Ƙoƙarin tashi Ridayya ta yi cikin sauri a nutse kuma Ustaz ya damƙe hannunta yana ƙara kame fuska saboda saukar muryar Mardiyya da ya ji.
Ta cikin wayar Diyya ta ƙara cewa "Baby na yi kewarka sosai na yi kewar mijina, ya kamata ka dawo tunda mayyar data na ce maka ka sake ta, kuma kai ma ka tabbatar mini baka son ta" da mamaki Ustaz yake jin furucin na Mardiyya ya lumshe idanunta zuciyarsa na matsewa yana jin yadda hannun Ridayya ke rawa wanda yake da tabbacin ba iya hannun bane hatta zuciyarta rawa take.
Mardiyya ta gyara zama idanunta akan wata ƙawarta data zo gidan ta ce "Ni daman na san bakai ka zaɓi Ridayya ba cusa maka ita aka yi,kuma gashi Umma ta saka ka rabu da mugun iri. Da ina cikin damuwa yanzu na samu nutsuwa ganin ka zama nawa gani ɗauka da cikinka wanda nake ƙoƙarin haifa maka, baby naga ka fito takara ashe kaga zan zama matar gwamna her Excellency na ji na ƙara son ka"
Barin ta ya yi ta yi magana son ranta don baya katse mutum a tsarinsa ya sauke numfashi kamar zai yi magana sai kuma ya kashe wayar domin ba ita ɗince a gabansa ba yanzu. Ridayya da sauri ta ƙwace hannunta ta miƙe jikinta na rawa kuka ne ke ƙoƙarin kwace mata amma ta hana faruwar hakan, sosai batun cikin Mardiyya ya saka ta cikin firgici da kaɗuwa da kuma jin ta furta wai Ustaz baya son ta, Umma ta saka ya sake ta duka wannan abubuwan mene gaskiyar batun?
So da Abbiey ke cewa ta amshi budurcinsa faɗa kawai ya yi don ta yi farin ciki ko mene? Kar dai ya munafurce ta ne? Ta rabu da MUNAFIKIN MIJI kuma wannan da take saka ran ya zame mata bango abin jigina ya zama silar yaye war baƙin cikin data ƙunsa a gidan Zameer shi ma ya kasance MUNAFIKIN MIJI. Innalillahi wa'inna ilahir raji'un dunƙulewa zuciyarta ta fara yi tana matsewa waje guda ɗacin da ranta ke yi mata har saman harshenta take jinsa.
Ustaz ya yi shiru shi kansa maganar Mardiyya ta jikkita masa zuciya yana son rikicin Ridayya bai kuma shirya rufe ta ba, babu ƙarya a zaman su. Yana ƙoƙarin miƙewa ya bi bayanta ya ji ƙarar faɗuwar abu dimmm! Yana juyawa ya ga Ridayya kwance a ƙasa goshinta ya daki gefen center table nan take ya fashe glasses ya caki gefen goshinta jini ya fara zuba.
Idan ta yi yunƙurin tashi sai ta sake yanke jiki ta faɗi, jikinta ya fara karkarwa tana kanannaɗewa kumfa ya fara fita idanunta rufe amma hawaye ne ke fita sosai nan da nan ta fita cikin haiyacinta rabon da farfaɗiyya ta tasar mata har haka shi kansa Ustaz ya mance yama ɗauka ko ta daina.
Ya riƙe kansa da kyau cikin sauri ya kunna karatun Alkur'ani ya ɗakko ladduma ya rufe ta gabaɗaya bai san wanne irin mataki zai ɗauka akan Diyya ba, ba zata ja masa masifa kullum rabin ransa tana faɗuwa ba. Ya jima durƙushe a gefenta idanunsa ya sauya ƙirjinsa ya ƙara buɗewa a hankali ya ga fitsari na jiƙa laddumar can ya ji ta saki ajjiyar zuciya bacci ya ɗauke ta.Bata san adadin lokacin data ɗauka tana bacci ba, ba kuma ta san mene ya saka ta bacci har haka ba ta farko tana buɗe idanunta da suka mata nauyi sosai ɗakin duhu sai ɗan ƙaramin haske ta miƙa hannu ta kunna haske a hankali ta jikin gina da jikin frame fuskar gadon sai a lokacin ta lura da sauyin kayan jikinta ga ƙamshin Abbiey ya mamaye ɗakin wanda hakan ke tabbatar mata bai jima da barin wajan ba. Bata son tunawa amma kamar yanzu furucin ke fita ta ci kuka son ranta wataƙila bata cikin matan da suka yi dace da gidan miji wataƙila bata cikin mutanen da za su rabauta da farinciki a nan duniya.
Zuciyarta ce ta ce "Kar ki zama mai butulcewa rahamar Ubangiji, gode masa da iya abinda ya ba ki da kuma abinda kike dashi, ki tuna rayuwar da kika yi a gidan iyayenki babu mai son ki sai Abbiey, kin zama mujiya gidan ubanki, mahaifinki ya ce ke ƴar zina ce, matar uba ta shayar dake uƙubar da ba za ki manta da ita ba, wacce ta haife ki bata son haɗa inuwa dake, ko wanne yaro gudun ki yake saboda kasancewar ki baƙa mummuna. Ridayya kin faɗa tarkon ɗa namiji saboda ki gujewa azabar da masifar gidan iyayenki, kin nuna masa so sa tunanin ya dace dake da tunanin kina son shi ba ki san birgeki kawai yake ba, kin yi amfani wahalar da kike sha wajan ganin kin bar gidan hakan yasa kika amincewa MUNAFIKIN MIJI, ruɗin zuciya, dana kalaman soyayya da tunanin idan Zameer ya bar ki ba za ki samu wani ba, ya saka kika amince kuka ai bata abinda a yanzu yake ƙoƙarin tarwatsa rayuwarki. Kin yi rayuwar aure a gidan Zameer kin zama baiwa kina rayuwa da karuwar mijinki da tunanin ƙanwar mijinki ce, kin sami mijinki turmi data ɓarya, ya aure ki a caca ya raba ki da kowa naki ya miki duka ya karya ki ya ƙona ki a fuska. Ƙaddarar auren MUNAFIKIN MIJI bai barki haka ba, ya mai dake mahaifarsa kika fuskance wulaƙancin ƴa ƙauyen Nahutun Batsari, suka jingina ki da sunan Maita saboda halittar da Ubangiji ya miki, wannan bai gamsu ba aka wayi gari an kawo ɗan shege da mijinki Zameer ya haifa. Ki duba girman abubuwa nan duk kika jure kika shanye saboda kina neman rabauta da Aljanna, kuma kika ɓoye wasu hallayen namijinki saboda ɗan da kuka haifa da shi da kare mutuncinsa har zuwa girma, ba ki da laifi Ridayya ƙaddara ke ɗawainiyya da rayuwarki kuma babban abin farinciki Ubangiji ne ya hallace ki ni'imomin da ya yi miki suna da matuƙar yawa....."

DU LIEST GERADE
MUNAFUKIN MIJI
RomantikNa kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yad...