗaukan turaren daya siyo for the first time a rayuwarsa, ya dinga kallon turaren na  ROJA DOVE AOUD a hankali ya dinga fesawa har su ƙasan wuyansa bayan kunne gashi kamshin na musamman ne, sai a lokacin yake duba price ɗin turaren lallai ya kashe kuɗi. Ya tattare sumarsa zuwa baya a karo na farko ya saka abu ya ɗaure dukda haka sai da wata ta kwanta gaban goshinsa ya dinga sakin murmushi shi kaɗai gabaɗaya wankansa na Ridayya yau. Ya kalli kansa sosai.

MUNAFUKIN MIJIHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin