34

14 4 1
                                    

*Ko da so....*

*34*

Ɗakin ta da ta yi ƴan matanci ta shige yana nan yadda yake sabbin furnitures kawai aka canja, bathroom ta shiga ta hau kuka itakam yanzu babu abinda yake mata daɗi sama da kuka tun tana mai sauti har ta koma shessheƙa, ga duk mai sauraro yasan kuka ne mai ciwo, sai da ta yi mai isar ta sannan ta wanke fuskarta ta fito, turus ta tsaya ganin Abdallah tsaye idanun sa jawur tamkar jan garwashi da sauri ta ƙarasa wurin sa "Abdallan mai aka ma?, baka da lafiya ne"

Girgiza kai ya yi alamun a'a, "to mai aka ma?"

"Ummi (sunan da yaran Bilkisu da na Hafsa ke faɗawa Bilkisu) ce ta ce da Mum Abie ya sake ki, shine Mum tace wallahi mayar mu zakiyi, yanzu fisabilillahi Mami tun da Abie ya daina son mu maine na za'a mayar mu, ko itama Mum ta daina son mu ne kamar Abie?"

Zama bakin gadon Hafsa ta yi sabida jirin da ke ɗibar ta, kamo hannun Abdallah ta yi ta ɗan jawo shi kusa ta yi " yanzu kai Abdallah waye ya ce ma Abie bai son su, kul na sake ji ka faɗi haka, kana jina Abie yana son ku fiye da yadda kuke son kanku"

Girgiza kai Abdallah ya yi "wallahi Mami baya son mu, Aɗɗalaq fa our tafsir mu'allim told us yana nufin cutting your relationship with your partner, in dai yana son mu da yanzu ai muna gida"

Make bakin Hafsa ta yi " na faɗa ma yana son ku kar in kuma ji ka faɗi haka kana jina"

Dafe bakin ya yi idanun sa suka cicciko da hawaye , nan da nan ya fara gumi Miƙewa Hafsa ta yi tare da barin ɗakin tasan Abdallah mutun ne mai tsananin zuciya in ta ƙyale shi tsanar mahaifin nasa zai yi.

Kalaman da Abdallan ya faɗa mata na Mum ta ceba zata rike su ba ke mata yawo a ka, itakam ba wanda ya isa ya mayar mata da yara sai dai in a haɗa a kora har da ita.

Aiman da suka shigo tare tuni ya yi bed room ɗin Abba, Abban na kwance yana bacci Aiman ɗin ya faɗa jikin sa tare da faɗin "Bumm!" Cakumo shi Abba ya yi suka hau dariya, Abba yasan shine kusan tunda Hafsa ta girma bai kuma sabo da wani yaro sabo mai sunan sabo ba irin Aiman yaron ya shiga ransa, sak uwar sa Hafsa yake.

Sai da suka gama wasan sannan Aiman ya ce "ina kwana Malam tsoho" ya faɗa cikin tsamin Muryar yarin ta, dariya Abba yasa "kaji tsoho na ce da tsoho ɗan uwan sa tsoho" turo baki Aiman ya yi " ni walllahi yaro ne, school teacher ɗin mu ma tace nine youngest a class ɗin mu"

Dariya Abba ya yi "a'a fa Aiman tsoron ka take ji, dan taga kai kato ne, jibi furfura a kanka" kuka Aiman yasa shi bai da furfura Abba yasa dariya ya hau lallashin sa.

Sai da ya yi shiru sannan Abba ya tuna baiji ma shi da waye suka zo ba, duda wataran shi kaɗai ake kawowa " ina yayun naka?," Abban ya tambaya.

Fuskar tausayi yaron ya yi tare da cewa "suna falo, mu da Mami ne da kayan mu ma muka zo, Abie ne yace Mami ta kwashe ta tawo da mu take ta kuka, jiya da daddare naji yana faɗa mata shine naje nace da yaya Abdallah ya kawon ruwan" ya faɗa cikin muryar yara, duda maganar Aiman batai kwari ba Abba ya fahinci mai yake nufi saukowa ya yi daga kan gadon hankali tashe falo ya nufa ganin yaran. Jugun jugum a zaune ya kuma tabbatar masa bawai shirmen Aiman bane da ƙamshin gaskiya a batun dan basa takurewa wuri guda, yara ne masu walwala da kazar kazar da ace lafiya ƙalau shigowar su da tun kan Aiman ya ƙaraso ɗakin sa hayaniyar su ya tada shi.

Ɗakin Mum Abba ya nufa bayan ya miƙawa Faruk Aiman da ya ruƙo hannun sa baya son yaron ya biyo shi, tun daga bakin ƙofa yake jin kukan Hafsa da faɗan Mum " to wallahi baki isa ba, tunda shi ɗan iska ne bai san ya kamata ba, dole yanzu bawai sai gobe ba a ɗauki yaran sa a mayar masa ai ke kaɗai ya aura dan haka ke kaɗai zai sako mana mu amsa ah to"

Ajiyar zuciya Abba ya yi tare da shiga ɗakin.

***********

Muktar yana gani suka fitar da kayan da ya haɗawa yaran ji yake kamar ya leƙa ya ce ta aje masa yaran sa, sai dai baya son abun yama Hafsa yawa baya son rashin mijin ta da yaran ta ya sa mata cuta yasan in yaran na kusa da ita suna mata hira damuwar ta zata ragu.

Sai da suka fi awa da tafiya sannan ya fito falon ya gyara, sannan ya shiga kitchen kwanukan da Faruk ya dafa musu indomie ya wanke ya fito ya shiga wanka, yana wankan yana share hawaye bai taɓa sanin shi ɗin ba jarumi bane sai yau da matar son sa da gudan jinin sa suka masa nisa.

Shigar sa ta kullum shigar manyan kaya ita ya yi sannan ya fito zuwa harabar gidan inda ya nufi unguwar su ta Dala.

Kusan tana nan yadda take, sai dai gine ginen ƙasa da suka ɗan sauya zuwa na bulo sakamakon waɗan da suka raba gado sun sake fasalillikan gidajen su.

Cikin gidajen da aka sauya harda gidan su Muktar, duda dama can bana ƙasa bane dan lokacin mahaifin su nada rai ya mayar da abun sa na bulo, sai dai tasowar arziƙin Muktar ya kuma gyare shi ya saka musu Tiles ko ina, gidan ya kuma kyau dai dai rayuwar average mutun ɗan Nigeria.

A ƙofar gida ya ci karo da Noor ɗan gidan Rashida saɓe da jaka, rissinawa Noor ɗin yayi "Abie ina kwana" daurewa Muktar ya yi tare da ɓoye damuwar sa " lafiya ƙalau Noor, daga ina haka?"

Murmushi Noor din ya yi " da yake yau ba mu da lectures shine na kawowa Aunty Juwairiyya kayan ta da ta ban ɗin ki, ta ce in kawo mata gun Inna, zata aiko Fahad ya amsa"

Gyaɗa kai Muktar ya yi "ma sha Allah, ɗin kin ya yi nisa kenan to Allah ya sa albarka" ya faɗa tare da ciro dubu huɗu a aljihu " ungo wannan ka rage wani abun" amsar kuɗin Noor ya yi tare da yin godiya inda Muktar ya shiga ciki da Sallamar sa.

"Assalamu alaikum"

Inna sa ke zaune tana gyara barkono ta amsa da "wa'alaikumusalam"

Yadda ta ɗago taga Muktar ya tsoratata duk ya faɗa Muryar shi ma ta yi kama data mara lafiya, samun gefen ta ya yi ya zauna, kallon sa a yi tasan halin zurfin cikin sa ko ta tambaya ba faɗa zai ba miƙewa ta yi tare da yin bakin inda shara take tahau rere barkonon, juyowar da ta yi ta ganshi riƙe da kansa, a hankali ta matso tare da taɓa shi ganin ta tambaye shi mai ke damun sa ko bai da lafiya ne ya yi shiru.

Firgigit ya dawo tunanin sa, " lafiya Muktar mai ke damun ka?, Kasan baka da lafiya ai da ka yi zaman ka a gida."

A hankali cikin rarraunar murya ya ce " Inna na saki Hafsa"

Farantin da ke hannun ta ne ya dire " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Muktar saki kuma, da hankalin ka, Anya kuwa, Hafsan"

Shiru ya yi tare da kasa yin magana, yasani Inna ba zata taɓa goyon bayan sa ba gashi kuwa yadda muryar ta, jikin ta da aikin ta ya nuna damuwa ƙara ra, kafin ya fara tunanin abin faɗa mata ta kuma magana " Ka yi maza ka je ka mayar da matar ka, haba Muktar saki fa, ko a mafarki aka ce mun zaka saki matar ka zance karya ne, ta ya zan yadda kai kake daɗamun da kan ka, ai ko ba yara tsakanin ku Muktar halaccin yarin yar nan gare ka bata cancanci saki ba, kaje ka mayar da ita."

Girgiza kai ya hau yi cikin kuka yake magana wanda ya tsoratata Inna dan tun Muktar baifi 12 years ba Inna ba zata iya tuna sanda taga kukan  sa ba, "Inna dan Allah karki bani Umarnin maida Hafsa, rabuwar mu shine mafi alkairi, nasani abune mai ciwo gare ni anma na yadda hukunci ne mafi kairi na yanke, aure ba iya soyayya kawai ke iya riƙe shi ba, nayi tunanin ada so is more than enough but na gane Ko da so akwai abubuwa da yawa...

Kasa magana Inna ta yi, ta zuba masa ido wanda har lokacin hawaye na bin kuncin sa.

Rubutawa
Aeshakhabir
Fadimafayau

Ko da soWhere stories live. Discover now